Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiNajeriya za ta samu ci-gaba idan yan siyasa suka hade kawunansu -...

Najeriya za ta samu ci-gaba idan yan siyasa suka hade kawunansu – Akpabio

By Salisu Ado Sulaiman

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Godswill Akpabio ya bukaci hadin kai tsakanin yan siyasa, yana mai cewa kasar za ta samu ci-gaba ne idan har suka cire son kai ko nuna bangaranci.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Akpabio ya yi wadannan kalamai ne wajen taron bikin yar gidan sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa kuma tsohon gwamnan jihar Ibrahim Dankwambo.

Taron bikin ya samu halartar yan majalisun tarayya akalla guda 70, ciki har da kakakin majalisar wakilan Najeriya Tajuddeen Abbas.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata