Rahoton Global Firepower Index na 2026 ya nuna cewa Masar ce ke kan gaba a jerin ƙasashen Afirka masu ƙarfin soji, inda ta zo ta 19 a duniya, sakamakon ingantaccen horo, sabbin kayan aiki da ƙarfafa rundunar ruwa da sama.
Rahoton, wanda aka samu a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an tantance ƙasashe sama da 140 ne bisa ƙarfin soji, adadin ma’aikata, kayan aiki da dabarun tsaro, tare da duba yadda ƙasashe ke shirin kare tsaro da zaman lafiyarsu.
Bayan Masar, Aljeriya ta zo ta biyu a Afirka da matsayi na 27 a duniya, yayin da Nijeriya ta zo ta uku a nahiyar da matsayi na 33, sakamakon sabunta kayan tsaro da kuma dogaro da ƙarfin ma’aikata wajen tinkarar ta’addanci da matsalolin cikin gida.
Rahoton ya kuma nuna Afirka ta Kudu a matsayi na huɗu (40 a duniya), sai Ethiopia (47), Angola (59), Morocco (56), Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (64), Sudan (66) da Tunisia (76), inda aka ce yawancin ƙasashen na ƙara zuba jari a fasaha, horo da dabarun zamani domin tabbatar da tsaro da daidaito a nahiyar Afirka.
