Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fama da barkewar cutar amai da gudawa a nahiyar Yammaci da Tsakiyar Afirka, inda ta zo na biyu a jerin ƙasashen da cutar ta fi shafa.
Daraktan yankin Yammacin da Tsakiyar Afirka na UNICEF, Gilles Fagninou, ya bayyana hakan a ranar Laraba, inda ya ce cutar ta zama ruwan dare a Nijeriya, inda take kashe mutane da dama.
Fagninou ya ce, yayin da damina ke ƙaruwa a yankin, yara ne ke cikin haɗari mafi girma, inda akalla yara 80,000 ke cikin haɗarin kamuwa da cutar.
