Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiNijeriya da makwabtan kasashe sun soma fatattakar Lakurawa

Nijeriya da makwabtan kasashe sun soma fatattakar Lakurawa

Nijeriya da Nijar, da kuma Chadi da wasu makwabtan kasashe sun yi haɗaka wajen fatattakar ‘yan kungiyar Lakurawa da suka addabi iyakokin kasar.
Wannan hadakar na da manufar kakkabe ‘yan ta’addan da ke aiwatar da miyagun ayyuka a kasashen Nijeriya da kasashen dake kewaye da ita.
 
Da yake karin haske akan matakan da suke dauka, daraktan yada labarai na hedkwatar tsaron Nijeriya Manjo-Janar Edward Buba, ya shaidawa jaridar Punch cewa hadin gwuiwar kasashen wajen sintiri akan iyaka zai rufe duk wata mafaka da Lakurawa za su bi domin shiga kasashen.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata