Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiNijeriya na bin kasashen Nijar, Togo da Benin tulin bashin kudin lantarkin...

Nijeriya na bin kasashen Nijar, Togo da Benin tulin bashin kudin lantarkin da ya kai N25bn – NERC

Hukumar kula da lantarki ta Nijeriya NERC ta ce, kasar na bin kasashen Togo, Nijar da Benin bashin dala $17.8m — kimanin N25bn na lantarkin da aka ba su a ƙarƙashin yarjejeniyoyin kasashen waje.

A cikin rahoton rubu’i na uku na 2025, hukumar NERC ta bayyana cewa kamfanonin sayar da lantarki sun tura wa kasashen uku takardar biyan kuɗi har dala $18.69m na lantarkin da suka sha a lokacin, amma suka biya $7.125m kawai, lamarin da ya bar ragowar bashi na $11.56m.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata