Shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, ya gargadi Nijeriya da sauran kasashen duniya cewa idan ba a dauki matakan gaggawa da hadin gwiwa ba, karuwar yawan jama’a musamman matasa na iya zama barazana ga zaman lafiya maimakon samun ci-gaba.
Banga ya bayyana haka ne yayin taron shekara-shekara na IMF da Bankin Duniya na shekarar 2025, inda ya yi hasashen cewa yawan jama’ar Nijeriya na iya karuwa da kusan mutane miliyan 130 nan da shekarar 2050.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, karuwar yawan matasa a nahiyar Afirka na iya zama dama ta ci-gaba ko kuma hadari a rashin kyakkyawan tattalin arziki.
Hakazalika, Banga ya nuna rashin ayyukan yi da tsarin tattalin arziki mai nagarta na iya haifar da tashin hankali da samar da baƙin haure daga ƙasashe masu tasowa.
Banga ya bayyana shekarun da ke tafe a matsayin muhimman lokuta a tarihin ɗan Adam, yana mai cewa nan da 2050, fiye da kashi 85 cikin 100 na al’ummar duniya za su kasance a ƙasashen da ake kira masu tasowa, inda matasa sama da biliyan 1.2 za su bukaci aikin yi amma guraben aiki miliyan 400 kacal ke da akwai.
