Sunday, April 5, 2026
HomeLabaraiNijeriya na kashe rabin kudin shigarta wajen biyan bashi maimakon kashi 97...

Nijeriya na kashe rabin kudin shigarta wajen biyan bashi maimakon kashi 97 – Kwamitin Shugaba Tinubu

Shugaban kwamitin kudi da gyaran haraji na Shugaba Tinubu, Mista Taiwo Oyedele, ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya yanzu tana kashe ƙasa da kashi 50 cikin 100 na dukkanin kudaden shigarta wajen biyan basussuka.

A yayin wata hira a taron PwC Executive Summit da aka gudanar a Legas, Oyedele ya ce kafin aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, Nijeriya tana kashe kusan kashi 97 cikin 100 na dukiyar da take samu wajen biyan basussuka.

A cewarsa, gwamnatin ta riga ta biya wasu tsofaffin basussukan ƙasashen waje da suka kai fiye da dala biliyan 7, asusun ajiyar kuɗin cikin gida ya karu daga dala biliyan 4 zuwa biliyan 20.

Har ila yau, harajin da ake karɓa daga mutane da kamfanoni ya tashi daga ƙasa da kashi 10 zuwa 13.5 cikin 100 a cikin shekaru biyu kacal.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata