DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, April 10, 2026
HomeLabaraiNijeriya ta kashe naira biliyan 8.8 wajen gyaran turakun lantarki da aka...

Nijeriya ta kashe naira biliyan 8.8 wajen gyaran turakun lantarki da aka lalata – TCN

Kamfanin Samar da Wutar Lantarki na Najeriya ya bayyana cewa an kashe biliyan 8.8 wajen gyara turakun lantarki da ‘yan bindiga da wasu bata gari su ka lalata a wurare daban-daban a fadin kasar nan.
Manajan daraktan kamfanin Injiniya Suleiman Abdulaziz ne ya sanar da hakan a Abuja, inda ya ce daga 13 ga watan Janairun 2024 zuwa yanzu manyan turakun lantarki 128 ne aka lalata.
Injiniya Suleiman ya nuna damuwarsa cewa duk lokacin da a ka cafke wadanda ke wannan aika-aikar ana gurfanar da su akan laifin sata a maimakon lalata kayan gwamnati, abinda ke sa ana bayar da su beli daga baya.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata