Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiNiMet ta yi hasashen ruwan sama da guguwa a Nijeriya daga Litinin...

NiMet ta yi hasashen ruwan sama da guguwa a Nijeriya daga Litinin zuwa Laraba

Hukumar lura da yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama da guguwa daga Litinin zuwa Laraba a sassa daban-daban na Najeriya.

A sanarwar da ta fitar a Abuja, NiMet ta ce akwai yiyuwar ruwan sama da guguwa a safiyar Litinin a Taraba da Adamawa, da kuma daga bisani a Zamfara, Kebbi, Kaduna da sauran yankuna.

A Arewa ta tsakiya, ana sa ran gizagizai da hasken rana a safiya sannan daga bisani a samu ruwan sama da guguwa a FCT, Kogi, Niger, Benue, Filato da Nasarawa.

A Kudu, za a fara da ruwan sama a Lagos, Ogun, Ondo, Akwa Ibom, Cross River, Rivers, Delta da Bayelsa, sannan daga baya a ci gaba da ruwan sama a Oyo, Ekiti, Osun, Edo da sauran jihohin kudu.

A ranar Talata kuma, za a fara da hasken rana a Arewa, sai daga baya a samu guguwa da ruwan sama a Bauchi, Taraba, Kaduna, Kebbi, Katsina, Kano da Adamawa kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ambato.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata