Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiNiMet ta yi hasashen ruwan sama mai yawa na kwanaki uku a...

NiMet ta yi hasashen ruwan sama mai yawa na kwanaki uku a Nijeriya

Hukumar kula da yanayi ta Nijeriya NiMet ta bayyana cewa daga ranar Litinin zuwa Laraba za a samu ruwan sama tare da guguwa da tsawa a sassa daban-daban na ƙasar.

An yi gargadin yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu jihohin Arewa musamman Adamawa, Taraba da Gombe.

Kazalika za’a samu ruwan sama kadan-kadan a garuruwan da ke yankin kudu a cewar hasashen na hukumar ta kula da yanayi a Najeriya.

NiMet ta shawarci jama’a, musamman direbobi da manoma da su dauki matakan kariya domin kauce wa hadura yayin da ake sa ran ruwan sama mai yawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata