Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiNiMet ta yi hasashen za a tafka mamakon ruwan sama na kwana...

NiMet ta yi hasashen za a tafka mamakon ruwan sama na kwana 3 a wasu jihohin Nijeriya

Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya NiMet ta yi hasashen cewa za a tafka ruwan sama da tsawa a wasu sassan kasar daga ranar Litinin zuwa Laraba.

Wani bayani da NiMet ta fitar ranar Lahadi a Abuja ta yi hasashen za a yi ruwan sama a wasu sassan jihohin Taraba, Kaduna, Gombe, Bauchi, Kebbi, Sokoto, Katsina, Jigawa da Kano a yankin arewa.

A cewar hukumar, za a iya samun tsawa da ruwan sama a wasu sassan jihohin Plateau, Babban Birnin Tarayya, Nasarawa, Kwara, Neja, Kogi, da Jihohin Benue.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata