Tuesday, April 7, 2026
HomeLabaraiNLC ta yi barazanar zanga-zanga kan “ruɗani” kan dokar zaɓe da majalisa...

NLC ta yi barazanar zanga-zanga kan “ruɗani” kan dokar zaɓe da majalisa ke gyara

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi gargaɗin yiwuwar zanga-zangar ƙasa baki ɗaya da kuma kaurace wa zaɓe, sakamakon abin da ta kira ruɗani da saɓanin matsaya daga Majalisar Dattawa kan gyaran Dokar Zaɓe, musamman game da aika sakamakon zaɓe ta na’ura.

Kungiyar ta zargi Majalisar Dattawa da watsi da buƙatar jama’a ga tsarin zaɓe a Nijeriya, saboda kasa fayyace ko aika sakamakon zaɓe ta na’ura tilas ne ko a’a.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, inda ya ce kungiyar na nuna damuwa mai tsanani kan “ruɗani da bayanai masu karo da juna” da ke fitowa daga Majalisar Dattawa dangane da gyaran Dokar Zaɓe ta 2022, musamman a kan batun e-transmission.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili, Mataimakin Manajan Edita kuma Mai Kula da Shirin Koyon Sanin Makamar Aiki ne a DCL Hausa. A matsayinsa na ƙwararren ɗan jarida yana tsara ayyukan rediyo da kafafen sada zumunta, fassarar labarai, da tabbatar da sahihancin bayanai. Yana jagorantar shirin horaswa ga masu koyon aiki tare da kula da ingancin rubuce-rubuce da shirye-shiryen gidan jaridar.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata