Jam’iyyar NNPP reshen Kano ta bukaci Fadar Shugaban Nijeriya da Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA) su fito su wanke jagoranta na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, daga zargin da ake alakanta shi da tallafa wa ta’addanci.
A sanarwar da Sakataren Yada Labarai na jiha, Injiniya Ibrahim Karaye, ya sanya wa hannu, jam’iyyar ta nemi a fitar da bayani a hukumance domin kawar da abin da ta kira zarge-zarge marasa tushe.
NNPP ta bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan Nijeriya mai kishin ƙasa, tana mai cewa tarihinsa a fannin ilimi da bunƙasa al’umma ya isa shaida. Ta kuma gargadi ‘yan siyasa da su guji amfani da batun tsaro a matsayin makamin takara.
Jam’iyyar ta roƙi gwamnatin tarayya da ofishin NSA su fayyace lamarin cikin gaggawa domin kauce wa abin da ta kira kunyatar da ƙasa da kuma yaɗuwar mummunar fahimta a idon duniya.
