Wani jigo a jam’iyyar NNPP Ladipo Johnson, ya bayyana kwarin gwiwar cewa jam’iyyar za ta lashe zaben Kano a 2027 ko da Gwamna Abba Kabir Yusuf fice daga cikinta tare da komawa APC.
Kalaman nasa sun zo ne a daidai gabar da Gwamnan ya gana da shugaban Nijeriya a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin 19 ga watan Janairun 2025.
A cewar Ladipo, ko kadan batun shirin ficewar Gwamnan daga NNPP ba ta girgiza su ba, kasancewar sun gina tubali mai kwari da zai taimaka musu wajen lashe zabe a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, kamar yadda Channels TV ya wallafa.
Duk da cewa ganawar Gwamna Abba da shugaba Tinubu ta ruruta batun komawar sa jam’iyyar APC, mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin Tofa ya ce ganawar tasu ta ta’allaka ne kan abubuwan da suka shafi kalubale, ayyuka da kuma ci-gaban jihar Kano.
