Jam’iyyar NNPP ta musanta rahotannin da ke cewa jagoranta na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, yana tattaunawa don sauya sheƙa zuwa APC, tana mai cewa karya ce tsagwaronta ta da aka kirkira domin ruɗar jama’a.
A cewar Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na kasa Ladipo Johnson, babu wata ganawa ko tattaunawa da aka taɓa yi tsakanin Sanata Kwankwaso da Shugaba Tinubu, ko APC game da sauya sheƙa, duk da jita-jitar da ta bazu a wasu wurare.
Rahotannin sun biyo bayan da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauya sheƙa zuwa APC, inda wasu ke danganta hakan da manyan bukatu da ake zargin Kwankwaso ya gabatar a yayin wata tattaunawa da jam’iyyar mai mulki da hakan ya kawo tsaiko game da komawarsa APC.
