Kungiyar malamai ta Najeriya NUT za ta karrama gwamnan Katsina Dikko Umaru Radda, bisa kyautata walwala da jin dadin malaman makaranta a jihar.
Za a yi taron karramawar ne a bikin ranar malamai ta duniya da za a gudanar a dandalin Eagle Square da ke Abuja.
A cewar kungiyar, Dikko Radda ya bullo da tsare-tsaren da suka taimaka wajen sanya jihar Katsina a gaba-gaba ta bangaren ilimi a Najeriya.
