A ranar Litinin 16 ga watan Yunin, 2025, ne wani shaida na EFCC, Umar Babangida, da ya bayyana a gaban kotun tarayya da ke Apo, Abuja, ya ce tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da Majalisar Zartarwa (FEC) ba su taba amincewa da kwangilar Mambilla da aka bai wa kamfanin Sunrise Power ba a 2003.
Shaidar ya ce Obasanjo ya umurci Ministan lantarki da karafa na gwamnatinsa Agunloye da ya janye bukatar, amma ya yi gaban kan sa wajen sanya hannu a yarjejeniyar kwangilar da kamfanin cikin awa 24, ba tare da izini ba.
EFCC ta ce minista Agunloye ya karɓi wasu kudade daga jami’in Sunrise, Shotire Jide Abiodun har sau uku daya hada da:
1. N3.6m – 10/08/2019
2. N500k – 22/10/2019
3. N1.12m – 13/11/2019
A karshen, rahoton na EFCC ya ce Agunloye na fuskantar tuhuma kan cin hanci da badakalar dala biliyan 6. Shari’a ta cigaba ranar 18 ga Yuni.
