Monday, April 6, 2026
HomeLabaraiOsinbajo ya isa Cote d'Ivoire don jagorantar sa ido kan zaben kasar

Osinbajo ya isa Cote d’Ivoire don jagorantar sa ido kan zaben kasar

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya isa Cote d’Ivoire domin Jan ragamar masu sanya ido kan zaben kasar da zai gudana a ranar Asabar 25 ga watan Oktoba da muke ciki.

Wata sanarwa da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fitar, ta bayyana cewa ta aika tawagar zuwa kasar ne, a wani yunkuri na tabbatar da turbar dimukuradiyya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Osinbajo, wanda ya yi mataimakin shugaban Nijeriya daga shekarar 2015 zuwa 2024 zai jagoranci jami’an sa ido kan zabe na ECOWAS guda 187.

Haka kuma akwai jami’ai guda 66 daga kungiyar tarayyar Afirka wato AU.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata