DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 106

Sojoji sun dakile yunkurin garkuwa da ‘yan bautar kasa

0

Dakarun haɗin gwiwa na “Operation Hadin Kai” sun dakile wani yunkurin garkuwa da masu yi wa kasa hidima 74 a hanyar Buratai zuwa Kamuya, jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo Sani Uba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, inda ya ce sojojin sun yi gaggawar kai dauki bayan motocin ɗaliban sun lalace a wurin da ake yawan yin garkuwa da mutane.

A cewar sa, masu yi wa kasa hidimar maza 36 da mata 38, motar tasu ta lalace ne da misalin ƙarfe 9:05 na dare a ranar Talata.

Sojojin sun gano matasan suna cikin haɗari, suka garzaya suka kwashe su zuwa sansanin soja da ke Buratai don kare su daga yiwuwar hare-haren ‘yan ta’addan.

Atiku Abubakar ya musanta bai wa jami’in sojan da ya kalubanci Wike kyautar mota

0

Tsohon dan takarar shugaban Nijeriya Atiku Abubakar, ya musanta rahotannin da ke cewa ya bai wa wani sojan ruwa, Laftanar Ahmed Yerima, sabuwar motar saboda abinda ya faru tsakanin sa da ministan Abuja, Nyesom Wike.

Mai ba wa Atiku shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe ne ya fitar da wannan bayani a shafinsa na X a ranar Alhamis, inda ya bayyana rahoton da ke yawo a kafafen sada zumunta a matsayin ƙarya tsantsa da babu hujja a ciki.

Ibe ya ce Atiku bai bai wa Laftanar Ahmed Yerima ko wani mutum motar Toyota SUV ba, saboda haka labarin kirkirarre ne.

Wadanda suka soke ni a baya yanzu yabo na suke – Olusegun Obasanjo

0

Tsohon shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo, ya ce ba za a taɓa gujewa suka ba a mulki, amma wadanda ke suka a yau su ne ke zama masu yabo a gobe.

Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Laraba a Ibadan yayin da yake ƙaddamar da tashar mota ta zamani a Iwo Road, Ibadan, wanda Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya gina domin sauƙaƙa zirga-zirga a birnin.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce Makinde ya cancanci yabo saboda ayyukan raya ƙasa da ke sauƙaƙa rayuwar jama’a.

Ya ce shima haka aka yi da shi lokacin yana shugaba amma yanzu masu sukar sa su ne ke yi masa godiya da kuma yaba masa.

Bukola ya shawarci PDP da ta dakatar da babban taron ta na kasa

0

Tsohon shugaban majalisar dattawan Nijeriya Bukola Saraki, ya shawarci jam’iyyar PDP ta dakatar da shirinta na gudanar da babban taronta na kasa da aka tsara gudanarwa daga ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamban 2025 a Ibadan, jihar Oyo, saboda rikice-rikicen siyasa da kuma hukuncin kotu.

Saraki ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a daren Laraba, bayan ganawarsa da mambobin kwamitin sulhu na jam’iyyar karkashin jagorancin Ambasada Hassan Adamu, yayin da suka kai masa ziyara a gidansa da ke Abuja.

Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya ce duk da ƙoƙarin da shugabannin jam’iyyar ke yi wajen warware sabani, taron Ibadan ya shiga cikin rikicin siyasa da hukuncin kotu wanda zai iya lalata sahihancin sakamakon da za a samu daga gare shi.

Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da harajin kashi 15 na man fetur da Gas

0

Hukumar kula da harkokin man fetur ta Nijeriya NMDPRA ta sanar da cewa an dakatar da aiwatar da harajin kashi 15 cikin 100 na kayan da ake shigo da su na man fetur da Gas.

A wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis, daraktan sashen yaɗa labaran hukumar George Ene-Ita, ya bayyana cewa shirin aiwatar da wannan haraji ba ya cikin tsarin gwamnati a halin yanzu.

Wannan na zuwa ne bayan rahotannin da suka nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da sanya harajin kashi 15 cikin 100 ga man fetur da dizal da ake shiga da su ƙasar.

Kotu ta daure ma’aikatan majalisar wakilai bisa damfarar miliyan 4.8

0

Kotun babban birnin tarayya ta Abuja ta rufe ma’aikata biyu na majalisar dokokin Nijeriya Mustapha Mohammed da Tijjani Goni a gidan yari, bisa kama su da laifin damfarar Naira miliyan 4.8 da sunan samar da aiki.

Mai Shari’a B.M. Bassi ne ya yanke wannan hukunci bisa samun su da laifin yaudarar mutane biyu da sunan za su sama musu aiki a babban bankin Nijeriya CBN da hukumar haraji ta FIRS.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ICPC, Demola Bakare ya fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa batun ya samo asali ne daga koke da wasu mutane suka shigar, wato Saifudeen Yakub da Aminu Abubakar, inda suka ce waɗanda ake zargin sun karɓi kuɗi don basu takardun bogi na aiki.

Bayan bincike, ICPC ta gurfanar da su kan tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi haɗin baki da karɓar kuɗi ta hanyar yaudara.

Dole mu karfafawa sojoji gwiwa saboda sadaukar da rayukansu da sukai – Tinubu

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya jinjina wa maza da mata na rundunar sojojin Nijeriya bisa jajircewa da sadaukarwar da suke yi don kare ƙasar daga barazanar tsaro.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Tinubu ya bayyana hakan ne a taron ƙungiyar Editocin Nijeriya NGE da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, inda ya ce sojojin suna fuskantar haɗari domin kare mutuncin kasar.

Shugaban ya ce duk da ƙalubalen da ake fuskanta na ta’addanci da ‘yan bindiga, gwamnatinsa tana ɗaukar matakai don karfafa rundunar sojoji da sauran jami’an tsaro.

A cewar sa, ya zama wajibi a ci gaba da kare su da kuma ba su goyon baya duba da irin hadarin da suke fuskanta.

Muna biyan ‘yan bindiga Naira miliyan 7 don zama a gidajenmu ko noma gonakinmu

0

Wasu al’ummomi a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja sun bayyana cewa suna biyan haraji ga ‘yan bindiga domin su samu damar zama a garuruwansu ko kuma ci gaba da noma gonakinsu.

A cewar shugaban al’ummar, Alhaji Yahaya, wanda ya bayyana haka yayin wata hira da shi a shirin Tsalle Daya na tashar Prestige FM Minna, ya ce al’ummarsu ta na biyan ‘yan ta’adda Naira miliyan bakwai a matsayin kudi domin barinsu su zauna a mahalllansu.

Ya ce garuruwan da ke karkashin ikon ‘yan bindigar sun haɗa da Makera, Galapai, Chukuba, Ushaka, Manini, Kawuri, Bakarie I, Utako da Magana, inda kowane mutum mai aure ke ba da gudunmawa wajen tara kudin.

Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar kan shigo cikin gari da bindigu har sai an ba su kuɗi, yayin da jami’an tsaro kuma suka daina yin sintiri a yankin.

Abin takaici ne a ce tawagar Super Eagles na bin bashi – Peter Obi

0

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023 Peter Obi, ya bayyana takaici kan rahotannin da ke nuna cewa tawagar wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya Super Eagles na bin bashi na alawus-alawus da wasu kudaden aiki.

Obi ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Talata, inda ya ce lamarin na iya rage wa ‘yan wasa ƙwazo da ƙwarin gwiwar wakiltar ƙasarsu da cikin himma.

Ya ce gwamnati na da alhakin kula da walwalar ‘yan wasa, tare da tabbatar da biyan hakkokinsu cikin lokaci da ƙarfafa musu gwiwa domin ci gaba da ba da gudunmawa ga ci gaban wasanni.

Sheikh Gumi ya musanta cewa ya gudu daga Nijeriya zuwa Turkiyya saboda barazanar Trump

0

Fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa tafiyarsa zuwa ƙasar Turkiyya ba ta da alaka da barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yiwuwar kai hari a Nijeriya saboda zargin kisan Kiristoci.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, bayan da hotunan Sheikh Gumi suka bayyana yana cikin ƙasar Turkiyya, wasu mutane a kafafen sada zumunta sun yada labarin cewa malamin ya gudu ne don tserewa hare-haren da ake zargin Amurka za ta kai Nijeriya.

Wasu masu amfani da dandalin X sun yi tsokaci suna cewa Gumi na iya zama cikin wadanda za su fuskanci hare-haren Trump, kasancewar an taba ganinsa yana tattaunawa da wasu ’yan bindiga a dazuka.

Sai dai Sheikh Gumi ya ce ya dade yana shirin tafiya tun kafin wannan barazana ta Trump.