DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 105

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya sauya manyan hafsoshin sojin kasar

Rahotanni sun tabbatar da cewa a daren Laraba ne Shugaba Paul Biya ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka ta sauya jami’ai a makarantar tsaro ta kasar ta Kamaru (International School of Security Forces).

Sabon sauyin ya shafi sassa daban-daban na makarantar, ciki har da sashen nazari, cibiyar bincike da tattara bayanai, da kuma sashen gudanarwa.

A cikin shekara guda kacal, Shugaba Biya mai shekara 92 ya yi sauyin manyan hafsoshin soja fiye da sau shida, tun bayan shekarar 2023 lokacin da juyin mulki ya yi kamari a kasashen yankin Sahel da ma makwabciyarsu Gabon.

An kama wasu ƴan Nijeriya 3 kan zargin aikata damfara ta yanar gizo a Kenya

0

Rundunar da ke gudanar da binciken manyan laifuka a ƙasar Kenya (DCI) ta tabbatar da kama wasu ’yan Nijeriya uku bisa zargin aikata damfara ta yanar gizo.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, jami’an DCI sun kama mutanen ranar Laraba, bayan al’ummar yankin sun shigar da korafi kan motsin mutanen da suke gani a daren cikin wani gida da basu amince da shi ba.

DCI ta bayyana cewa mutanen uku sun ce suna gudanar da kasuwanci na intanet, sai dai an gano cewa suna zaune ne a kasar ba bisa ka’ida ba, kuma ba tare da samun lasisin aiki a kasar ba.

BBC ta nemi afuwar Trump kan wani bidiyo da aka yanke jawabinsa ba daidai ba

Shugabancin kafar yada labarai ta BBC ya nemi afuwar shugaban Amurka Donald Trump kan gyaran bidiyon da aka yanke jawabinsa ba daidai ba, tare da cewa hakan ba hujjar kai ta gaban kotu bane.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, BBC ta fitar da wannan sanarwa ne bayan ta tabbatar da cewa Shugabanta Dr. Samir Shah, ya rubuta wa Shugaba Trump wasiƙar neman afuwa kan wani bangare na jawabinsa da aka gyara ba daidai ba a cikin wani shiri da ta watsa.

A ranar Litinin, BBC ta nemi afuwa kan yadda wani bangare na shirin ya nuna kamar Trump ya kira magoya bayansa su ta da tarzoma kafin abinda ya faru na mamaye majalisar domokin Amurka a 6 ga Janairu 2021.

BBC ta ce tana nadamar gyaran bidiyon, sannan lauyoyinta sun rubuta wa tawagar Trump cewa ba a ga wata hujja da za ta zama dalilin shigar da kara ana neman diyyar dala biliyan ɗaya ba.

Tinubu ya sake nada Janar Buba Marwa (rtd) a shugabancin hukumar NDLEA

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Janar Mohammed Buba Marwa mai ritaya a matsayin shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a sabon wa’adi na shekaru biyar, wanda zai kai shi har zuwa shekarar 2031.

Marwa dai ya fara aikin a matsayin shugaban hukumar ne tun a Janairun 2021 bayan nadin da tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari ya yi masa.

Marwa, wanda dan asalin jihar Adamawa ne kuma tsohon soja, ya halarci makarantar horas da sojoji (NDA), ya kai mukamin laftanar a shekarar 1973.

Gwamnatin Nijeriya ta dage harajin shigo da fetur da dizal na kashi 15

0

Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da aiwatar da harajin shigo da fetur da dizel na kashi 15% zuwa farkon shekarar 2026, bayan tattaunawa mai zurfi da aka yi kan shirin.

Jaridar Punch ta rawaito cewa, wannan dagewa ta samu amincewar shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, bayan da shugaban hukumar tara haraji ta kasar Dr. Zacch Adedeji ya tura takarda mai dauke da bukatar hakan.

Rahoton ya bayyana cewa harajin, wanda aka amince da shi tun ranar 21 ga watan Oktoban 2025, an tsara shi ne domin karfafa masana’antu masu tace mai na cikin gida da kuma daidaita farashin man a kasuwa.

Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya ce taron PDP babu gudu babu ja da baya

0

Gwamnan jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin shirya babban taron jam’iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta yanke hukuncin gudanar da babban taron jam’iyya a garin Ibadan.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Gwamna Fintiri ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai, bayan wani muhimmin taron jiga-jigan jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.

Taron ya samu halartar Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, Amb. Umar Damagum, Bukola Saraki, kakakin jam’iyyar, Debo Ologunagba, da sauran manyan jiga-jigai a cikinta.

Fintiri ya ce taron ya tattauna muhimman batutuwa da dama, yana mai jaddada cewa zasu tafi Ibadan domin babban taronsu, kuma wannan kudiri ba zai canza ba.

Ƴan Nijeriya sun gargadi Turai kan barazanar da Wike ke yi wa demokradiyya a ƙasar

0

Kungiyar Nigeria Unite ta kai karar minista Nyesom Wike zuwa ga Kungiyar Tarayyar Turai

Ministan Abuja Nyesom Wike ya dauko hanyar kassara dimukuradiyya a Nijeriya. Wannan shi ne babban zargin da ke cikin wata zungureriyar wasika da ƙungiyar ta “Nigeria Unite” ta gabatar ga   shugabar hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen. Kungiyar mai rajin kare dimukuradiyya ta  nuna tsananin damuwa cewa dimokuradiyya a Nijeriya na dab da rugujewa — tare da zargin cewa Ministan Abuja, Barrister Nyesom Wike, na mamaye siyasa da karya tsarin mulkin Nijeriya.

A cikin wasikar da aka aika ranar 11 ga Nuwamba 2025, ƙungiyar ta ce halayen Wike da goyon bayan da yake samu daga gwamnatin tarayya sun jefa Nijeriya cikin hanyar zama ƙasar jam’iyya ɗaya, lamarin da ke shafar dimokuradiyya gaba ɗaya a kasashen yankin Sahel.

A cewar wasikar, Wike ana zarginsa da:

damfarar tsarin siyasa,

tsoratar da ‘yan adawa,

sayen hukumomi da alkalai,

murƙushe jam’iyyun PDP, LP da ADC,

kulle ofisoshin jam’iyyun adawa da amfani da albarkatun gwamnati don rushe su,

da kuma amfani da ’yan sanda, wasu alkalan tarayya, da ma’aikatan INEC wajen murde tsarin siyasa.


Wasikar ta ce dabi’un ministan na Abuja sun kai ga samar da :

rabuwar kawuna a tsakanin ‘yan majalisar Rivers saboda rikicinsa da Gwamna Sim Fubara,

ƙone majalisar dokoki da rikice-rikicen doka,

tilasta wa gwamnoni, sanatoci da manyan jam’iyyun adawa shiga APC,

da kuma karkatar da dimokuradiyya zuwa salon mulkin kama-karya.


Ƙungiyar ta gargadi cewa yadda “APC ke amfani da barazana, cin hanci, da cin zarafi don murƙushe adawa” na nuna cewa Nijeriya na dab da zama ƙasar jam’iyya ɗaya — abin da ka iya haifar da tarzoma da tashin hankali kafin zaɓen 2027.

Wasikar ta da kungiyar Nigeria ta aike wa kasashen Turai ta kuma zargi Majalisar Dokokin Nijeriya da zama mai “rauni kuma a ƙarƙashin ikon shugaba  Tinubu,” ta ce rashin sa hannun su wajen tsare doka da oda ya ƙara buɗe ƙofa ga zalunci da karya tsarin mulki.

A cikin buƙatunta, ƙungiyar Nigeria Unite ta roƙi Tarayyar Turai, Majalisar Dinkin Duniya, Amurka da Birtaniya su sa baki cikin lamarin, su sanya takunkumi kai tsaye kan Nyesom Wike, da kuma wasu alkalan da ake zargi suna taimaka masa.

Wasikar ta yi gargadin cewa duk wata rugujewar dimokuradiyya a Nijeriya — ƙasa mai mutane miliyan 250 — ka iya haifar da girgizar siyasa da tsaro a yammacin Afirka, ta ƙara yawan kwararar ’yan gudun hijira, ta kuma haifar da barazana ga Turai da Amurka.

A ƙarshe, ƙungiyar ta ce lokaci ya yi da kasashen duniya ya kamata su tashi tsaye domin “kare dimokuradiyya kafin lamarin ya rikide ya zama abin tsoro.

Libya ta kora ‘yan Nijeriya 80 gida saboda zama ba bisa ka’ida ba a kasar

0

Hukumomin Libiya sun kori ’yan Nijeriya 80 daga ƙasar bayan kama su suna zama ba bisa ƙa’ida ba, a wani yunkuri na rage cinkoso a cibiyoyin da ake tsare masu aikata irin laifin.

Hukumar yaki da masu shiga kasar ba bisa ka’ida ba tare da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Nijeriya da ke Tripoli ne suka jagoranci mayar da su ta filin jirgin sama na Mitiga International Airport a ranar Laraba.

Kungiyar Migrant Rescue Watch, wadda ke sa ido kan walwalar ’yan ci-rani a Libiya, ta bayyana cewa an kora mutanen ne bisa umarnin kotu da hukumar ’yan sanda ta fitar.

Majalisar dattawan Nijeriya na shirin haramta daukar ‘yan kasa da shekaru 18 aikin soji

0

Majalisar dattawan Nijeriya na shirin amincewa da kudurin da zai haramta daukar mutane ‘yan ƙasa da shekaru 18 a aikin soja.

Sanata Abdulaziz Yar’Adua daga Katsina ne ya gabatar da kudurin, wanda ke neman soke tsohuwar dokar soji ta 2004 tare da kawo sabuwar doka da ta dace da tsarin mulki da harkokin tsaro na zamani.

A yayin gabatar da kudurin, Sanata Yar’Adua ya ce tun da jimawa ake da bukatar gyaran, domin dokar da ake amfani da ita yanzu ta samo asali ne daga umarnin soja, wanda bai dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.

Ya ce sabuwar dokar za ta kawo canje-canje da dama, ciki har da tsaurara hukunci ga manyan laifukan soja, kare kotunan soja daga tsoma bakin manyan jami’ai, da tabbatar da cewa ƙwararrun lauyoyin soja za su iya kare rundunar a kotunan fararen hula.

Sojoji sun dakile yunkurin garkuwa da ‘yan bautar kasa

0

Dakarun haɗin gwiwa na “Operation Hadin Kai” sun dakile wani yunkurin garkuwa da masu yi wa kasa hidima 74 a hanyar Buratai zuwa Kamuya, jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar, Manjo Sani Uba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, inda ya ce sojojin sun yi gaggawar kai dauki bayan motocin ɗaliban sun lalace a wurin da ake yawan yin garkuwa da mutane.

A cewar sa, masu yi wa kasa hidimar maza 36 da mata 38, motar tasu ta lalace ne da misalin ƙarfe 9:05 na dare a ranar Talata.

Sojojin sun gano matasan suna cikin haɗari, suka garzaya suka kwashe su zuwa sansanin soja da ke Buratai don kare su daga yiwuwar hare-haren ‘yan ta’addan.