DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 107

Dole mu karfafawa sojoji gwiwa saboda sadaukar da rayukansu da sukai – Tinubu

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya jinjina wa maza da mata na rundunar sojojin Nijeriya bisa jajircewa da sadaukarwar da suke yi don kare ƙasar daga barazanar tsaro.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Tinubu ya bayyana hakan ne a taron ƙungiyar Editocin Nijeriya NGE da aka gudanar a Abuja a ranar Laraba, inda ya ce sojojin suna fuskantar haɗari domin kare mutuncin kasar.

Shugaban ya ce duk da ƙalubalen da ake fuskanta na ta’addanci da ‘yan bindiga, gwamnatinsa tana ɗaukar matakai don karfafa rundunar sojoji da sauran jami’an tsaro.

A cewar sa, ya zama wajibi a ci gaba da kare su da kuma ba su goyon baya duba da irin hadarin da suke fuskanta.

Muna biyan ‘yan bindiga Naira miliyan 7 don zama a gidajenmu ko noma gonakinmu

0

Wasu al’ummomi a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja sun bayyana cewa suna biyan haraji ga ‘yan bindiga domin su samu damar zama a garuruwansu ko kuma ci gaba da noma gonakinsu.

A cewar shugaban al’ummar, Alhaji Yahaya, wanda ya bayyana haka yayin wata hira da shi a shirin Tsalle Daya na tashar Prestige FM Minna, ya ce al’ummarsu ta na biyan ‘yan ta’adda Naira miliyan bakwai a matsayin kudi domin barinsu su zauna a mahalllansu.

Ya ce garuruwan da ke karkashin ikon ‘yan bindigar sun haɗa da Makera, Galapai, Chukuba, Ushaka, Manini, Kawuri, Bakarie I, Utako da Magana, inda kowane mutum mai aure ke ba da gudunmawa wajen tara kudin.

Ya ƙara da cewa ‘yan bindigar kan shigo cikin gari da bindigu har sai an ba su kuɗi, yayin da jami’an tsaro kuma suka daina yin sintiri a yankin.

Abin takaici ne a ce tawagar Super Eagles na bin bashi – Peter Obi

0

Tsohon ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar Labour Party a zaɓen 2023 Peter Obi, ya bayyana takaici kan rahotannin da ke nuna cewa tawagar wasan ƙwallon ƙafa ta Nijeriya Super Eagles na bin bashi na alawus-alawus da wasu kudaden aiki.

Obi ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Talata, inda ya ce lamarin na iya rage wa ‘yan wasa ƙwazo da ƙwarin gwiwar wakiltar ƙasarsu da cikin himma.

Ya ce gwamnati na da alhakin kula da walwalar ‘yan wasa, tare da tabbatar da biyan hakkokinsu cikin lokaci da ƙarfafa musu gwiwa domin ci gaba da ba da gudunmawa ga ci gaban wasanni.

Sheikh Gumi ya musanta cewa ya gudu daga Nijeriya zuwa Turkiyya saboda barazanar Trump

0

Fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa tafiyarsa zuwa ƙasar Turkiyya ba ta da alaka da barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yiwuwar kai hari a Nijeriya saboda zargin kisan Kiristoci.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, bayan da hotunan Sheikh Gumi suka bayyana yana cikin ƙasar Turkiyya, wasu mutane a kafafen sada zumunta sun yada labarin cewa malamin ya gudu ne don tserewa hare-haren da ake zargin Amurka za ta kai Nijeriya.

Wasu masu amfani da dandalin X sun yi tsokaci suna cewa Gumi na iya zama cikin wadanda za su fuskanci hare-haren Trump, kasancewar an taba ganinsa yana tattaunawa da wasu ’yan bindiga a dazuka.

Sai dai Sheikh Gumi ya ce ya dade yana shirin tafiya tun kafin wannan barazana ta Trump.

Gwamnonin Kaduna da Sokoto sun bukaci a gaggauta samar da ‘yansandan jihohi

0

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bukaci a kafa ‘yan sandan jihohi cikin gaggawa, yana mai cewa hakan ne kadai zai taimaka wajen kawo karshen matsalar tsaro a Nijeriya.

Uba Sani ya bayyana hakan ne a birnin Legas yayin wani taron da aka gudanar kan rawar da gwamnonin jihohi ke takawa domin yaki da matsalar tsaro.

Ya ce, rundunar tsaro irin su Amotekun a kudu maso yamma ba su da hurumin doka da zai ba su damar yaki da ‘yan ta’adda, saboda haka kafa ‘yan sandan jihohi ya zama wajibi idan har ana son kauda matsalar baki daya.

Gwamnan ya bayyana cewa Nijeriya na da ‘yan sanda kusan dubu 400 da kuma sojoji kasa da dubu 250, yayin da yawan jama’a ya haura miliyan 230.

Uba Sani ya kara da cewa gwamnatocin jihohi da sarakunan gargajiya ne suka fi sanin matsalolin tsaro a yankunansu, saboda haka dole a basu cikakken iko domin jagorantar wannan shirin na yaki da matsalar.

Tattalin arzikin Nijeriya zai ninku zuwa shekarar 2037 — Ministar Kudi

0

Gwamnatin Nijeriya ta ce tana kan hanyar ninka tattalin arzikinta bisa ma’aunin GDP zuwa shekara ta 2037, bisa hadin gwiwar da ke tsakanin ma’aikatar kudi da babban bankin Nijeriya (CBN).

Karamar ministar kudi, Doris Uzoka-Anite ce ta bayyana haka a ranar Talata a Abuja yayin da take gabatar da jawabi a taron shekara-shekara na manyan jami’an babban bankin Nijeriya.

Ta ce samun hadin kai tsakanin bangarorin da suka shafi kudi na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar.

A cewarta, burin gwamnati shi ne ta cimma karuwar GDP sama da kashi 4% a kowace shekara zuwa 2027, wanda hakan zai ninka darajar tattalin arzikin Nijeriya zuwa 2037 idan aka ci gaba da samun karuwar da ta kai kashi 7% a duk shekara.

Jam’iyyar PDP ta ce tana kan bakanta kan babban taron ta na kasa

0

Jam’iyyar adawa ta PDP a Nijeriya ta bayyana cewa ba za ta janye shirinta na gudanar da taron zaben shugabanninta na kasa da aka tsara a ranar 15 da 16 ga Nuwamba ba, duk da sabon umarnin kotun tarayya na hana yin taron.

Mataimakin mai magana da yawun jam’iyyar, Ibrahim Abdullahi, ya shaida wa Daily Trust cewa sabon hukuncin kotu bata lokaci ne kawai, yana mai cewa jam’iyyar na bin umarnin kotun koli wanda ya tabbatar da cewa jam’iyyu na da ikon gudanar da harkokinsu na cikin gida ba tare da tsoma bakin kotu ba.

Abdullahi ya ce PDP ba za ta lamunci abin da ya kira hukuncin da wasu suka tsara ba, yana mai jaddada cewa jam’iyyar ta samu kafuwa daga ‘yan Nijeriya ne ba daga kotu ba.

A ranar Talata da ta gabata mai shari’a Peter Lifu na kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da umarnin hana PDP gudanar da taron a Ibadan, tare da umartar INEC da kada ta sa ido ko ta amince da sakamakon taron, wanda ya biyo bayan karar da tsohon gwamnan Jigawa kuma dan takarar shugabancin jam’iyyar, Sule Lamido, ya shigar yana kalubalantar tsarin sayar da fom din takara.

Injiniya Sagir Koki ya fice daga jam’iyyar NNPP

0

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar birnin Kano a matakin tarayya Injiniya Sagir Ibrahim Koki, ya bayyana ficewarsa daga NNPP saboda rikicin cikin gida da ke kara kamari a cikin jam’iyyar.

A cikin wata wasika da ya rubuta ranar 11 ga Nuwamba, 2025, wacce ya tura wa shugabar jam’iyyar na mazabar Zaitawa, Koki ya ce ya dauki wannan mataki ne bisa tsarin dokar ƙasa da ke ba kowane ɗan Nijeriya ‘yancin shiga ko barin kowace jam’iyya.

Ya ce rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar a matakin kasa ya yi tsananin da har ya zama abin da ke hana shi gudanar da aikinsa yadda ya kamata da kuma wakiltar al’ummar Kano Municipal yadda ya kamata.

Hon. Koki, wanda aka zabe shi karkashin jam’iyyar NNPP a 2023, ya gode wa jam’iyyar bisa damar da ta bashi ya yi hidima ga al’umma, yana mai bayyana cewa goyon baya da amincewar da ya samu daga ‘ya’yan jam’iyyar sun kasance abin alfahari.

Majalisar wakilan Nijeriya ta katse zamanta na ranar Talata saboda muhawara kan kasafin kudin 2026

0

Majalisar wakilan Nijeriya ta katse zamanta na ranar Talata sakamakon zazzafar muhawara kan kasafin kudin 2026

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ba a samu gabatar da kuduri ko guda ba a zaman Talatar sakamakon daukar matakin, lamarin da ba a saba ganin irin sa ba.

Musayar yawu tsakanin ‘yan majalisar dai ya biyo bayan samun rabuwar kai game da yadda za a tafiyar da batun kasafin kudin Nijeriya na shekarar 2026.

Duk da cewa babu wata sanarwa a hukumance daga shugabancin majalisar, majiyoyi sun bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali ne kan wa’adin da aka bai wa ministocin kudi, kasafi da tsare-tsare tare da akanta janar na kasar, kan biyan basusukan da ‘yan kwangila ‘yan asalin Nijeriya ke bi.

‘Yan bindiga sun hallaka mai juna biyu a kauyen Alkalije da ke Sokoto

0

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Alkalije da ke karamar hukumar Yabo a jihar Sakkwato, inda suka hallaka mutane biyar ciki har da mace mai juna biyu da safiyar Litinin.

Majiyoyi sun ce maharan sun afka garin ne da sassafe suna harbe-harbe, inda wasu mazauna kauyen biyu suka samu raunuka kuma aka garzaya da su asibiti.

Garin Alkalije na karkashin masarautar Kilgori kuma yana iyaka da karamar hukumar Silame da wasu yankuna na jihar Kebbi, inda ake zargin ta nan maharan ke shigowa.

Wani dattijo a yankin ya ce ‘yan bindigar sun saba kai farmaki daga Kebbi da Silame, suna hallaka mutane da sace wasu, har ma suna kakaba haraji kan al’umma, inda ya roki gwamnati ta kafa sansanin tsaro a yankin domin dakile hare-haren.