DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 108

‘Yan bindiga sun hallaka mai juna biyu a kauyen Alkalije da ke Sokoto

0

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari garin Alkalije da ke karamar hukumar Yabo a jihar Sakkwato, inda suka hallaka mutane biyar ciki har da mace mai juna biyu da safiyar Litinin.

Majiyoyi sun ce maharan sun afka garin ne da sassafe suna harbe-harbe, inda wasu mazauna kauyen biyu suka samu raunuka kuma aka garzaya da su asibiti.

Garin Alkalije na karkashin masarautar Kilgori kuma yana iyaka da karamar hukumar Silame da wasu yankuna na jihar Kebbi, inda ake zargin ta nan maharan ke shigowa.

Wani dattijo a yankin ya ce ‘yan bindigar sun saba kai farmaki daga Kebbi da Silame, suna hallaka mutane da sace wasu, har ma suna kakaba haraji kan al’umma, inda ya roki gwamnati ta kafa sansanin tsaro a yankin domin dakile hare-haren.

PDP ƙarƙashin jagorancin Damagum na tattauna yiwuwar korar Wike daga jam’iyyar

0

Kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na duba yiwuwar korar ministan Abuja Nyesom Wike daga jam’iyyar, bisa bayanai da Daily Trust ta tattaro daga manyan majiyoyi a jam’iyyar.

Majiyoyin sun bayyana cewa da alama shugabannin jam’iyyar sun kai matakin gajiya da rikicin cikin gida da suke zargin Wike da haddasawa, kuma idan kokarin sulhu da kwamitin da Adolphus Wabara ke jagoranta ya ci tura, za a kori Wike daga jam’iyyar.

Wani jigo a jam’iyyar ya ce Wike ya nuna cewa sai ra’ayinsa kawai ake bi, kuma dukkan gwamnonin da ke kusa da shi sun kasa lallasar sa, kana ya ce babu yadda za a bari mutum ya ci-gaba da zama jagoran PDP alhali yana goyon bayan shugaban kasa daga jam’iyyar APC.

Wani babban jigo a Arewa ya kara da cewa yawancin mambobin NWC karkashin jagorancin Umar Damagum sun fara cimma matsaya kan korar Wike da magoya bayansa, domin dukkan yunkurin sasanci da aka yi tun bayan zaben 2023 sun gaza kawo sulhu.

An samu cacar baki tsakanin Wike da wani jami’in soja kan mallakar wani fili a Abuja

0

An samu musayar yawu a ranar Talata tsakanin ministan Abuja Nyesom Wike, da wani jami’in soja a yankin Gaduwa, Abuja, bayan takaddama kan iko da wani fili.

Bidiyon da aka gani ya nuna Wike yana zargin jami’in da mallakar filin ba bisa ka’ida ba, inda ya tambaye shi dalilin da ya sa sojoji ke iƙirarin mallakar filin a dalilin tsohon hafsan rundunar ruwan Nijeriya.

Jami’in, wanda ke sanye da kayan soji, ya ce an samu filin bisa doka kuma an bi dukkan ka’idojin da suka kamata, lamarin da ya fusata ministan har ya daka masa tsawa.

Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, rundunar sojin Nijeriya ko hukumar FCTA basu fitar da wata sanarwa ba.

Hukumar FCTA ta Abuja dai na ci-gaba da kokarin hana kwace filaye da gina gine-gine ba bisa ka’ida ba a fadin birnin.

Sanata daga jihar Cross River ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

0

Sanata Agom Jarigbe mai wakiltar mazabar Arewa ta jihar Cross River ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda ya sanar da majalisar dattawa ta hanyar aika wasiƙa a hukumance.

A yayin zaman majalisar da aka watsa kai tsaye a NASSTV a ranar Talata, mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Barau Jibrin, ya karanta wasiƙar ficewar sanatan, inda Jarigbe ya ce rikice-rikicen cikin gida a PDP ne suka tilasta masa daukar matakin ficewar.

Jarigbe ya bayyana cewa ya yanke wannan shawara ne bayan tunani mai zurfi kan halin da jam’iyyar ta tsinci kanta a matakin jiha da kasa, inda ya koka da rarrabuwar kawuna da rashin sulhu a cikinta.

A cewarsa, jam’iyyar APC ce ke ba shi cikakken dandali na ci-gaba da gudanar da ayyukan da za su amfani al’ummar mazabarsa.

Ana yunkurin tsige Akpabio daga shugabancin majalisar dattawan Nijeriya – Sanata Uzor Kalu

0

Tsohon gwamnan Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya yi zargin cewa lallai an shirya yunkurin tsige shugaban majalisar dattawan Nijeriya Godswill Akpabio.

Da yake zantawa da manema labarai a majalisar, Kalu ya ce batun ba jita-jita ba ne, domin wasu ‘yan majalisa sun taba tattaunawa kan hakan, sai dai shirin bai yi nasara ba.

Kalu ya bayyana cewa shi da wasu abokan aikinsa ba za su taɓa yarda da irin wannan yunƙuri ba, yana mai kira ga ‘yan majalisa su fifita zaman lafiya, hadin kai da muradun kasa.

A kan batun tsaro, Kalu ya ce yana goyon bayan kalaman tsohon shugaban Amurka Donald Trump, yana mai bayyana cewa taimakon sirri da diflomasiyya daga Amurka na kara karfafa Nijeriya wajen yaki da ta’addanci.

Kaso 75 cikin 100 na yara a jihar Katsina na fuskantar matsanancin talauci – UNICEF

0

Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ya bayyana cewa sama da kashi 75 cikin 100 na yara a jihar Katsina na fama da talauci ta fuskoki da dama, inda suke rasa muhimman abubuwan rayuwa kamar lafiya, abinci mai gina jiki, da ilimi.

Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ne ya bayyana haka a yayin taron horaswa na shugabannin kananan hukumomi 34 a jihar Katsina, wanda aka shirya don tattauna hanyoyin rage talaucin yara ta hanyar tsarin kariyar jama’a mai dogaro da sahihan bayanai.

Rahama ya bayyana cewa kididdigar hukumar kididdiga ta Nijeriya (NBS) da sauran hukumomi sun nuna cewa yawan mace-macen yara a jihar ya kai 159 cikin haihuwa dubu 1, wanda ke nufin yaro ɗaya cikin shida ba ya kai shekara biyar da rai.

Farah ya jaddada cewa zuba jari a kan yara wajibi ne, domin shi ne ginshiƙin da zai tabbatar da makoma mai ɗorewa da ci-gaba a jihar Katsina.

Kotu ta sake bayar da umarnin dakatar da babban taron jam’iyyar PDP na kasa

0

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta sake hana jam’iyyar PDP gudanar da taron gangamin ta na kasa da aka shirya yi a Ibadan, Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.

Kotun ta kuma hana hukumar zabe ta Nijeriya INEC sa ido kan taron da ake sa ran za a zabi sabbin shugabanni na kasa.

Mai shari’a Peter Lifu ne ya bayar da wannan sabon umarni a ranar Talata, bayan sauraron karar tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, wanda ya koka cewa an hana shi damar siyan fom din neman shugabancin jam’iyyar.

Alkalin ya ce PDP ta saba doka da sharuddan da ake bukata wajen shirya irin wannan taro, inda ya kara da cewa rashin bibiya da bin tsarin doka na iya zama barazana ga dimokuradiyya a kasar.

Gwamnati na tattaunawa da Amurka kan barazanar harin soji da Trump ya yi – Ministan yada labaran Nijeriya

0

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa tana tattaunawa da hukumomin Amurka kan barazanar soja da shugaban Amurka Donald Trump ya yi mata.

Ministan labarai da wayar da kan jama’a Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da Sky News, inda ya ce ana samun ci-gaba ta hanyar diflomasiyya wajen daidaita dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

Idris ya bayyana cewa wasu daga cikin bayanan da Amurka ke dogaro da su na da rauni, saboda rashin fahimtar yadda matsalar tsaro da bambancin ƙasar ke da sarkakiya.

Haka kuma ya musanta cewa Nijeriya ta rasa wani yanki ga ‘yan bindiga, yana mai cewa hakan ba gaskiya bane.

A cewar sa, Amurka ta kasance abokiyar haɗin gwiwa wajen yaƙi da ta’addanci, yana mai kira da ta ci-gaba da taimakawa domin samar da zaman lafiya a ƙasar.

‘Yan bindiga na kafa doka tare da karbar haraji a wasu yankuna na Arewa – Dambazau

0

Tsohon babban hafsan sojin kasa kuma tsohon ministan cikin gida na Nijeriya, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau mai ritaya, ya bayyana cewa ’yan bindiga da masu tayar da kayar baya sun mamaye wasu yankunan Arewa, inda suke karɓar haraji tare da kafa dokoki a cikin al’umma.

Dambazau ya bayyana haka ne a taron kafafen yada labarai da tsaro da aka gudanar a Birnin Kebbi, yana mai cewa matsalar tsaro a yankin ta haura shekaru ashirin, inda dubban mutane suka mutu miliyoyi suka rasa matsugunni, manoma da makiyaya kuma suka yi asarar dukiyoyinsu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Dambazau ya bukaci gwamnoni su kafa ma’aikatar albarkatun ma’adinai domin amfani da arzikin kasa wajen habaka tattalin arziki da rage talauci da rashin tsaro.

Haka kuma, ya nemi a farfaɗo da masarautu, a habaka noma, da rage yaran da ba sa zuwa makaranta domin dawo da zaman lafiya a yankin Arewa.

Gwamnati ta bukaci ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankalinsu kan barazanar Trump

0

Gwamnatin Nijeriya ta bukaci ’yan kasar su kwantar da hankalinsu dangane da sabanin diflomasiyya da ke tsakaninta da Amurka.

Ministan yada labarai Alhaji Mohammed Idris ne ya yi wannan kira yayin da ya kai ziyarar ban girma ga gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi a ranar Litinin.

A cewar sanarwar da Malam Rabiu Ibrahim, mataimakin minista na musamman kan yada labarai ya fitar a Abuja, Idris ya je Jigawa ne domin halartar taron matasan Arewa maso Yamma na 2025 da kuma gabatar da nasarorin da shugaba Tinubu ya cimma cikin shekaru biyu da suka gabata.

Ministan ya ce shugaba Tinubu na da cikakkiyar kwarewa da karfin guiwa wajen kare martabar Nijeriya da gyara duk wata matsala ta dangantaka da kasashe abokan hulɗa.

A cewarsa, ’yan Nijeriya kada su firgita, su kwantar da hankali, Tinubu zai iya warware lamarin cikin lumana kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.