DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
Home Blog Page 116

Gwamnan Katsina Radda ya gabatar da kasafin 2026 na Naira biliyan 897

0

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya gabatar da kasafin kudin jihar na shekarar 2026 wanda ya kai Naira biliyan 897.8 a zauren majalisar dokokin jihar, inda ya ce sabon kasafin ya fi na bara da kaso 29.7 cikin dari.

Radda ya ce kashi 81 cikin 100 na kudaden za a kashe su ne wajen manyan ayyukan ci-gaba, yayin da kashi 18.6 cikin 100 zai tafi wajen biyan albashi da sauran kudaden gudanarwa, kuma kasafin zai mayar da hankali kan fannin ilimi, lafiya, noma da samar da ruwa.

A cewar gwamnan, ma’aikatar ilimi ce ta samu kaso mafi tsoka da fiye da naira biliyan 156 domin bunkasa ingancin karatu da gina sabbin makarantu a fadin jihar wanda hakan na cikin kokarin gwamnatinsa na gina tushe mai karfi ga ci-gaban jihar.

Hakazalika, Radda ya ce za a cigaba da aiwatar da kasafin ta hanyar sauraron bukatun al’umma daga kananan hukumomi da kauyuka, tare da tabbatar da tsaro da farfado da tattalin arzikin karkara.

Kashim Shettima ya tafi Brazil domin halartar taron sauyin yanayi karo na 30

0

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bar Abuja zuwa Brazil domin wakiltar shugaba Bola Tinubu a babban taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya karo na 30 da za a gudanar a birnin Belém na kasar Brazil.

Taron, wanda shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva ke jagoranta tare da hadin guiwar wasu kasashe, zai gudana daga ranar 6 zuwa 7 ga watan Nuwamba, inda za a tattauna batutuwan da suka shafi kariyar dazuka, halittu, da adalcin yanayi.

Mai magana da yawun ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, ya bayyana cewa Shettima zai gabatar da jawabin Nijeriya kan sauyin yanayi, sannan ya halarci tarukan kwamitoci da za su tattauna batun canjin makamashi da yarjejeniyar Paris.

Haka kuma, Shettima zai yi ganawa da shugabanni da masu ruwa da tsaki don tattauna yadda Nijeriya za ta shiga kasuwar carbon finance da ake sa ran za ta samar da har dala biliyan uku a duk shekara.

China ta gargadi Amurka game da yi ma Nijeriya barazana da katsalandan

Gwamnatin kasar China ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu, tana mai gargadi ga kowace kasa da ke tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Nijeriya.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Mao Ning, ta bayyana haka ne a martani ga barazanar shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya zargi gwamnatin Nijeriya da kisan Kiristoci.

Trump ya ce zai dauki matakin soja da kuma katse tallafin Amurka idan gwamnatin Tinubu ta kasa shawo kan matsalar, amma kasar China ta ce irin wannan barazana ba ta dace da dangantakar kasa da kasa ba.

Mao Ning ta kara da cewa Sin na goyon bayan Nijeriya wajen tafiyar da mulkinta bisa tsarin da ya dace da yanayin kasar, tare da yin watsi da duk wani yunkurin amfani da addini a matsayin dalilin tsoma baki kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.

Ba a take hakkin Kiristoci a Nijeriya ba – Babban hafsan tsaron Nijeriya

0

Babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Olufemi Oluyede ya karyata ikirarin cewa ana zaluntar Kiristoci a Nijeriya, inda ya ce babbar matsalar Nijeriya ita ce ta’addanci.

Janar Oluyede ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin lokacin da ya mayar da martani kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump wanda ya zargim ‘yan ta’adda na kai hare-hare kan Kiristoci.

Oluyede ya ce sojojin Nijeriya na aiki tuƙuru wajen yaƙar ta’addanci da tabbatar da tsaro, tare da samun nasara sakamakon sabon tsarin tsaro da shugaba Tinubu ya kafa.

Hakazalika ya ƙara da cewa rundunar soji za ta cigaba da ƙoƙari wajen dawo da zaman lafiya tare da buƙatar haɗin kan ƙasashen duniya domin yaƙi da ta’addanci.

Ya kamata ka taka wa Matawalle burki – Jam’iyyar PDP ta shaida wa Tinubu

0

Kungiyar dattawan Arewa ta jam’iyyar PDP ta zargi ministan tsaron Nijeriya, Bello Matawalle, da jagorantar sauya shekar da dama daga PDP zuwa APC ta hanyar abin da ta kira cin hanci da tsoratarwa.

A wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na kasa, Dr Abbas Sadauki, ya fitar, ta ce, tsohon gwamnan na Zamfara yana amfani da mukaminsa da dukiyar da ya mallaka wajen jan magoya bayan PDP musamman a jihohin Zamfara da Kaduna su koma jam’iyyar APC.

Ƙungiyar ta ce matakin Matawalle wani yunkuri ne na raunana jam’iyyar PDP a yankin Arewa maso Yamma kafin zaɓen 2027, tana mai gargadin cewa, amfani da kuɗi da barazana wajen rusa jam’iyyar adawa na haifar da barazana ga dimokuraɗiyya.

Gwamnan Bayelsa, Douye Diri ya sauya sheka zuwa APC daga PDP

0

Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya bar jam’iyyar PDP ya koma APC a hukumance a wani biki da aka gudanar a filin wasa na Samson Siasia da ke Yenagoa a ranar Litinin.

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ne ya jagoranci tawagar manyan jiga-jigan APC ciki har da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da wasu gwamnoni.

Diri, wanda ya yi murabus daga PDP a watan Oktoba, ya bayyana cewa ya yanke shawarar komawa APC ne don ceto jihar Bayelsa daga halakar PDP wadda ya kira da jirgin da ke nitsewa kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Haka kuma ya kara da cewa, sauyawar tasa ba ta mutum daya ba bace, ta al’ummar Ijaw ce baki daya kuma yana yaba wa shugaba Tinubu bisa aiwatar da aikin hanya daga Legas zuwa Kalaba wadda ya ce soyayya ce ga mutanen Ijaw.

Shugaba Tinubu zai nada jakadun Nijeriya a kasashen wajen

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu na shirin kammala nadin jakadun da za su wakilci Nijeriya a kasashen waje bayan tsawon lokaci kasar na fama da gibi a diflomasiyya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun ce an shiga matakin karshe na tantance jerin sunayen da za a fitar, bayan da wasu daga cikin wadanda aka tura sun rasu, wasu sun yi murabus, ko kuma sun kai lokacin ritaya.

Rahotanni sun nuna cewa majalisar dattawa ta riga ta tantance wadanda aka turo tun da dadewa, sai dai a sake duba jerin domin tabbatar da cewa sunayen da ke ciki sun cancanta kafin a fitar da sakamakon karshe.

Real Madrid na da shiga rai amma burina yin nasara tare da Arsenal – William Saliba

0

Dan wasan baya na Arsenal, William Saliba, ya bayyana cewa sha’awar da Real Madrid ta nuna masa na da matukar daukar hankali, amma burinsa shi ne ya lashe kofuna tare da Arsenal kafin tunanin komawa wata kungiya.

A wata tattaunawa da gidan talabijin na Telefoot, Saliba ya ce, hakika yana da daukar hankali idan kulob kamar Real Madrid ta nuna sha’awa a kanka, amma yana so ya fara lashe kofuna da Arsenal kafin yin tunanin wani abu dabam.

Saliba, dan shekara 22, ya kasance ginshikin tsaron Arsenal tun bayan dawowarsa, inda ya taimaka wa kungiya ta fafata a manyan gasanni.

Wannan furuci nasa na nuni da cewa har yanzu yana da cikakken jajircewa ga Arsenal duk da rade-radin da ke danganta shi da Real Madrid da sauran manyan kungiyoyi.

Magoya bayan bangaren Wike sun mamaye hedkwatar PDP a Abuja

0

Wasu magoya bayan bangaren sabon mukaddashin shugaban jam’iyyar PDP, Mohammed Abdulrahman, sun mamaye hedkwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja, a ranar Litinin suna rera wakokin goyon baya, tare da bukatar bangaren Umar Damagum ya bar ofis nan take.

Rahotanni sun ce rikicin cikin gida na jam’iyyar ya kara kamari bayan dakatar da sakataren jam’iyya, Sanata Samuel Anyanwu, da lauya Kamaldeen Ajibade na tsawon wata guda, abin da ya haifar da kafa sabon bangare karkashin Abdulrahman.

A daya bangaren, magoya bayan ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, sun gudanar da taro a wani wuri daban inda suka sanar da dakatar da Damagum da kwamitinsa.

Jami’an tsaro sun bazu a wurin domin hana tashin hankali yayin da bangarorin biyu ke kokarin kwace ikon ginin jam’iyyar, inda bangaren Abdulrahman ya mamaye ofishin shugaban jam’iyya na kasa.

An rantsar da shugabar kasar Tanzania, Samia Suluhu

0

Shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta karbi rantsuwa a ranar Litinin bayan zaben da aka yi cikin tashin hankali kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Jam’iyyar adawa ta Chadema ta ce daruruwan mutane sun rasa rayukansu a hannun jami’an tsaro amma hukumar zabe ta bayyana cewa Suluhu ta lashe zaben da kashi 98 cikin dari.

An gudanar da bikin rantsuwar a fadar gwamnati da ke Dodoma ba tare da halartar jama’a ba, yayin da intanet ke a katse gaba ɗaya tun ranar zabe, wanda hakan ya hana samun sahihan bayanai daga kasar.

Wata majiyar diflomasiyya ta ce an samu rahotannin mutuwar mutane da dama a asibitoci, yayin da Chadema ta bayyana cewa sama da mutum 800 ne suka rasa rayukansu, duk da cewa babu tabbacin wannan adadi.

Hukumomin kasar sun musanta zargin amfani da karfin iko, yayin da makarantu da sufuri suka tsaya cak a fadin kasar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.