DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
Home Blog Page 117

Rikicin PDP na kara yin kamari yayin da bangarorin Damagum da Anyanwu ke shirin shiga ofishin jam’iyyar a lokaci guda

0

Da yiyuwar kara samun rikici a jam’iyyar PDP yayin da bangarorin shugaban jam’iyya Umar Damagum da sakatare Samuel Anyanwu ke shirin komawa aiki a ofishin jam’iyyar na kasa da ke Wadata Plaza, Abuja, a yau Litinin.

A ranar Asabar, bangaren Damagum ya gudanar da taro a Legacy House da ke Maitama, yayin da bangaren Anyanwu kuma ya yi nasa taron a ofishinsa da ke Wuye a Abuja.

Wata majiya daga jam’iyyar ta shaida wa Daily Trust cewa duka bangarorin biyu na shirin yin aiki a ofishin jam’iyyar guda, abin da ke haifar da fargaba a tsakanin ma’aikata na jam’iyyar.

Majiyar ta kara da cewa bangaren Nyesom Wike na kokarin jan hankalin wasu mambobin kwamitin gudanarwa domin samun rinjaye a cikin jam’iyyar, lamarin da zai iya haddasa sabon rikici idan duka bangarorin suka hadu a ofishin a yau.

Amurka na shirin kakaba takunkumi ga gwamnonin Arewa 12 da wasu sarakunan gargajiya

Gwamnonin Arewa 12 da wasu sarakunan gargajiya da ma wasu manyan alkalai sun shiga cikin wata sabuwar ce-ce-ku-ce ta diflomasiyya bayan Majalisar dokokin Amurka ta fara nazarin wani kudiri da zai iya sanya musu takunkumi.

Amurka ta na zarginsu da hannu a kisan kiyashi kan Kiristoci da cin zarafi ta hanyar dokokin shari’a da batun raina addini a Nijeriya.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai damuwa ta musamman tare da umartar sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da ya dauki mataki cikin lokaci.

Kudirin da Sanata Ted Cruz ya dauki nauyi, mai suna “Nigeria Religious Freedom Accountability Act 2025”, yana neman sanya takunkumi kan manyan jami’an gwamnati, sarakuna, da alkalai da ake zargi da amincewa ko tallafawa cin zarafi kan Kiristoci da sauran ƙananan ƙungiyoyin addini kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.

Idan aka amince da kudirin, za a iya sanya musu takunkumin hana visa, toshe asusun banki da sauran takunkumin kudi bisa tsarin dokar Global Magnitsky, musamman ga gwamnonin jihohi 12 da suka aiwatar da dokar Shari’a mai cike da sabani a tsakanin Kiristoci da Musulmi.

Akpabio ya musanta yin izgilanci ga Trump kan barazanar yaƙi da Nijeriya

0

Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya musanta wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa ya yi izgilanci ga shugaban Amurka Donald Trump kan barazanar yaƙi da Nijeriya.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Eseme Eyiboh, ya fitar a Abuja ranar Litinin, Akpabio ya ce kalaman da aka danganta masa ƙarya ce kuma ƙoƙari ne na tayar da husuma tsakanin shi da shugaban Amurka.

A cewarsa, rubutun da wata kafar sada zumunta mai suna Rant HQ ta wallafa ba gaskiya ba ne, tare da zargin masu yada shi da neman haddasa rikici tsakanin Nijeriya da Amurka.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, sanarwar ta ƙara da cewa hoton da aka haɗa da rubutun an yi amfani da shi ne wajen ƙara wa ƙaryar armashi, domin ya sa jama’a su gaskata abin da bai furtawa ba.

Hukumomin kasar Nijar sun sake kama shugaban RTS da wasu ‘yan jaridu uku

0

‘Yan jaridu hudu ne da suka hada da shugaban gidan rediyo da talabijin sarauniya, kuma wakilin sashen Faransanci na RFI, Moussa Kaka hukumomin Nijar suka kama a ranar Lahadi 2 ga watan Nuwamba 2025.

Sauran ‘yan jaridar sun hada da editan sarauniyar, Ibro Chaibou da kuma wasu fitattun ‘yan jarida na Nijar irin su Souleymane Brah, da Oumarou Kane, da Seriba Yousouf

Daman a ranar 30 ga watan Oktoban da ya gabata ne aka kama shugaban kafar yada labaran ta Saurauniya kafin daga bisani a sake shi.

SERAP ta maka Akpabio da Abbas kotu kan zargin cin hanci na Naira miliyan 3 a majalisar dokoki

0

Kungiyar SERAP ta shigar da shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, kotu saboda kin bincikar zargin cewa ‘yan majalisa suna biyan har Naira miliyan uku domin gabatar da kudiri ko koke a majalisar.

Karar ta biyo bayan wani faifan bidiyo da dan majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Ibrahim Auyo, ya yada inda ya ce ana karɓar tsakanin Naira miliyan 1 zuwa 3 domin a gabatar da kudiri ko koke a majalisar.

SERAP ta nemi kotu ta tilasta wa Akpabio da Abbas su mika lamarin ga hukumomin yaki da cin hanci don bincike da gurfanarwa, tare da daukar matakan kare Ibrahim Auyo da ya fallasa zargin.

Kungiyar ta ce wannan zargi babban cin amanar jama’a ne da ya sabawa rantsuwar kama aiki, tana mai jaddada cewa bai kamata cin hanci ya zama sharadi wajen gudanar da ayyukan majalisa ba.

Taimako Nijeriya ke buƙata daga Amurka wajen yaki da matsalar tsaro ba tsoratar da ita ba – Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

0

Tsohon gwamnan Jihar Kano, kuma Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan yadda Shugaban Amurka Donald Trump ke ta yin maganganu masu tsanani kan Nijeriya, bayan sanya ta cikin jerin kasashen da ake kiran “ƙasashe masu damuwa ta musamman.”

Kwankwaso ya ce Nijeriya ƙasa ce mai cikakken ‘yancin kanta, wacce matsalolinta na tsaro ba su da alaƙa da addini ko kabila. Sannan kuma zai fi dacewa Amurka ta taimaka da sabbin fasahohi wajen yaki da ‘yan ta’adda, maimakon yin barazana da ka iya rarraba ƙasar.

Kwankwaso ya kuma bukaci gwamnati ta nada jakadu na musamman domin tattaunawa da gwamnatin Amurka, tare da tabbatar da jakadun dindindin don kare muradun Nijeriya a kasashen waje.

A karshe, Kwankwaso ya kira ‘yan Nijeriya da su hada kai a wannan lokaci maimakon rarrabuwa sannan yana mai yi ma kasar fatan alheri.

Gwamnan Kaduna ya yi sabbin nade-nade 34 a jihar

0

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da nadin jami’ai 34 tun daga kwamitoci, hukumomi, da mukaman shawara daban-daban a fadin jihar domin inganta gudanar da gwamnati da kuma karfafa ayyukan jama’a.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Lahadi, an bayyana cewa nadin na da nufin bai wa kwararru masu hazaka da kwarewa damar ba da gudummawa ga cigaban tattalin arziki da siyasar jihar.

Daga cikin sabbin nade-naden akwai Dr. Suwaiba Shehu Ibrahim, da aka nada a matsayin shugabar hukumar Ilimin sakandare ta jihar Kaduna, ta taba zama sakatariyar dindindin a hukumar koyar da malamai ta jihar, kuma malama ce a Jami’ar Kaduna.

Sauran mambobin sun hada da Nita Byack George, Monday Tela Bako, Aliyu Haruna Ahmed, da Hon. Aliyu Ibrahim, yayin da Muhammad Kabir Uthman, lauya kuma masani a fannin gudanarwa, ya zama sakataren hukumar.

Nijeriya a shirye take ta karbi taimakon Amurka wajen yaki da ‘yan bindiga muddin za a mutunta ‘yancinta – Gwamnatin Nijeriya

0

Biyo bayan barazanar da shugaban Amurka, Donald Trump ya yi na ɗaukar matakin soja kan zargin cin zarafin Kiristoci a Nijeriya, gwamnatin Nijeriya ta ce za ta yi maraba da taimakon Amurka wajen yaƙi da ‘yan ta’adda muddin za a mutunta cikakken ‘yancinta na cikin gida.

Trump ya wallafa a shafinsa cewa ya umurci ma’aikatar tsaron Amurka ta shirya matakin gaggawa idan Nijeriya ta gaza dakatar da kisan Kiristoci, tare da barazanar dakatar da duk wani tallafi kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Daniel Bwala, ya ce Nijeriya za ta karɓi duk taimako muddin ana mutunta huruminta, yana mai cewa taron da ake shirin gudanarwa tsakanin Tinubu da Trump zai taimaka wajen ƙarfafa haɗin kai kan yaƙi da ta’addanci.

Tun da farko dai, shugaba Bola Tinubu ya musanta zargin wariyar addini, yana mai cewa gwamnatinsa tana aiki tare da shugabannin addinai don tabbatar da tsaro da kare ‘yancin kowane ɗan ƙasa, Musulmi ko Kirista.

Shugaba Tinubu na amfani da karfi ga ‘yan adawa domin sauya sheka zuwa APC, in ji jam’iyyun adawa a Nijeriya

0

Wasu jam’iyyun adawa a Nijeriya na zargin Shugaba Bola Tinubu da amfani da kudaden gwamnati da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin tilasta wa ‘yan adawa su koma jam’iyyar APC.

A cewar kakakin jam’iyyun PDP, NNPP da CUPP, wato Debo Ologunagba, Oladipo Johnson, da Mark Adebayo, sauya shekar da ake ta gani daga ‘yan adawa zuwa APC na nuna cewa jam’iyyar mai mulki na dab da rugujewa daga ciki.

Sai dai kakakin yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya karyata zargin, yana mai cewa wadanda suka koma jam’iyyar sun yi hakan ne da son ransu saboda irin nasarorin da APC ke samu a mulki, kuma jam’iyyar na da cikakken tsari da zai hana ta fadawa rikicin cikin gida.

Zargin Trump na kisan Kiristoci a Nijeriya ba gaskiya ba ne, cewar wani lauya a Nijeriya

0

Wani lauya kuma tsohon mai ba da shawara ga shugaban kasa, Chief Okoi Obono-Obla, ya zargi Shugaban Amurka Donald Trump da wasu bangarorin gwamnatin Amurka da yin nuni da karya da kuma raini kan zargin cewa ana kisan Kiristoci a Nijeriya.

Yayin da yake magana a Calabar a ranar Lahadi, Obono-Obla ya bayyana matakin Amurka a matsayin diplomasiyya mai cike da ruɗani wadda ke nuna girman kai da son nuna karfi, yana mai cewa Amurka na amfani da batun addini ne domin kawo rudani a Nijeriya.

Okoi ya kara da cewa, ita kanta Amurka na fama da hare-haren ‘yan bindiga a majami’u amma ba ta bukaci sojojin kasashen waje su shigo mata ba, to bai kamata ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Nijeriya ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, lauyan ya gargadi Amurka da cewa duk wani yunƙuri na kutse a cikin harkokin Nijeriya da sunan kare addini zai zama karya doka a matakin kasa da kasa.