DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
Home Blog Page 118

Nijeriya za ta karbi bashin Dala biliyan daya daga bankin duniya

0

Bankin Duniya ya shirya amincewa da bashin dala biliyan ɗaya ga Nijeriya a ranar 16 ga watan Disamba, ƙarƙashin shirin saka hannun jari da samar da ayyukan yi a Nijeriya.

Bashin, wanda ya ƙunshi dala miliyan 500 na IDA da dala miliyan 500 na IBRD, zai tallafa wa sauye-sauyen tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da ƙarfafa saka hannun jari daga kamfanoni masu zaman kansu.

A cewar bankin, za a gudanar da shirin ta ma’aikatar Kudin Nijeriya, don taimaka wa Nijeriya ta tashi daga matakin farfaɗo da tattalin arziki zuwa ci-gaba mai ɗorewa ta hanyar rage hauhawar farashi da bunƙasa fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Jam’iyyar SDP ta jaddada dakatarwar da ta yi ma El-Rufai na tsawon shekaru 30

0

Kungiyar shugabannin jam’iyyar SDP na jihohi 37 ta tabbatar da cewa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, har yanzu yana cikin dakatarwa daga jam’iyyar na tsawon shekaru 30.

Wannan sanarwa ta fito ne bayan jita-jitar da ke yawo cewa El-Rufai na shirin komawa cikin jam’iyyar kafin babban taronta na kasa.

Shugaban kungiyar, Femi Olaniyi, ya shaida wa jaridar PUNCH a ranar Lahadi an Abuja cewa, babu komawa baya a kan hukuncin da kwamitin gudanarwa na kasa ya dauka kan El-Rufai.

A cewarsa, El-Rufai ya shiga jam’iyyar ne ta bayan gida kuma tun a ranar 3 ga watan Afrilu, 2025 an bayyana cewa duk wanda ke son shiga jam’iyyar sai ya bi matakin ofishin mazaba da na jiha, amma El-Rufai bai bi wannan hanya ba. Don haka ne kwamitin kasa ya dakatar da shi har na shekaru 30, kuma wannan hukunci ba zai canza ba.

Shugaba Tinubu zai gana da Trump ba da jimawa ba, in ji Daniel Bwala

Fadar shugaban Nijeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu da shugaban Amurka, Donald Trump za su gana a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a kasar.

Wannan na zuwa ne bayan kalaman Trump da suka zargi gwamnatin Nijeriya da rashin daukar mataki kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci, inda ya kuma yi barazanar kai hari a Nijeriya da kuma dakatar da tallafin Amurka.

Mai ba shugaban kasar shawara Mr Daniel Bwala ya ce shugabannin biyu na da kyakkyawar alaka wajen yaki da ta’addanci, inda ya kara da cewa gwamnatin Trump ce ta amince da sayar wa Nijeriya makamai, kuma gwamnatin Tinubu ta yi amfani da damar wajen samun gagarumar nasara a yaki da ta’addanci.

PDP Bangaren Wike ya dakatar da Damagum yayin da sabon rikicin shugabanci ya sake kunno kai a jam’iyyar

0

Jam’iyyar PDP ta sake fadawa cikin rikici yayin da sabuwar rarrabuwar kai ta kunno kai a cikin shugabancinta, inda wani bangare mai goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sanar da dakatar da mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Umar Damagum, da wasu mambobin kwamitin gudanarwa guda biyar.

Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Asabar a madadin bangaren, sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya bayyana mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa ta Tsakiya, Mohammed Abdulrahman, a matsayin sabon mukaddashin shugaban jam’iyyar.

Anyanwu ya ce an dakatar da Damagum bisa rashin iya aiki, almundahana, da kin bin hukuncin kotu, tare da tura shi gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar.

Haka kuma ya kara da cewa an dakatar da mai magana da yawun jam’iyyar, Debo Ologunagba, bisa fitar da sanarwa ba tare da izini ba, sai mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin kudu, Taofeek Arapaja, da kuma mai kula da harkokin kudi, Daniel Woyenguikoro, bisa zargin almundahana.

Hakazalika, an dakatar da shugaban matasa na kasa, Sulaiman Kadade, da mataimakin sakataren kasa, Setonji Koshoedo, na tsawon kwanaki 30 kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sai dai a baya, kwamitin karkashin jagorancin Damagum shi ma ya dakatar da Sanata Samuel Anyanwu, lauyan jam’iyyar, Kamaldeen Ajibade (SAN), da wasu mambobi biyu, abin da ya kara tsananta rikicin cikin gida da jam’iyyar ke ciki a halin yanzu.

Jam’iyyar PDP ta dakatar da mambobinta hudu na tsawon wata daya

0

Kwamitin Ayyuka na Kasa na jam’iyyar PDP ya dakatar da mai ba da shawara kan harkokin shari’a na kasa, Kamaldeen Ajibade (SAN), sakataren jam’iyya na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, mataimakin mai ba da shawara kan shari’a, Okechukwu Osuoha da kuma sakataren shirya taruka na kasa, Umaru Bature, na tsawon wata guda bayan hukuncin kotu da ya dakatar da taron gangamin jam’iyyar da aka shirya.

Jaridar Punch ta ruwaito mai magana da yawun jam’iyyar, Debo Ologunagba, ne ya bayyana haka yayin da yake magana da manema labarai a ranar Asabar, bayan taron gaggawa da kwamitin ya gudanar a ofishin jam’iyyar da ke a Maitama, Abuja.

Ologunagba ya ce kwamitin ya dauki matakin ne bisa tanadin kundin tsarin jam’iyyar, tare da mika wadanda abin ya shafa ga kwamitin ladabtarwa domin daukar matakin da ya dace.

PDP ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin dakatar da babban taronta a Ibadan

0

Jam’iyyar PDP ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin kotun tarayya da ta dakatar da gudanar da babban taronta da aka shirya yi a Ibadan, jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya fitar a ranar Juma’a, PDP ta bayyana hukuncin a matsayin kutse ga tsarin dimokuradiyya, tana mai jan hankalin mambobinta da su ci gaba da shirin taron ba tare da rudani ba.

Jam’iyyar ta ce ta umarci lauyoyinta su daukaka kara nan take, tare da jaddada cewa hukuncin bai hana ta ci-gaba da shirye-shiryen gudanar da taron da zai zabi sabbin shugabannin jam’iyyar ba, domin ci-gaba da kare dimokuradiyya a Nijeriya.

Matatar man Dangote ta yi alkawarin samar da wadataccen man fetur a lokacin bukukuwan karshen shekara

0

Matatar man Dangote ta tabbatar da cewa za ta samar da isasshen man fetur da dizal a fadin Nijeriya a lokacin bukukuwan karshen shekara domin a cewar kamfanin, yawan man da ake tacewa a kullum yanzu ya haura abin da ake bukata.

Mai kula da harkokin yada labarai da dabarun kasuwanci na rukunin kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka samu daga ofishinsa a ranar Asabar, inda ya ce matatar tana fitar da lita miliyan 45 na fetur da lita miliyan 25 na dizal a kullum.

Chiejina, ya ce kamfanin na aiki tare da hukumomi da masu rarraba man domin tabbatar da isar sa cikin sauki a fadin kasar.

A cewarsa, karuwar tace man a cikin gida na taimakawa wajen karfafa Naira ta hanyar rage kudaden da ake fitarwa waje da kuma karfafa kudaden da ke shigowa cikin gida.

Nijar da Chadi na son karfafa dangantakarsu

0

Kasashen Nijar da Chadi sun kammala wani taron hadin gwiwa na kwanaki biyu da suka gudanar a birnin N’djamena na kasar Chadi karkashin jagorancin Firaministocin kasashen biyu.

A yayin taron kasashen biyu sun kara jaddada dadaddariyar yarjejeniyar dangantakar da ke a tsakaninsu tare da rattaba hannu kan wadansu sabbi.

Nijar da Chadi na da dadaddiyar dangantaka mai kyau a tarihi a matsayin su na kasashe makwabtanta juna.

Matsalar Nijeriya ba ta addini ba ce illa rashin shugabanci nagari – Sowore

0

Dan gwagwarmayar kare hakkin dan’Adam kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya mayar da martani ga kalaman shugaban Amurka, Donald Trump da ya bayyana cewa Kiristoci na fuskantar barazana a Nijeriya.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, Sowore ya ce ceto Nijeriya ba zai fito daga waje ba, sai dai daga ingantaccen shugabanci a cikin gida. Sannan matsalar Nijeriya ba ta takaita ga addini ba, illa sakacin gwamnati, cin hanci, da rashin shugabanci mai nagarta.

Jaridar Punch ta ruwaito Sowore ya kara da cewa duka Kiristoci da Musulmai na fama da hare-haren ‘yan bindiga da talauci a sassa daban-daban na kasar, maimakon a rika kallon matsalolin tsaro ta fuskar addini, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su hada kai wajen neman shugabanci nagari da kare rayukan jama’a.

Nijeriya ta musanta zargin Trump kan kisan Kiristoci a kasar

Gwamnatin Nijeriya ta musanta maganganun shugaban Amurka, Donald Trump, da ke cewa ana yawan kisan Kiristoci a Nijeriya tare da kiranta “kasa mai matsalar tauye ‘yancin addini.”

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a safiyar Asabar, gwamnatin ta ce wadannan zarge-zargen ba su da tushe kuma ba su bayyana ainihin halin da ake ciki a kasa ba.

Sanarwar ta kara da cewa, karkashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu, Nijeriya na ci gaba da yaki da ta’addanci tare da karfafa zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai, da kuma kare rayuka da hakkin ‘yan kasa kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hakazalika, sanarwa ta ce gwamnatin Nijeriya za ta cigaba da tattaunawa da gwamnatin Amurka domin kara fahimtar juna kan kokarin da ake yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.