DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
Home Blog Page 119

Yadda fitinar bayan zabe ta yi ajalin mutane sama da 700 a Tanzaniya

Jam’iyyar adawa ta Chadema a Tanzaniya ta bayyana cewa fiye da mutane 700 ne suka mutu cikin kwana uku na zanga-zangar bayan zaɓen shugaban ƙasa, wadda ta haifar da tarzoma da tsaurara matakan tsaro a fadin ƙasar.

A cewar rahoton jaridar Daily Trust, zaɓen ya gudana ne cikin tashin hankali, katsewar intanet da kulle hanyoyin sadarwa, lamarin da ya sa ake diga ayar tambaya kan sahihancin zaɓen da gaskiyar sakamakon.

DCL Hausa ta ruwaito cewa, shugabar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan, mai shekara 65, wadda ke neman wa’adin farko cikakke a ƙarƙashin jam’iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM), ta fuskanci hamayya daga ‘yan takara 16. Sai dai hana wasu manyan ‘yan adawa shiga takara da shari’o’in da ke ci gaba, sun jefa shakku cikin tsarin.

Kakakin jam’iyyar Chadema, John Kitoka, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa adadin mutanen da suka mutu a babban birnin kasar, Dar es Salaam ya kai kusan 350, yayin da a a birnin Mwanza ya wuce 200. AFP ya ce jimillar ta kai kusan 700, kuma “na iya ƙaruwa” saboda an kafa dokar hana fita da dare tun ranar Laraba.

Tinubu ya umurci sabbin hafsoshin tsaro da su murƙushe duk wata barazanar tsaro

0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci sabbin hafsoshin tsaron da su tashi tsaye wajen murƙushe duk wata barazanar tsaro da ke tasowa a sassan Nijeriya.

Da yake bayani bayan tattabatar dasu a fadarsa a Alhamis dinnan, Tinubu ya ce barazanar tsaro na ta karuwa, kuma abin damuwa shi ne fitowar sabbin kungiyoyin ‘yan ta’adda a yankunan Arewa ta tsakiya, Arewa maso yamma da kuma wasu sassa na Kudu.

Ya ƙara da cewa ‘yan Nijeriya na bukatar zaman lafiya cikin gaggawa, don haka ya bukaci hafsoshin su yi aiki da kishin ƙasa.

Sojojin da ake tsare da su bisa zargin juyin mulki a Nijeriya sun kai 42 a wani binciken jaridar Daily Trust

Yawan sojojin da ake tsare da su bisa zargin yunƙurin juyin mulki ya ƙaru zuwa 42, kamar yadda majiyoyi daga cikin rundunar sojin suka tabbatar wa jaridar Daily Trust.

Majiyoyin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa, har yanzu ana ci gaba da gano yadda kowannensu ya taka rawa da yadda shirin ya faro.

Majiyar ta kara da cewa hukumar leken asiri ta sojoji DIA da na ci gaba da bin diddigin lamarin,yayin adadin wadanda ake zargi ya karu daga 16, zuwa 42.

Sai dai mai bai wa shugaba Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce fadar shugaban kasa na tare da matsayar rundunar tsaron kan wannan batu.

Barayin daji sun yi ajalin Dagacin kauye a jihar Sokoto

0

‘Yan bindiga sun kai mummunan hari a kauyen Kurawa, karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto, inda suka halaka mutane uku ciki har da dagacin kauyen.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare, inda maharan suka kai farmaki bayan sun rushe katangar da mutane suka yi a matsayin kariya daga hare-hare.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa sun samu bayani daga wani kauye a makwabta cewa ‘yan bindiga na kan hanyarsu zuwa Kurawa, inda suka hanzarta sanar da hukumomin tsaro.

Duk da haka, bayan da ‘yan bindigar sun shiga kauyen, suka fara harbe-harbe na kusan mintuna 30, inda jami’an tsaro da vigilante suka yi ƙoƙarin fatattakar su.

Sai dai duk da hakan, dagacin garin, Hussaini Alhaji Yawalle, da wasu mutum biyu sun mutu a harin.

Majalisar Dattawa ta tabbatar da Bernard Doro a matsayin Minista

0

Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da Bernard Doro a matsayin sabon minista, bayan tattaunawa da shi da ta ɗauki kusan mintuna 30.

Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa Doro, shi ne mutum na uku da aka naɗa daga Jihar Filato, ya yi alkawarin yin aiki cikin tsari, gaskiya da jinkai.

Majalisar ta nuna gamsuwa da ƙwarewar aikin sa, sannan ta bukace shi da ya yi aiki domin al’umma.

Sulhu da ‘yan bindiga ba tare da an karbe makamansu ba, hatsari ne mai girma – Gwamna Dauda

0

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gargadi gwamnoni da hukumomin tsaro da su guji sulhu da ‘yan ta’adda da ba tare da an karɓe makamansu ba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman idris ya fitar Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani jawabi da ya gabatar a cibiyar nazarin tsaro ta kasa NISS da ke Abuja a ranar Laraba.

Gwamnan ya ce, yaki da ‘yan bindiga a Zamfara ya samo asali ne daga matsalolin tattalin arziki, rashin aikin yi, rikice-rikice da yaduwar makamai daga kasashen makwabta.

Gwamna Lawal ya jaddada cewa tatttaunawa da ‘yan ta’adda ba tare da an kwace makamansu ba ba dai-dai bane,zaman lafiya yana samuwa ne idan aka yi afuwa tare da karɓe makamansu,domin idan aka barsu da bindigu rikici ba zai kare ba.

Daukacin ‘yan majalisar wakilan jihar Enugu sun koma APC

Shugaban majalisar wakilan Nijeriya Tajudeen Abbas, ne ya sanar da hakan a zaman majalisar da aka yi a Alhamis dinnan, inda ya karanta wasikun sauyin shekar da ‘yan majalisar suka aika masa,wanda Gwamnan Enugu, Barista Peter Mbah, ya halarci zaman.

‘Yan majalisar da suka sauya sheƙa sun ce sun bar jam’iyyunsu ne saboda rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyun adawa.

Bayan zaɓen 2023, jam’iyyar Labour ce ta lashe kujeru bakwai cikin takwas na jihar Enugu, yayin da PDP ta samu kujera ɗaya.

Muna so a ba mu damar kafa karin kananan hukumomi – Gwamnatin Bauchi

0

Gwamnatin jihar Bauchi ta mika bukatar neman a bata damar kirkirar sabbin kananan hukumomi 29 a jihar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa mataimakin magatakardar Majalisar Dokokin jihar Bauchi, Musa Yerima, ne ya aika da bukatar neman sahalewar kwamitin gyaran kundin tsarin mulki na kasa domin amincewa.

A halin yanzu, Bauchi na da kananan hukumomi 20 da kundin tsarin mulki na 1999 ya amince da su,idan aka ƙara waɗannan sabbin guda 29 da ake nema, yawan kananan hukumomin jihar zai kai 49,wadda ke da kusan al’umma miliyan 10.

A cikin wasikar da Yerima ya aika wa shugaban kwamitin Majalisar Dattawa kan gyaran kundin tsarin mulki, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa suna neman sabbin kananan hukumomin ne bisa tanadin Sashe na 100, sakin layi na 3 na kundin tsarin mulki, kuma ana neman sahalewar Majalisun kasar ta amince da su bisa Sashe na 8(5).

Tinubu ya amince da sabon harajin 15% ga masu shigo da fetur da dizal a Nijeriya

0

Wannan umurni na Tinubu ya fito ne a cikin wata wasika da aka aika wa hukumar tattara haraji ta kasa FIRS da hukumar kula da albarkatun man fetur ta NMDPRA, wadda mai taimaka masa na musamman, Damilotun Aderemi, ya sanya wa hannu a ranar 21 ga Oktoba 2025.

Shugaban FIRS, Zacch Adedeji, ne ya gabatar da wannan shawarwarin ga shugaban ƙasa, inda ya bayyana cewa harajin zai taimaka wajen karfafa masana’antun tace mai, tabbatar da daidaiton farashin mai, da kuma kare darajar Naira a kasuwar mai.

Adedeji ya bayyana cewa rashin daidaito tsakanin farashin man da ake tacewa a gida da wanda ake shigowa da shi daga waje yana janyo tashin farashi a kasuwa.

Gwamnatin Tanzaniya ta umurci ma’aikata su yi aiki daga gida, bayan rikicin zabe

0

Gwamnatin kasar Tanzaniya ta umurci dukkan ma’aikatan gwamnati su ci gaba da yin aiki daga gida, yayin da ta kuma shawarci masu aikin kamfanoni masu zaman kansu su ba ma’aikatansu dama su yi aiki daga gida.

DW Africa ta rawaito cewa, a wani sako da sakataren ma’aikatar yada labarai ta Tanzaniya, ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya nemi ‘yan kasar su gudanar da harkokinsu daga gida saboda halin da ake ciki.

Wannan umarni ya zo ne bayan da gwamnati ta kakaba dokar hana fita da a Dar es Salaam sakamakon tashin hankali da ya biyo bayan rikicin zaɓe da ya barke a ranar Laraba.

Rahotanni sun bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a yayin da hukumomi ke kokarin dawo da zaman lafiya a babban birnin ƙasar.