DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
Home Blog Page 120

Za a kawar da talauci a Nijeriya kafin shekarar 2030 – Gwamnatin Nijeriya

0

Gwamnatin Nijeriya tare da kungiyar ActionAid Nigeria, sun bayyana aniyarsu ta kawar da talauci a Nijeriya kafin shekarar 2030 ta hanyar aiwatar da tsare-tsare waɗanda za su ƙarfafa wa mutane da ba da dama ga masu aiki tukuru.

Daraktan kungiyar ActionAid Nigeria, Andrew Mamedu, ya ce kawar da talauci zai yiwu ne idan gwamnati da ‘yan ƙasa suka haɗa kai tare da bin hanyoyi masu kyau da fadada Tunani.

Ya nuna damuwa kan yadda kasafin kuɗin Nijeriya ya ƙaru daga Naira biliyan 300 a 1999 zuwa Naira tiriliyan 54.5 a 2024, amma talauci bai ragu yadda ake tsammani ba.

A cewarsa Nijeriya tana asarar kusan dala biliyan 18 a kowace shekara saboda kashe kudi ba bisa ka’ida ba.

Ya yi kira ga gwamnati ta koyi darasi daga ƙasashen China da India waɗanda suka fitar da miliyoyin mutane daga talauci ta hanyar saka jari a fannonin ilimi, lafiya, samar da ababen more rayuwa, da karawa marasa galihu karfi.

Za mu hada kai wajen magance matsalar tsaron da ta addabi Nijeriya – sabbin hafsonshin tsaron Nijeriya

0

Sabbin hafsoshin tsaron Nijeriya sun ce za su yi aiki tare domin magance dukkan barazanar tsaro a faɗin kasar, tare da kare martabar ƙasar a kowane fanni.

Jaridar Daily Trust, ta rawaito cewa Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin sabbin hafsoshin da shugaban Tinubu ya tura dasu don amincewa a ranar Laraba.

Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya Janar Oluyede, ya bayyana cewa akwai buƙatar Nijeriya ta kafa masana’antar samar da makamai a cikin gida domin rage dogaro da na kasashen waje.

A cewarsa siyan kayan yaki daga kasashen waje akwai tsada sossai, don haka ya kamata a fara kerasu a gida Nijeriya.

Kazalika ya nemi a sake fasalin rundunar ‘yan sanda don rage nauyin da ake dora wa sojoji wajen gudanar da ayyukan da bai kamata su yi ba.

Gwamnatin Tinubu ta fitar da Naira biliyan 2.3 don biyan bashin albashi da karin girma na malaman jami’o’i

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta saki kudin da ya kai Naira biliyan 2.3 domin biyan bashin albashi da karin girma na malamai a jami’o’in ƙasar.

A cewar Daraktar Yada Labarai ta Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Hajiya Folasade Boriowo, wacce ta fitar da sanarwar a madadin Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, gwamnatin ta sake jaddada kudirinta na farfaɗo da harkar ilimi a manyan makarantu ta hanyar ƙarin tallafin kuɗi, gyaran manufofi, da ci gaba da tattaunawa da ƙungiyar ASUU da sauran ƙungiyoyin jami’o’i.

DCL Hausa ta ruwaito cewa, Dokta Alausa ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani kan yadda tattaunawa ke gudana da ƙungiyoyin malaman jami’a da na sauran cibiyoyin ilimi.

Ya ce Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dage wajen warware matsalolin da suka daɗe suna damun malaman jami’o’i da inganta walwalarsu ta hanyar gaskiya da tsari mai ɗorewa.

Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta riga ta saki ₦2.311bn, wanda ke zama kashi na 8 na biyan bashin albashi da karin girma na malaman, ta hannun Ofishin Akanta-Janar na Ƙasa (OAGF).

Majalisar wakilan Nijeriya ta amince wa Tinubu ya ciyo bashin dala biliyan 2.35

Majalisar wakilai ta Nijeriya ta amince da bukatar shugaban Tinubu na neman bashin dala biliyan 2.347 daga ƙasashen waje domin cike gibin kasafin kuɗin 2025 da kuma sake biyan wani tsohon bashin a Eurobond.

An amince da bukatar ne bayan rahoton kwamitin Majalisa kan tallafi da harkokin basussuka da shugaban kwamitin, Ɗan majalisa Abubakar Hassan Nalaraba, ya gabatar a zaman majalisar da kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya jagoranta.

Jaridar Punch ta rawaito cewa tun bayan da shugaba Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023, gwamnatinsa ta karɓi basussuka da dama domin tallafa wa shirin gwamnati da ayyukan ci gaba.

A cikin shekaru biyu, Nijeriya ta karɓi sama da dala biliyan 7.2 daga bankin duniya da kuma bashin dala biliyan 1 daga bankin raya Afirka.

Sojojin Nijeriya za su murƙushe ‘yan ta’addan Lakurawa — Babban hafsan sojin kasa Janar Waidi Shaibu

0

Babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Waidi Shaibu, ya sha alwashin murƙushe sabuwar ƙungiyar ‘yan ta’addan Lakurawa wadda ke addabar wasu sassan arewacin Nijeriya.

Janar Shaibu, wanda Shugaba Tinubu ya nada kwanan nan, ya bayyana haka ne yayin da Majalisar Dattawa ke tantance shi a Larabar nan.

A cewar sabon hafsan sojin, yana da gogewa a fagen yaki da ta’addanci tun lokacin da ya jagoranci sojoji a jihar Borno, inda ya ce a lokacin sunci karfin Boko Haram, kuma da dama daga cikinsu sun miƙa wuya.

Ya kara da cewa, sun yi amfani da fasahar zamani wajen inganta ayyukan soji, wanda hakan ya taimaka wajen lalata ƙungiyoyin ta’addanci da dama.

Janar Shaibu ya kuma bayyana cewa nan gaba, rundunar soji za ta mayar da hankali wajen ci gaban ma’aikata da kula da jin daɗinsu.

Tinubu ya cire masu manyan laifuka daga jerin wadanda za su amfana da afuwar shugaban kasa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan takardun afuwa da sassauta hukunci ga wasu mutane da aka taɓa yanke wa hukunci, domin aiwatar da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na yin afuwa.

Kamar yadda sanarwar fadar shugaban ƙasa ta bayyana a ranar Talata, 29 ga Oktoba, 2025, matakin ya biyo bayan tattaunawa da Majalisar Koli ta Ƙasa da kuma ra’ayoyin jama’a game da batun.

Shugaban ƙasa ya kuma bada umarnin sake nazarin jerin sunayen wadanda aka fara tsara yi musu afuwa domin tabbatar da adalci da tsaro.

Sanarwar ta ce an cire sunayen wadanda suka aikata manyan laifuka kamar sace mutane, fataucin miyagun ƙwayoyi, safarar mutane, damfara, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, daga jerin.

Wasu kuma da aka riga aka yi musu afuwa a baya, an rage musu hukunci ne kawai ba a sake su gaba ɗaya ba.

A cewar gwamnatin tarayya, wannan mataki ya zama dole saboda muhimmancin tsaron ƙasa, jin tausayin waɗanda aka yi wa laifi, da kuma girmama ƙoƙarin hukumomin tsaro.

Muna karɓar saƙonnin barazanar kawo mana hari a majalisa – Shugaban kwamitin tsaron majalisar waƙilai

0

Shugaban kwamitin tsaron cikin gida na Majalisar Wakilai, Honarabul Garba Ibrahim Muhammad, ya bayyana cewa majalisar na shan barazanar kai mata hari daga ’yan ta’adda, abin da ya haifar da bukatar karfafa tsaro a cikin ginin majalisar.

Honarabul Muhammad ya bayyana hakan ne a yayin jin ra’ayi kan kudirin kafa hukumar tsaron majalisa da aka gudanar a Abuja, inda ya ce majalisar ta zama abin bibiya ga miyagu da ke amfani da raunanan matakan tsaro.

A cewarsa sun sha barazana daga ’yan ta’adda da ke cewa zasu tarwatsa ginin majalisar, haka kuma wasu masu zanga-zanga sun yi barazanar rufe ta.

Ya ce kudirin yana nufin samar da tsaron da ya dace da abin da ake amfani da shi a majalisun kasashe masu ci gaba, domin kare ’yan majalisa, ma’aikata, da duk masu ziyartar ginin.

Sama da mutum 170 ne ke son zama ’yan Nijeriya daga kasashen ketare – Ministan cikin gida

0

Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji Ojo, ya bayyana cewa sama da ’yan kasashen ketare 170 ne suke neman zama ’yan Nijeriya.

Tunji Ojo ya sanar da hakan ne a shafinsa na X, bayan ya jagoranci taron Citizenship Advisory Committee a Abuja.

A cewarsa, an kafa kwamitin ne domin duba da kuma ba da shawarar neman zama dan Nijeriya ga masu bukata domin amincewa.

Kwamitin ya kunshi manyan jami’an gwamnati daga ma’aikatun Shari’a, harkokin kasashen waje, hukumar tsaro ta DSS, da hukumar shige da fice ta NIS.

Majalisar Dattawan Nijeriya za ta tantance sabbin Hafsoshin tsaro da shugaba Tinubu ya nada

0

Majalisar Dattawan Nijeriya ta shirya fara tantance sabbin hafsoshin tsaro da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada, domin tabbatar da su.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar bayan karanta wasikar shugaba Tinubu da ke neman a tabbatar da sabbin shugabannin rundunonin tsaro.

Cikin jerin wadanda za a tantance akwai Janar Olufemi Oluyede, Manjo Janar Waidi Shaibu, Air Vice Marshal Sunday Aneke da Rear Admiral Idi Abbas.

Rahotanni sun nuna cewa za a gudanar da tantancewar a kebance, kamar yadda majalisar ke yawan yi kan batutuwan tsaro, don guje wa bayyanar bayanan sirri na kasa.

Zuwa yanzu rahotanni na nuni da cewa tuni,manyan jami’an suka halarci zauren majalisar domin tantancewar a Larabar nan.

Ciyo bashi bayan cire tallafin man fetur ba dai-dai bane – Sarki Muhammadu Sanusi II

Tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya soki gwamnati bisa ci gaba da ciyo bashi duk da cire tallafin man fetur.

Sarki Sanusi ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin wani taro da aka gudanar a Abuja, inda ya ce cire tallafin man ya karawa gwamnati kuɗaɗen shiga, don haka bai dace a ci gaba da aro kudi ba.

Ya jinjina wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa cire tallafi da daidaita farashin musayar kuɗi, yana mai cewa matakan suna da tsauri amma sun zama wajibi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Sarkin ya yi gargadin cewa,duk wannan matakan, ba za su yi tasiri ba idan ba’asa gaskiya da tsauraran matakai kan kashe kuɗin gwamnati ba.