Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 16

Jam’iyyar PDP za ta ƙalubalanci zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a Abuja

0

Jam’iyyar PDP ta ce ta shirya lauyoyi na musamman domin shigar da ƙorafe ƙorafe sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Abuja.

Jam’iyyar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bisa zargin an tafka kura-kurai a tsarin zaɓen tare da tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a daga ɓangaren abokan hamayya.

A cewar PDP, rahotannin da suka samu daga wakilansu a rumfunan zaɓe sun nuna yadda aka yi katsalandan a wasu wurare, lamarin da ke iya shafar sahihancin sakamakon ƙuri’un da aka bayyana.

Asusun ba da lamuni na Duniya zai tallafawa Nijar da dalar Amurka miliyan 91

0

Asusun ba da lamuni na Duniya ya cimma yarjejeniya da hukumomin ƙasar Nijar, a wani shiri na bayar da wasu tallafi ga kasar, inda Nijar za ta karɓi kusan dala miliyan 91 wato sama da biliyan 50 na FCFA.

A cewar IMF, ana sa ran tattalin arzikin Nijar zai haɓaka da kashi 6.7% zuwa shekarar 2026, duk da ƙalubalen tsaro da sauyin yanayi da kasar ke fuskanta.

Jam’iyyun adawa ba zasu taɓa yadda da sahihancin zaɓe ba muddin ba sune suka yi nasara ba – Festus Keyamo

0

Ministan sufurin jiragen saman Nijeriya, Festus Keyamo, ya soki jam’iyyun adawa kan martaninsu game da zaɓen ƙananan hukumomin Abuja, yana cewa yawanci sukan amince da sahihancin zaɓe ne kawai idan aka ayyana su a matsayin masu nasara.

Keyamo ya bayyana cewa irin waɗannan kalamai na iya raunana amincewar jama’a da tsarin dimokuraɗiyya, inda ya bukaci ’yan siyasa su riƙa karɓar sakamakon zaɓe cikin girmamawa, ko sun yi nasara ko sun sha kaye.

NNPP ta zargi gwamnatin Kano da farautar masu yi mata adawa

0

Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta zargi gwamnatin jihar da kai wa mambobinta hari abin da jam’iyyar ta ce ba su dace da ka’idojin dimokuradiyya ba.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran NNPP na Kano, Injiniya Ibrahim Karaye, ya fitar, jam’iyyar ta ce gwamnati ta fara janye kujerun aikin Hajji da aka riga aka ware wa wasu daga cikin mambobinta, ciki har da tsofaffin kwamishinoni, masu ba da shawara da wasu shugabannin jam’iyyar.

NNPP ta ce wadannan mutane ’yan Kano ne, kuma suna da ’yancin cin irin wadannan abubuwa da gwamnati ke samarwa.

Haka kuma, jam’iyyar ta zargi gwamnati da tsangwama da tsoratar mambobinta domin mayar da motocin aiki da aka ba su a lokacin da suke kan mukamai, tana mai cewa motocin na daga cikin hakkokinsu da suka yi hidima.

Gwamnatin Kano ta ware naira miliyan 99 domin rigakafin cutar mahaukacin kare

Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe Naira miliyan 99 domin fara shirin rigakafin cutar mahaukacin kare (rabies), inda ake sa ran yi wa akalla karnuka 10,000 allurar rigakafi a mataki na farko.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktar Wayar da Kai ta Ma’aikatar Raya Dabbobi ta jihar, Halima Gadanya, ta fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ce gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ne ya bayar da amincewar a matsayin wani bangare na kokarin gwamnatinsa na kare lafiyar al’umma daga cututtukan da ake iya kauce musu amma masu hadari.

Shirin zai kasance karkashin jagorancin Ma’aikatar Raya Dabbobi ta jihar, inda kwamishinan ma’aikatar, Aliyu Isah Aliyu, zai kula da aiwatar da shi kamar yadda jaridar Punch ta ambato.

Wike ya koka kan ƙarancin masu fitowa zabe a Abuja

0

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana gamsuwarsa kan yadda ake gudanar da zaɓen kananan hukumomi cikin lumana a fadin Abuja, duk da korafin ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a wasu sassan birnin.

Da yake magana bayan zagayen sa ido da ganawa da masu zaɓe, Wike ya ce yanayin tsaro ya kasance cikin kwanciyar hankali, yana mai danganta hakan da kokarin jami’an tsaro.

Ministan ya ƙara da cewa a irin wannan zaɓen da ba na gama-gari ba, ana yawan samun ƙarancin mahalarta, amma abin da ya fi muhimmanci shi ne an gudanar da zaɓen cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.

Dangane da kalaman Sanata Ireti Kingibe wadda ta soki takaita zirga-zirga a matsayin kama-karya, Wike ya ce bai kakaba dokar hana fita ba.

FCT na da sama da masu rajista miliyan 1.5 da ake sa ran za su zabi shugabannin kananan hukumomi shida—Abuja Municipal, Bwari, Gwagwalada, Kuje, Abaji da Kwali—tare da kujeru 68 da ake takara, ciki har da shugabanci shida da kujerun kansiloli 62.

Babu jam’iyyun NNPP, PDP, da ADC a takardun zaɓen cike gurbi na Kano

Rahotanni daga Arise News sun nuna cewa manyan jam’iyyun adawa guda uku, NNPP, PDP, da ADC ba su bayyana a takardun zaɓe na zaben cike gurbin kujeru biyu a majalisar dokokin jihar Kano da ake gudanarwa a ranar Asabar ba.

Zaɓen na cike gurbi ne na kujerun da suka samu rashin cancanta bayan rasuwar tsoffin ‘yan majalisa a bara, wadanda suka kasance membobin NNPP kafin rasuwarsu.

Rahoton ya kara da cewa jam’iyyun siyasa tara ne aka jera a takardun zaɓen, ba tare da PDP, NNPP da ADC ba.

Trump ya ƙara harajin kashi 10% ga kasashen duniya

0

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanya karin harajin kashi 10 cikin 100 kan dukkan kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar, bayan da kotun kolin kasar ta soke wasu daga cikin harajin da ta bayyana a matsayin marar tsari.

Trump ya rattaba hannu kan dokar ne a Fadar White House, yana mai cewa sabon harajin zai fara aiki kusan nan take, kamar yadda kafafen sadarwar kasar suka ruwaito.

A cewar wata takarda daga Fadar White House, sabon harajin zai fara aiki daga ranar 24 ga Fabrairu na tsawon kwanaki 150.

Sai dai an ware wasu bangarori da ake ci gaba da bincike a kansu, ciki har da bangaren magunguna, da kuma kayayyakin da ke shiga Amurka karkashin yarjejeniyar kasuwanci ta Amurka, Mexico da Canada.

Sai dai wani jami’in Fadar White House ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa gwamnatin Trump za ta nemi hanyoyin da za ta aiwatar da harajin da ya dace ko wanda aka riga aka amince da shi nan gaba.

An samu ƙarancin fitowar masu zaɓe a zaɓen cike gurbi a Kano

0

An fara zaɓen cike gurbi na kujeru biyu a majalisar dokokin jihar Kano a safiyar Asabar, inda aka samu ƙarancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a a sa’o’in farko na zaɓen.

Zaɓen na gudana ne a rumfunan zaɓe 1,014 da ke cikin mazabu 24, biyo bayan rasuwar Aminu Sa’ad Ungogo mai wakiltar Ungogo da kuma Sarki Aliyu na mazabar Kano Municipal a watan Disamban 2025.

Kimanin masu rajista 535,000 ake sa ran za su halarci zaɓen. Rahotanni sun nuna cewa kayan zaɓe sun isa rumfunan zaɓe da wuri, amma jami’ai da mazauna yankuna sun nuna damuwa kan ƙarancin mahalarta, duk da fatan cewa yawan masu fitowa zai ƙaru yayin da rana ke tafiya.

Rahotanni daga sassa daban-daban na mazabun sun nuna cewa ana gudanar da zaɓen cikin lumana, ba tare da tangarda ba kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.

Ƴan adaidaita ne suka yi jigilar kayan zaben kananan hukumomin Abuja

0

An tura babura masu kafa uku da aka fi sani da Keke NAPEP domin jigilar muhimman kayayyakin zabe na INEC zuwa rumfunan zabe a zaben kananan hukumomin Babban Birnin Tarayya (FCT).

An ga kekunan na tsaye a wasu cibiyoyin rarraba kaya, inda jami’an zabe ke tabbatar da an kulle akwatunan zabe da takardun sakamako yadda ya kamata kafin a tura su zuwa unguwanni daban-daban a fadin Abuja.

Jaridar The Nation ta ruwaito amfani da Keke NAPEP na zama hanya mai sauki kuma mai rahusa wajen kai kayan zabe zuwa matakin karshe, musamman a wuraren da manyan motoci ke fuskantar cunkoso ko matsalar shiga.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu rahotannin koke-koke masu yawa dangane da rarraba kayan zaben a FCT, duk da cewa masu sa ido na ci gaba da bibiyar yadda ake gudanar da aikin domin kauce wa jinkiri ko wata tangarda.