Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 17

’Yan bindiga sun yi ajalin mutum 30 a Zamfara

0

Akalla mutum 30 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka bace bayan harin ’yan bindiga a kauyen Dutsin Dan Ajiya da ke karamar hukumar Anka a jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce maharan sun kai farmakin ne da tsakar dare na ranar Alhamis zuwa safiyar Juma’a, inda suka rufe hanyoyin shiga kauyen tare da bude wuta kan mai uwa da wabi.

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa bayan harin ne aka gano gawarwakin mutum 30, yayin da wasu suka jikkata, wasu kuma har yanzu ba a san inda suke ba.

Lamarin ya faru ne kasa da awanni 48 bayan gwamnatin jihar Zamfara ta kaddamar da sabbin kayan yaki da jiragen sa ido marasa matuki domin karfafa yaki da matsalar tsaro.

Kodayake Gwamnan ya umurci mataimakinsa, Mani Mumuni, da ya kai ziyara yankin domin jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ’yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

Sanata Kingibe ta zargi Wike da tafiyar da mulkin kama-karya a Abuja

Sanata mai wakiltar Babban Birnin Tarayya (FCT), Ireti Kingibe, ta zargi Ministan FCT, Nyesom Wike, da tafiyar da mulki irin na kama-karya tare da kin hada kai da masu ruwa da tsaki a yankin.

Da take magana a shirin Politics Today na Channels Television, Kingibe ta ce ministan ba ya son yin aiki tare da zababbun wakilai da jami’an gwamnati domin kai ribar dimokuradiyya ga mazauna FCT.

Ta bayyana cewa duk da wasikun da ta aike masa tana nuna shirinta na ba da hadin kai, har yanzu ba ta samu amsa mai gamsarwa ba.

Har ila yau, Kingibe ta soki matakin da ministan ya dauka na kakaba dokar hana fita ta awanni 22 gabanin zaben kananan hukumomin da ake gudanar wa a ranar 21 ga Fabrairu a Abuja.

Ministan ya ayyana ranar Juma’a a matsayin ranar hutu tare da hana zirga-zirga daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe washegari Asabar.

Orano a shirye yake ya tattauna da gwamnatin sojan Nijar

Kamfanin hakar uranium na Faransa, Orano, ya bayyana cewa a shirye yake ya fara tattaunawa da hukumomin mulkin soja na Jamhuriyar Nijar domin lalubo mafita da sasantawa kan batutuwan da ke tsakaninsu.

Kamfanin ya ce yana da niyyar warware sabanin cikin lumana ta hanyar tattaunawa da mahukuntan Nijar, bayan takaddama da ta biyo bayan sauyin mulki da aka samu a kasar.

Orano na daya daga cikin manyan kamfanonin da ke hakar uranium a Nijar, kasar da ke cikin manyan masu samar da ma’adinan uranium a duniya.

Hukumomin Nijar dai sun dauki wasu matakai kan harkokin kamfanin tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi, lamarin da ya haifar da rashin jituwar da ke bukatar sasantawa tsakanin bangarorin biyu.

Gambiya ta nuna damuwa kan ’yan kasarta da ke shiga yake-yake a ketare

Gwamnatin Gambiya ta bayyana matukar damuwa kan rahotannin da ke nuna cewa wasu ’yan kasarta na tafiya kasashen waje domin shiga yake-yake a turai.

A wata sanarwa da ma’aikatar yada labarai ta kasar ta fitar, ta ce an samu bayanan cewa wasu ’yan Gambiya sun rasa rayukansu bayan shiga yakin kasashen ketare. Sai dai sanarwar ba ta ambaci yakin Ukraine kai tsaye ba.

Binciken da kamfanin dillancin labarai na Agence France-Presse (AFP) ya gudanar ya nuna cewa Rasha na daukar maza ’yan Afirka da alkawarin samar musu da ayyukan farar hula masu tsoka, amma daga bisani a tura su fagen daga a Ukraine.

Sauran kasashen Afirka da suka hada da Najeriya, Kenya da Afirka ta Kudu su ma sun nuna damuwa kan yadda ake daukar ’yan kasashensu domin shiga yakin.

Chadi na tattauna yiwuwar dawowar dakarun Faransa kasarta

Rahotanni daga kafafen yada labarai na kasa da kasa sun nuna cewa tattaunawa ta yi nisa tsakanin ƙasar Chadi da Faransa kan yiwuwar sake dawowar dakarun Faransa a kasar, shekara guda bayan ficewarsu a hukumance.

Sai dai har zuwa yanzu babu wata sanarwa a hukumance daga mahukuntan N’Djamena ko na Paris da ke tabbatar da hakan.

Sojojin Faransa sun kammala ficewa daga Chadi a karshen watan Janairun 2025, bayan da gwamnatin kasar ta bukaci hakan a watan Nuwamban 2024, tare da kalubalantar yarjejeniyar tsaro da ta hada kasashen biyu tun shekarar 1966.

Ficewar Faransa daga Chadi ya zo ne a cikin guguwar korar dakarunta daga yankin Sahel, inda lamarin ya fara daga Mali, ya wuce Burkina Faso, sannan ya isa Jamhuriyar Nijar kafin Chadi ta bi sahu.

Majiyoyi sun ce tattaunawar ta kara karfi ne bayan wani babban taron koli kan huldar kasashen waje da aka gudanar a karshen watan Janairun 2026, tsakanin Shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby, da takwaransa na Faransa, Emmanuel Macron.

Shugaba Tinubu ya yi kira da a zauna lafiya gabanin zaɓen Abuja, Kano da Rivers

0

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a, jami’an tsaro da jami’an Hukumar zaɓe Mai zaman kanta (INEC) da su gudanar da ayyukansu cikin tsari da natsuwa yayin zaɓukan da za a yi ranar Asabar a Babban Birnin Tarayya (FCT), Kano da Rivers.

A cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya bukaci duk masu haƙƙin zaɓe su fito su kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ba.

INEC za ta gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi shida na FCT, da kuma zaɓukan cike gurbi a mazabun Ahoada East II da Khana II a Jihar Rivers, da Kano Municipal da Ungogo a Jihar Kano.

Gwamnatin Nijeriya za ta kafa kwalejin koyon likitanci ta sojoji don magance karancin likitoci

0

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirin kafa kwalejin koyon likitanci ta soji “Armed Forces College of Medicine and Health Sciences” a matsayin wani mataki na dakile karancin likitoci da cike giɓin likitoci 340,000 a Nijeriya.

Shirin ya biyo bayan taron ministoci da suka haɗa da ministan ilimi Dr. Maruf Tunji Alausa, karamar minstar ilimi Suwaiba Ahmed, da ministan tsaro, Christopher Musa, tare da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, lafiya da tsaro.

Kwalejin za ta zama wata hanya ta ƙarfafa ayyukan kiwon lafiya na sojoji, horar da likitoci da masu jinya, masu kwarewa wajen kula da masu raunin a wajen yaki, da kuma samar da karin likitoci a fadin ƙasa.

Kotu ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar tsohon Ministan Shari’a Abubakar Malami zuwa 27 ga Fabrairu

0

Kotun tarayya da ke Abuja ta ɗage shari’ar tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, tare da ɗansa Abdulaziz, zuwa 27 ga Fabrairu, 2026.

Alƙaliyar kotun, Joyce Abdulmalik, ta ɗauki wannan mataki ne sakamakon hutun da ministan Abuja, Nyesom Wike ya bayar gabanin zaɓen kananan hukumomin Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa a safiyar ranar shari’ar, ma’aikatan kotu kaɗan ne suka halarta, kuma babu lauyoyi ko ɓangarorin shari’ar da suka bayyana a kotun.

Kotu a Marocco ta yanke wa magoya bayan Senegal da suka ta da tarzoma a gasar AFCON 2025 hukunci

0

Wata kotu a ƙasar Morocco ta yanke wa magoya bayan Senegal 18,hukunci bisa laifin ta da tarzoma a wasan karshe na cin kofin Nahiyar Afrika na 2025.

An same su da laifin tayar da hankali da lalata wasu kayayyaki bayan sun kutsa cikin filin wasa, suka jefa kujeru, tare da arangama da jami’an tsaro sakamakon bugun fanareti da aka bai wa ƙasar mai masaukin baki.

Duk da cewa Senegal ta doke Morocco da ci 1–0, tarzomar ta jawo asarar fiye da dala $476,000, kuma an dakatar da wasan na ɗan lokaci.

Kotun ta yanke wa mutum 11 hukuncin ɗaurin shekara guda, mutane huɗu watanni shida, sai wasu huɗu watanni uku.

Lauyoyin masu laifin sun ce hukuncin ya yi tsauri, kuma sun bayyana aniyar ɗaukaka ƙara.

DSS za su gurfanar da Elrufa’i gaban kuliya a ranar 25 ga Fabrairu

Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya , SSS ta ce za ta gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna State, Nasir El-Rufai, a gaban kotu ranar 25 ga Fabrairu, bisa zargin aikata laifukan intanet.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeri NAN, ya rawaito mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta saka ranar shari’ar bayan babban alkalin kotun tarayya, mai shari’a John Tsoho, ya mika mata shari’ar.

DSS ta shigar da tuhume tuhume uku kan El-Rufai bisa zargin yin kutse a kiran wayar mai ba shugaba Tinubu shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu.

A wata hira da El-rufa’i ya yi a gidan talabijin na Arise a kwanakin baya, ya ce shi da wasu suna sauraron kiran wayar Nuhu Ribadu abinda wasu ke ganin hakan na barazana ga tsaron kasa.