Monday, April 6, 2026
Home Blog Page 15

Sojojin Nijeriya sun dakile wani kwanton-bauna da Lakurawa suka yi musu a jihar Kebbi

0

Ayarin motocin Babban Kwamandan Runduna ta 8, Manjo Janar Bemgha Koughna, ya tsallake rijiya da baya bayan da dakarun sojin Nijeriya suka dakile wani hari na kwanton-bauna da ake zargin ‘yan ta’addar Lakurawa sun shirya a kusa da Tsaunin Mayama, Jihar Kebbi. Lamarin ya faru ne yayin da kwamandan ke hanyarsa ta zuwa duba dakarun da ke aiki a yankin.

Sanarwar da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Runduna ta 8, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya fitar ta ce dakarun sun mayar da martani cikin gaggawa bayan harin, inda suka kashe ‘yan ta’adda biyar tare da tarwatsa sauran. Ya bayyana cewa matakin ya hana maharan cimma manufarsu tare da tabbatar da tsaron ayarin.

Bayan kammala artabun, sojojin sun yi bincike a yankin inda suka kwato makamai da kayayyaki, ciki har da bindigogi, harsasai, babura biyar da kuma kudade. Rundunar ta ce dakarunta na ci gaba da sintiri domin hana sake faruwar hare-hare, tare da jaddada kudurin sojin Nijeriya na kare fararen hula da murkushe barazanar ‘yan ta’adda.

Hukumar tace fina-finai ta Kano ta soke lasisin wani gidan gala bisa dalilai na tsaro

0

Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta soke lasisin gudanar da ayyukan wani gidan gala mai suna Sunsiro Entertainment, wanda ke kan titin Yahaya Gusau, Sharada, Kano.

Daukar matakin ya biyo bayan samun korafe-korafe kan tarbiyya tare da sahihan rahotannin tsaro daga al’ummar yankin da abin ya shafa.

A cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ya bayyana cewa shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya amince da matakin ne bisa ga sakamakon binciken da ke kunshe a cikin rahoton ’yan sanda da kuma shawarwarin da kwamitin sa ido na hukumar ya gabatar.

Dimukuradiyyar Nijeriya na cikin barazana a mulkin Tinubu – Atiku Abubakar

0

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya nuna damuwa kan karancin fitowar masu kada kuri’a a zaben da aka gudanar ranar Asabar a Abuja.

Cikin wani sako da hadiminsa Paul Ibe ya wallafa a shafinsa na X, ya ce hakan na nuni da irin bazaranar da dimukuradiyya a Nijeriya ke fuskanta karkashin gwamnatin shugaba Tinubu.

Ya yi zargin cewa rashin fitowar masu zaɓe, na da alaka da yanayin tsoratarwa da kuma tauye ‘yancin yan adawa da ya ce ana yi a kasar, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

Hukumar NERC ta gargadi masu kai wa wadanda wutar lantarki ta ja dauki

0

Hukumar kula da wutar lantarki ta Nijeriya NERC ta yi gargadi ga masu yunkurin kai wa wadanda wuta ta ja dauki ba tare da bin matakan da suka dace ba.

Cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X, NERC ta kuma gargadi mutane da su kaucewa taba wayoyin lantarki da kuma gujewa kusantar su.

Hukumar ta kuma bukaci a rika barin kwararru suna kai dauki, ko sa hannu a duk wani abu da ke bukatar hakan wanda ya shafi wutar lantarki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Amurka za ta koro karin ‘yan Nijeriya 19 gida kan aikata munanan laifuka

0

Gwamnatin Amurka ta kara sanya sunayen ‘yan Nijeriya 19 cikin kundin masu munanan laifuka, yayin da ta ke shirin kora su gida.

Wasu bayanai daga shafin yanar gizo na ma’aikatar tsaron cikin gidan Amurka sun nuna cewa mutanen da aka kara, sun sa adadin wadanda za a kora gida ya kai 113.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa laifukan da ‘yan Nijeriyar suka aikata sun hadar da safarar miyagun kwayoyi, cin zarafi, damfara da wasu miyagun laifuka.

Ma’aikatar tsaron ta bayyana cewa da zarar ta kammala bin matakan da suka dace, za ta kora mutanen gida.

Wata annoba ta afka wa sansanonin barayin daji a jihohin Zamfara da Neja

Rahotanni sun ce wata annoba ta bulla a wasu sansanonin ’yan bindiga a jihohin Neja da Zamfara, lamarin da ake cewa yana kara tsananta halin da suke ciki tare da shafar ayyukansu.

Majiyoyi sun bayyana wa jaridar Daily Trust cewa barkewar cutar na zuwa ne a daidai lokacin da suke fama da karancin abinci, kudade da magunguna, abin da ake zargin yana haifar da matsin lamba a cikin kungiyoyin tare da rage karfin aikinsu a wasu yankunan da abin ya shafa.

Wani mutum da ya tsere daga hannun masu garkuwa a Jihar Neja, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ya shaida yadda waɗanda ake tsare da su daga cikin ’yan bindigar ke fama da cututtuka daban-daban yayin da yake cikin sansanin.

Barayin daji sun yi kwanton-bauna sun yi ajalin askarawan CPG na jihar Zamfara ana dab da buda-baki

0

Wasu barayin daji da aka kiyasta yawansu ya haura 10 sun yi kwanton-bauna ga askarawan CPG na jihar Zamfara har suka yi ajalin biyu daga cikinsu.

Lamarin ya faru ne a yankin mazabar Magamin Diddi cikin karamar hukumar Maradun ta jihar da yammacin Lahadi ana dab da buda-bakin azumin ranar.

Kansilan mazabar Magamin Diddi/Faru Bello Hussaini ne ya tabbatar da faruwar hakan ga DCL Hausa.

Kansilan ya ce bai kai rabin kilomiya ba daga inda lamarin ya faru zuwa cikin garin Magami, har ma barayin dajin suka yi ta kokarin kutsa kai cikin gari don kara tafka wata aika-aikar.

Ya ce bayanan sirri ne aka bayar cewa barayin dajin sun tare wasu gungun mutane da suka fito daga Maradun zuwa Magami, sai jami’an sa kan bisa babura biyu, suka hanzarta kai agaji, ba tare da sun sani sani ba, ashe kusan babura bakwai na barayin dajin na can boye, sai da suka raba tsakiya aka auna musu darma nan take biyu suka ce ga garinku nan.

Jami’an tsaron Chadi hudu sun kwanta dama a wata fafatawa da wasu mahara a arewacin kasar

0

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar 17, ga watan Febarairun da muke ciki a lokacin da wata motar jigilar wani kamfani ke cikin tafiya kan hanyar da ke tsakanin Faya da Kouba Olanga ta fada tarkon wasu mutane masu dauke makamai inda nan take suka halaka direban motar.

To sai dai rahotanni na nuni da cewa kwana daya bayan hallaka direban ne wasu makusanta shi suka farwa maharan da suka halakashi, nan ne jami’an tsaro suka shiga lamarin, a yayin fafatawar su da maharan manyan jami’an tsaron Chadin hudu suka kwanta dama, sai dai a cewar majiyar tsaro su ma maharan an hallaka uku daga cikin su.

Wata majiya daga gwamnatin kasar ta ce za a kara tsaurara tsaro nan gaba a yankin da ke cikin hamada sahara wanda yake fama da hare hare a kan hanya.

Masu zanga zanga a Sénégal na neman adalci ga dalibin Jami’ar Cheikh Anta Diop ta birnin Dakar da aka halaka

0

Masu zanga zangar da suka hada da magoya bayan jam’iyya mai mulki ta Pastef sun amsa kiran wata hadaka ce ta dalibai da ‘yan fafutikar farar hula domin yin Allah wadai da kalubantar cin zarafin da ‘yan sanda suke yi.

Kutsen da jami’an tsaron ‘yan sandan suka yi ɗakin kwanan daliban Jami’ar Cheikh Anta Diop da kuma wasu fayafayen bidiyo masu tayar da hankali da aka gani su ne suka harzuka ‘yan kasar wadanda da dama suka tsammaci bankwana da irin wadannan dabi’u tun bayan zuwan sabbin hukumomin kasar a shekarar 2024.

To sai dai babban mai shigar da kara na kasar ya ce dalibin Jami’ar Abdoulaye ba ya rasu ne sakamakon fadowa daga saman bene na hudu inda dakin shi yake a Jami’ar a lokacin da yake kokarin guje wa gobarar da ta tashi, amma masu zanga zangar na cewa dalibin ba zai yi yunkurin gudun ba idan jami’an tsaron ba su abkawa dakunan kwanan nasu ba.

A cewar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International mutum 66 ne aka hallaka a cikin rikicin siyasa a kasar daga shekarar 2021 zuwa 2024 wani yanayi marar dadi da kasar ta samu kanta a tarihi.

Shugaba Tinubu ya taya waɗanda suka samu nasara a zaɓukan Abuja, Kano da Rivers, murna

0

Shugaba Tinubu ya taya waɗanda suka samu nasara a zaɓen ƙananan hukumomin Abuja da kuma zaɓen cike gurbi da aka gudanar a jihohin Kano da Rivers.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa sakamakon zaɓukan na nuna ci gaban dimokiraɗiyya da yanayin siyasa a ƙasar, inda ya buƙaci dukkan ɓangarori su mutunta zaɓen da masu kaɗa kuri’a suka yi.

Haka kuma, Tinubu ya yaba da jagorancin ministan Abuja Nyesom Wike, yana mai cewa rawar da ya taka ta taimaka wajen tabbatar da tsari, zaman lafiya da nasarar gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.