Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 23

ADC ta soki yunƙurin kama El-Rufai tare da zargin gwamnati da tsoratar da ‘yan adawa

0

Jam’iyyar ADC ta yi Allah-wadai da abin da ta kira yunƙurin kama tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, a filin jirgin sama ba tare da sammaci ba, tana mai cewa hakan na tayar da tambayoyi kan bin doka da nuna bangaranci.

A sanarwar da Sakataren Yada Labarai na Kasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce bai kamata doka ta zama makamin yaki da ‘yan adawa ba, duk da cewa babu wanda ya fi karfinta.

ADC ta kuma zargi gwamnatin APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu da nuna bambanci a yaki da cin hanci, tana mai cewa ana tsananta bincike kan masu sukar gwamnati yayin da wasu ke samun karɓuwa a jam’iyya mai mulki.

Jam’iyyar ta bukaci hukumomin tsaro su kiyaye kwarewa da kundin tsarin mulki, tare da jaddada cewa ya kamata siyasa ta gudana ta hanyar kuri’a da hujja, ba ta hanyar tsoratarwa ba.

Atiku ya zargi ICPC da son zuciya kan yunkurin kama El-Rufa’i

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya zargi Hukumar ICPC da nuna son zuciya bayan abin da ya kira yunƙurin kama tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, a filin jirgin sama bayan dawowarsa ƙasa.

Atiku ya bayyana a shafinsa na X cewa ya kai wa El-Rufai ziyarar goyon baya, yana mai cewa an yi yunƙurin kama shi ba tare da gabatar da sammaci ba. Ya wallafa hotunan ganawar sirri da suka yi a wani gida mai zaman kansa.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin tsaida El-Rufai a filin jirgin, amma daga bisani aka bar shi ya wuce bayan takaddama da ta ɓarke. Sai dai ICPC da sauran hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun zazzafar muhawara ta siyasa, bayan El-Rufai ya ƙara kusanci da jam’iyyar ADC tare da sukar gwamnatin tarayya a bainar jama’a kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Nijeriya na cikin kasashen da ke yawan daukar yara aikin soja – MDD

0

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana Nijeriya a cikin kasashe biyar da ke da mafi yawan daukar yara cikin kungiyoyi masu amfani da makamai, tana mai gargadin cewa matsalar yara a yankunan rikici na kara tsananta a duniya.

Wakiliyar MDD kan Yara da Rikici, Vanessa Frazier, ta ce a 2024 kadai an tabbatar da yara sama da 7,400 da aka dauka ko aka yi amfani da su a rikice-rikice kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ta ce kasashen da abin ya fi kamari sun hada da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, Nijeriya, Somaliya, Syria da Myanmar, inda ta jaddada cewa kowanne adadi na wakiltar rayuwar yaro da aka lalata.

A Nijeriya musamman Arewa maso Gabas, dubban yara sun shiga halin kunci sakamakon rikicin ‘yan ta’adda, inda sace-sace da tilasta musu shiga kungiyoyin makamai suka zama ruwan dare.

Frazier ta bukaci a maida hankali kan kariya da ilimi tare da hukunta masu daukar yara, tana mai cewa kare yara ba zabin son rai ba ne, illa wajibi domin samar da zaman lafiya mai dorewa.

Tinubu zai je Kano ranar Litinin domin karbar Gwamna Abba cikin jam’iyyar APC

0

Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai isa Kano ranar Litinin domin karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC a wani gagarumin taro da za a yi a filin wasa na Sani Abacha Stadium da ke Kofar Mata.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima da wasu gwamnoni na APC za su halarci taron da ake kallon a matsayin muhimmin gangamin siyasa a Arewa maso Yamma.

Shugaban APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, ya ce taron zai zama alamar karɓar Yusuf a hukumance cikin jam’iyya, yana mai cewa hakan babban ci gaba ne ga APC a Kano, wadda ake dauka a matsayin muhimmiyar cibiyar siyasa a Nijeriya.

Ya ce an kafa kwamitoci da dama domin tabbatar da tsaro da gudanar da taron ba tare da tangarda ba, ciki har da kwamitin tsaro mai mambobi 15 karkashin jagorancin Kanal Umar Malami, da kwamitin wurin taro karkashin Bala Mohd Gwagwarwa.

Sauran kwamitocin sun hada da na yada labarai da hulda da jama’a, na lafiya da tsafta, da kuma na ladabi da karɓar baki, tare da kafa kwamitin wayar da kai domin tabbatar da halartar jama’a da dama a taron.

EFCC ta kama matasa 3 kan zargin fyace majina da N500 a jihar Borno

0

Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin Nijeriya zagon kasa ta kama wasu matasa 3 da take zargi da fyace majina da N500 a Maiduguri jihar Borno.

Cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook, EFCC ta bayyana sunayen matasan da Adam Muhammad, Muhammad Muhammad da kuma Bashir Musa.

Hukumar ta cafke matasan ne bayan da wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna matasan na share majina da takardar kudi ta Naira 500.

Haka kuma hukumar ta ce za ta gurfanar da su a gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

Hukumar ‘Road Safety’ ta kori jami’anta 43 kan saba wa dokokin aiki

0

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta Nijeriya FRSC ta kori jami’anta 43 kan samun su da aikata laifukan da suka shafi saba wa ka’idojin aiki.

Wata sanarwa da jami’in wayar da kai na hukumar Olusegun Ogungbemide ya fitar, ta nuna cewa an kori 31 daga cikin jami’an ne saboda laifin barin wurin aiki ba bisa ka’ida ba, biyar saboda aikata wasu munanan laifuka, sai bakwai saboda laifukan da suka shafi aikin sintiri.

Babban kwamandan FRSC Shehu Muhammad, ya bayyana daukar matakin a matsayin wata hanya ta tsaftace aikin hukumar, yana mai cewa ba za ta lamunci duk wani nau’i na rashin da’a ko saba dokar aiki ba.

INEC ta gabatar da kasafin N873.78bn domin gudanar da zaɓen 2027

0

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta gabatar da buƙatar kasafin kuɗi na Naira biliyan 873.78 domin gudanar da babban zaɓen shekarar 2027.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya gabatar da wannan buƙata ne a gaban kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Wakilai kan Harkokin Zaɓe a Majalisar Ƙasa, a ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa tuni aka fara shirye-shiryen zaɓen 2027 bisa tanadin doka da ke buƙatar a amince da kuɗaɗen zaɓe aƙalla kwanaki 360 kafin ranar da za a gudanar da zaɓen.

Taron kare kasafin kuɗin ya samu jagorancin Sanata Simon Bako Lalong, tare da takwaransa daga Majalisar Wakilai, Hon. Adebayo Balogun.

Gwamnatin Sokoto za ta biya ma’aikata albashin Fabarairun 2026 a ranar 13 ga wata

0

Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya bayar da umarnin a biya ma’aikatan gwamnati albashin watan Fabarairun 2026 a ranar 13 ga wata.

 

Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin ta fitar, tare da cewa an dauki matakin duba da karatowar azumin Ramadan.

 

A cewar ta, hakan zai taimaka wa ma’aikatan wajen samun saukin tafiyar da al’amura yayin gabatar da ibada.

Zan yi murabus idan aikin titin Abuja-Kaduna-Kano bai zama mai inganci ba – Minista Dave Umahi

0

Ministan ayyuka na NIjeriya David Umahi ya yi alkawarin sauka daga mukaminsa muddin aikin titin Abuja-Kaduna-Kano bai fito da inganci ba.

Umahi ya bayyana haka ne a lokacin da yake kare kasafin kudin ma’aikatarsa a gaban majalisar dokokin Nijeriya, kamar yadda Channels TV ya wallafa.

An samu tambayoyi kan dalilan da suka sanya ma’aikatar ayyuka ta bai wa wani kamfani da ba a san shi ba aikin, sai dai Umahi ya kare matakin da cewa kamata yayi a mayar da hankali kan ingancin aiki ba wai shaharar kamfani ba.

Kasshim Shettima ya tafi Ethiopia don wakiltar Shugaba Tinubu a taro

0

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima ya tafi birnin Addis Ababa na Ethiopia domin wakiltar shugaba Tinubu a taron kungiyar tarayyar Afirka na 2026.

Baya ga taron kungiyar, Kashim Shettima zai halarci wasu tarukan da kuma ganawa da jagororin Afirka a bangarori daban daban, da nufin karfafa alakar Nijeriya da wasu kasashen a Afirka.

Ya samu rakiyar wasu ministoci da kuma manyan jami’an gwamnati, kuma ana sa ran zai koma gida Nijeriya bayan kammala duka tarukan, kamar yadda fadar shugaban kasa ta sanar.