Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 24

Shehu Sani ya yi watsi da zargin Amurka kan su Kwankwaso

0

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa akwai bukatar ‘yan majalisar Amurka su sake yin bincike kan zargin da suke yi wa Kwankwaso da wasu kungiyoyi na tauye ‘yancin addini.

Shehu Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na X, yana mai cewa a lokuta da dama, kungiyoyin Miyetti Allah da Miyetti Allah Kautal Hore ba sa tsira daga fuskantar farmakin ‘yan ta’adda.

Kazalika ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa Kwankwaso ya musgunawa wani bangare na addini, yana mai cewa zamanin mulkinsa a Kano ya isa shaida.

Alkali ya janye daga shari’ar EFCC da Abubakar Malami

0

Mai shari’a Obiora Egwuatu ya janye kansa daga shari’ar da hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arziki zagon kasa ta Nijeriya ta shigar da tsohon ministan shari’ar Nijeriya Abubakar Malami SAN.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ruwaito Alkalin na cewa ya janye daga shari’ar ne saboda dalilai na kashin kai da kuma barin gaskiya ta yi halinta.

Jerin shari’a guda biyu ce dai EFCC ta shigar da Abubakar Malami a gaban kotu kan mabambantan zarge-zarge.

NNPP da APC sun yi watsi da zargin Amurka kan Kwankwaso na tauye ‘yancin addini

Jam’iyyun NNPP da APC sun yi watsi da zargin da wasu ‘yan majalisar Amurka suka yi kan tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, kungiyar makiyaya da Miyetti Allah da kuma Miyetti Allah Kautal Hore, na cewa suna tauye ‘yancin addini a Nijeriya.

‘Yan majalisar dai sun gabatar da wani kuduri da ke bukatar a kwace kadarorin wadanda suka zarga, tare da hana su bizar shiga Amurka.

Sai dai APC ta ce zargi kawai bai isa hujjar hana Kwankwaso morar ‘yancinsa na yawo ba, kana babu cikakken bincike tare da bin tsarin da ya dace kan lamarin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ita kuwa jam’iyyar NNPP, yayin wani taron manema labarai a Abuja, bayyana lamarin ta yi a matsayin bi-ta-da-kulli kawai.

Tinubu ya nada Amb Isma’il Abba Yusuf a shugabancin hukumar NAHCON

0

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya nada Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaba hukumar kula da aikin hajji ta kasa, NAHCON.

 

Nada shi na bukatar amincewar Majalisar Dattawa kamar yadda dokar NAHCON ta 2006 ta tanada.

 

A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Mr Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Bola Tinubu ya aika wasika ga shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, yana neman majalisar ta tabbatar da nadin cikin gaggawa.

 

Ambasada Ismail Abba Yusuf zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman wanda ya yi murabus a wannan mako bayan shafe kusan watanni 14 a mukamin.

 

Sanarwar ta bayyana cewa Ambasada Ismail Abba Yusuf gogaggen jami’in diflomasiyya ne, wanda ya taba zama jakadan Nijeriya a kasar Türkiye daga 2021 zuwa 2024. Ana sa ran nadin nasa zai taimaka wajen ci gaba da tafiyar da harkokin aikin Hajji da ayyukan NAHCON.

Nijeriya ta sadaukar wajen samar da daidaito a Liberia – Lt. Gen. Waidi Shaibu

0

Babban hafsan sojin kasa na Nijeriya Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce gagarumar sadaukarwar da Nijeriya ta yi ne ya samar da daidaito da zaman lafiya a  Liberia, lokacin da kasar ke fama da yakin basasa.

Waidi Shaibu ya bayyana haka ne a Liberia yayin bikin tunawa da ‘yan mazan jiya na kasar, kamar yadda sashen hulda da jama’a na rundunar sojin Nijeriya ya bayyana cikin wata sanarwa.

A cewar sa, Nijeriya ce ta dauki kaso mafi tsoka na nauyin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar, a zamanin yakin.

Ya kuma jaddada kudurin gwamnatin Nijeriya wajen ci gaba da karfafa alaka da kasar musamman ta fuskar tsaro.

Amurka na shirin hana Kwankwaso da karin wasu mutane bizar shiga kasar

0

‘Yan majalisar dokokin Amurka biyar sun mika wani kuduri da ke bukatar kakaba takunkuman da suka hada da hana biza da kuma kwace kadarorin jagoran jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso, kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah da Kautal Hore.

Kudurin ya biyo bayan shirin gwamnatin Amurka na daidaita zargin da ta kira da matsi kan ‘yancin addinin Kiristoci a Nijeriya, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

‘Yan majalisar sun yaba da matakin shugaban Amurka Donald Trump na sanya Nijeriya cikin kasashen da ke bukatar kulawa ta musamman.

A cewar su, akwai bukatar gwamnatin Trump ta yi amfani da dukkanin damar da take da ita wajen kawo karshen musgunawar da suka ce ana yi wa Kiristoci da sauran mabiya addinai daban-daban.

Jihohin Nijeriya sun kashe N455bn don biyan basukan ketare a shekarar 2025 – NBS

0

Bayanai daga hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS sun nuna cewa jihohin Nijeriya sun kashe N455.38bn wajen biyan basukan ketare a shekarar 2025.

Hakan na nuni da kari da sama da kaso 25 a kudaden da suka kashe a shekarar 2024, inda suka biya N362.08bn, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Masana fannin tattalin arziki dai sun nuna damuwa da cewa hakan na yin barazana ga damar gwamnatocin na gabatar da wasu manyan ayyuka, biyan albashin ma’aikata da kuma gabatar da harkokin yau da kullum.

Amurka za ta tura karin dakarun sojinta zuwa Nijeriya

0

Bayanai daga shafin jaridar New York Times sun nuna cewa gwamnatin Amurka na shirin aikewa da karin dakarun sojinta zuwa Nijeriya.

 

Hakan dai kari ne ga jami’an da Amurkan ta fara tura wa zuwa kasar a makon da ya gabata, kamar yadda babban kwamandan sojin Amurka da ke Afirka Janar Dagvin R Anderson ya tabbatar.

 

Bayanan da suka fito sun nuna cewa dukkanin dakarun za su taimaka ne wajen bai wa sojojin Nijeriya horo, ba tare da sa hannu a ko wane irin aikin sanar da tsaro ba.

Mafi yawan ‘yan majalisar dokokin Nijeriya za su fadi zabe in da gaskiya a ciki – Sowore

0

Dan gwagwarmaya a Nijeriya Omoyole Sowore ya ce kaso 90 na ‘yan majalisar dokokin kasar ba za su koma kujerunsu ba in har za a gudanar da zabuka cikin gaskiya.

 

Sowore ya bayyana haka ne a matsayin marokan cece-kucen da ya barke game da batun gyaran dokar zabe, musamman sashen da ke magana kan aikewa da sakamako ta hanyar amfani da yanar gizo.

 

Da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels cikin shirin safiya, Sowore ya zargi ‘yan majalisun da kin bullo da dokokin da za su tabbatar da sahihancin zabuka a kasar, domin suna tsoron rasa kujerunsu.

 

A cewar sa, hujjar da aka gabatar ta cewa rashin yanayin sadarwa mai kyau zai tilasta yin amfani da takardu, tana nuna gazawa wajen kokarin tabbatar da adalci.

Tottenham ta kori mai horas da ‘yan wasanta Thomas Frank

0

Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham da ke Ingila ta sanar da korar mai horas da ‘yan wasanta Thomas Frank.

 

Daukar matakin ya biyo bayan rashin nasarar da kungiyar ta samu a hannun Newcastle United a gida, lamarin da ya bar ta a matsayin ta 16 kan teburin Firimiyar Ingila.

 

Haka kuma, maki biyar ne kacal ya rage tsakanin kungiyar da fadawa ajin ‘yan dagaji wato ‘relegation zone’ kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.