Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 29

Magoya bayan Senegal 18, da aka tsare a Morocco sun fara yajin cin abinci gabanin shari’arsu

0

Magoya bayan kasar Senegal guda 18, da aka tsare a Morocco bisa zargin tayar da tarzoma yayin wasan karshe na AFCON da aka yi a watan da ya gabata, sun fara yajin cin abinci gabanin shari’arsu, a cewar lauyansu.

Lauya Patrick Kabou ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Juma’a cewa mutanen sun shafe lokaci tun 18 ga Janairu ba tare da an bayyana musu tuhume-tuhumen da ake yi musu ba, ranar da aka kama su bayan rikicin da ya biyo bayan wasan karshe da Senegal ta doke Morocco.

Kabo ya ce wadanda ake tsare da su sun koka da cewa ‘yan sanda sun yi musu tambayoyi da harshen Faransanci da Larabci, alhali harshen da suka iya shi ne Wolof, wanda shi ne yaren gargajiyarsu.

INEC ba ta da hurumin zaɓar shugabancin PDP – Turaki

0

Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar PDP da ke karkashin jagorancin Tanimu Turaki, ya bayyana cewa Hukumar zaben Nijeriya INEC, ba ta da hurumin zaɓar shugabanci ko tsoma baki a harkokin cikin gida na jam’iyyar.

Sakataren yada labarai na kasa na PDP, Ini Ememobong, ne ya bayyana hakan yayin martani kan taron da INEC ta yi da jam’iyyun siyasa, wanda kwamitin rikon kwarya da Abdulrahman Mohammed ke jagoranta ya halarta a madadin PDP.

Ememobong ya ce duk da cewa INEC ta gayyaci shugabannin jam’iyyu, gayyatar wasu tsofaffin ‘ya’yan PDP da ke ikirarin jagorantar wani kwamitin rikon kwarya ya sabawa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, domin babu irin wannan tanadi a cikinsa.

Shugaban kasar Congo mai shekaru 82 zai sake tsayawa takara

0

Shugaban Jamhuriyar Congo, Denis Sassou Nguesso, ya bayyana cewa zai sake tsayawa takara a zaben shugaban ƙasa da za ayi 15 ga Maris.

A yanzu dai yana da shekaru 82, kuma ya jagoranci ƙasar mai arzikin man fetur na tsawon shekaru 42, wanda ya zama ɗaya daga cikin shugabannin Afirka da suka dade a kan mulki bayan Paul Biya na Cameroon da Teodoro Obiang Nguema Mbasogo na Equatorial Guinea.

Sassou Nguesso ya yi wannan sanarwar ne gaban dimbin al’umma a karamar hukumar Ignie, inda ya yi alkawarin inganta tsaron abinci da tallafawa matasa.

Kotu a Nijeriya ta umurci Birtaniya ta biya fam miliyan 20 ga iyalan ma’aikata 21 da aka halaka a 1949

0

Wata kotu a Nijeriya ta umurci Gwamnatin Birtaniya da ta biya fam miliyan 20 ga kowane iyali daga cikin iyalan ma’aikatan ma’adanai na kwal 21 da hukumomin mulkin mallaka suka kashe a shekarar 1949 a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

Hukuncin ya fito ne daga Mai Shari’a Anthony Onovo na babbar kotun jihar Enugu, wanda kuma ya umurci Birtaniya da ta nemi afuwar hukuma kan kisan gillar da aka yi wa ma’aikatan.

DW Afrika ta rawaito cewa an harbe ma’aikatan ne a wajen ma’adanai na kwal a Iva Valley a ranar 18 ga Nuwamba, 1949, yayin da suke zanga-zangar lumana kan mummunan yanayin aiki, bambancin albashi, wariyar launin fata, da kuma albashin da ba a biya su ba.

Messi ya yanke shawarar komawa Barcelona

0

Fitaccen ɗan wasan ƙwallon kafa, Lionel Messi, ya yanke shawarar cewa zai koma tsohon kulob dinsa Barcelona a nan gaba, kamar yadda rahotannin jaridar Marca suka bayyana.

Rahoton ya ce duk da ba a bayyana rawar da Messi zai taka ba idan ya koma Barcelona, ko dai a matsayin ɗan wasa, jami’i, ko wani matsayi na daban a cikin kulob din.

Masu sharhi kan harkokin ƙwallon ƙafa na ganin wannan mataki na iya zama wani babban sauyi ga Barcelona, duba da irin rawar da Messi ya taka a tarihin kulob din, inda ya zama fitaccen ɗan wasa mafi nasara a tarihi.

’Yan ta’adda sun san abin da zai biyo baya duk lokacin da suka kai hari kan Kiristoci – Trump

0

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ’yan ta’adda sun san abin da zai same su duk lokacin da suka kai hari kan Kiristoci, yana mai cewa ba za a lamunci irin wadannan hare-hare ba.

Trump ya fadi hakan ne yayin wani jawabi da ya yi, inda ya bayyana matakan da gwamnatinsa ta dauka na kai hari kan kungiyoyin ta’addanci, musamman ISIS, ciki har a Nijeriya da sauran sassan Afirka.

Ya ce a karkashin gwamnatinsa, Amurka ta dauki tsauraran matakai na soja da na tsaro domin raunana ISIS da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda, tare da aikewa da sako karara cewa duk wanda ya kai hari kan fararen hula, musamman wanda ke da alaka da addini, zai fuskanci sakamako mai tsanani.

Alƙali ya yi barazanar soke belin Abdulrasheed Maina da ake zargin kan zambar N738.6m

Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Abuja, ta yi barazanar soke belin tsohon shugaban kwamitin garambawul a harkar fansho na ƙasa, Abdulrasheed Maina, bisa zargin yin dabaru daban-daban domin jinkirta shari’arsa.

Alƙali Abubakar Kutigi ya nuna ɓacin rai ne yayin zaman kotu da aka gudanar Alhamis, 5 ga Fabrairu, 2026, bayan lauyan Maina ya gabatar da takardar tura shi asibiti tare da neman dage shari’a, duk da cewa takardar ba ta nuna wata babbar rashin lafiya ba, kamar yadda shafin hukumar EFCC ya ruwaito.

Alƙalin ya ce shari’ar ta yi shekaru huɗu ana jan ƙafa, sakamakon abin da ya kira dabarun Maina na jinkirta shari’a, inda ya bayyana cewa Maina bai halarci kotu ba tun shekaru huɗu da suka gabata.

Majalisar dattawa ta musanta ƙin amincewa da aika sakamakon zaɓe ta na’ura

0

Bangaren ’yan adawa a Majalisar Dattawan Nijeriya ya fayyace a ranar Alhamis cewa Majalisar ba ta ƙi amfani da tsarin tura sakamakon zaɓe ta na’ura ba a ci gaba da aikin gyaran dokar zaɓe, sabanin rahotannin da aka yaɗa a kafafen yaɗa labarai.

 

Wannan bayani ya zo ne sa’o’i ƙasa da 24 bayan Majalisar Dattawa ta fuskanci suka a ranar Laraba, biyo bayan rahotannin da ke cewa ’yan majalisar sun yi watsi da shawarar tura sakamakon zaɓe ta na’ura, tare da ƙin saka dokar hana masu sayen ƙuri’a da sauran masu aikata laifukan zaɓe shiga harkar zaɓe na tsawon shekaru 10.

 

Bayan yaɗuwar rahotannin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ƙaryata labarin tare da jaddada cewa Majalisar ta bar tsarin tura sakamakon zaɓe ta na’ura yadda yake a ƙarƙashin dokar zaɓe ta 2022.

 

Da yake zantawa da ’yan jarida a ranar Alhamis, jagoran bangaren marasa rinjaye a Majalisar Dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe, ya ce sun ga dacewar yin wannan bayani ne sakamakon abin da ya kira “rashin fahimta” da ya biyo bayan zaman Majalisar na ranar Laraba.

Kotu ta yankewa tsohon shugaban bankin NEXIM hukuncin daurin shekaru 490

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, a yau Alhamis 5 ga Fabrairu, 2026, ta samu nasara a kotu, inda aka yanke wa Robert Orya, tsohon Darakta Janar na Bankin Shigo da Fitar da Kaya na Nijeriya (NEXIM) daga shekarar 2011 zuwa 2016, hukuncin daurin kurkuku kan laifin zamba ta kusan Naira biliyan 2.4.

EFCC, wadda lauya Samuel Ugwuegbulam ya wakilta wajen shari’ar, ta gurfanar da Orya a gaban Mai shari’a F.E. Messiri na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.

Kotun ta same shi da laifi a kan tuhume-tuhume guda 49, tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a kowane tuhuma, wanda jimillarsu ta kai shekaru 490 a gidan yari.

Shugaba Tinubu ya girke sojoji a Kwara bayan harin da aka kai jihar

0

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin girke dakarun soji a Kwara bayan harin da ya hallaka mutane da dama a jihar.

 

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya fitar, ya ce an girke dakarun ne domin zakulo wadanda suka kai harin, tare da hana afkuwar irin sa a nan gaba.

 

Kazalika ya nuna damuwa tare da yin Ala wadai da abin da ya kira ‘mummunan hari’ kan al’umma, baya ga bayyana maharan a matsayin marasa imani.

 

Harin da aka kai garin Woro a jihar ta Kwara, ya zo ne bayan wani sumame da sojoji suka kai a yankin cikin makon da ya gabata.

 

Tuni dai Gwamnan jihar Abdulrahman Abdulrazaq ya sha alwashin daukar matakin da zai kawo karshen ayyukan ta’addanci musamman a kan iyakokin Kwara da Neja.