Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 28

Nijar da Nijeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro da farfado da kasuwanci a iyakar kasashen

Daraktan Janar na Hukumar Kwastam na Nijar, Colonel Mohamed Siddo Yacouba, ya kai ziyarar aiki a Abuja inda ya tattauna da takwaransa na Hukumar Kwastam ta Nijeriya.

Bayan wani zama tsakanin wakilan ƙasashen biyu, an rattaba hannu kan yarjejeniyoyi don ƙarfafa tsaro a iyakar kasashen don sauƙaƙe da farfado da harkokin kasuwanci a manyan hanyoyin shiga da fita tsakanin kasashen.

Wannan mataki na nuna fara sasantawa tsakanin mahukuntan Abuja da Niamey bayan watanni na rikicin diflomasiyya tsakanin kasashen makwabta.

An kama ɗan jaridar Mali bisa zargin cin mutuncin shugaban Nijar, Janar Tiani

Hukumomin ƙasar Mali sun kama tare da tsare ɗan jarida Youssouf Sissoko, bisa zargin cin mutuncin shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tiani.

Sissoko, wanda shi ne Daraktan Jaridar Alternance a Mali, an kama shi ne a ranar Alhamis, 5 ga Fabrairu 2026, bayan jaridar tasa ta wallafa wani labari da a ciki ta caccaki Janar Tiani, tare da zarginsa da ɗora alhakin harin da ƙungiyar IS ta kai a Yamai kan Faransa, Bénin da Côte d’Ivoire.

A cikin labarin, jaridar ta kuma zargi Janar Tiani da ƙarya, tare da cewa yana ƙoƙarin mayar da ƙasar Nijar wani dakin gwaje-gwaje na siyasar guba.

Sai dai ƙungiyar ’yan jarida masu zaman kansu ta riga ta bayyana damuwarta kan kamun Sissoko, inda ta bukaci a bayar da belinsa kafin ranar 9 ga Maris 2026, ranar da ake sa ran a gurfanar da shi gaban kotu.

Kashim Shettima ya kai ziyarar ta’aziyya Ilorin kan harin Kaiama

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya isa birnin Ilorin na Jihar Kwara domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bisa harin da aka kai wa al’ummar Woro da ke Karamar Hukumar Kaiama a ranar Talata.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, jirgin Mataimakin Shugaban ya sauka a Filin Jirgin Sama na Janar Tunde Idiagbon da misalin karfe 10:30 na safiyar Asabar, inda ya zo domin nuna alhini da duba halin tsaro.

Mataimakin Shugaban ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, Sanata Ali Ndume, da Sanata Ovie Omo-Agege zuwa jihar.

A filin jirgin saman, Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, tare da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Yakubu Salihu, da Sanatan Kwara Ta Arewa, Sadiq Umar, ne suka tarbe shi.

Gwamnatin Nijeriya ta ƙara kuɗin ‘uniform’ ga ma’aikatan jinya zuwa ₦80,000

Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin kuɗin sayen tufafin aiki ga ma’aikatan jinya da ke ƙarƙashin aikinta, daga ₦20,000 zuwa ₦80,000 a duk shekara.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Hukumar Albashi, Alawus da Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa (NSIWC) ce ta amince da wannan ƙarin, inda wata sanarwa ta tabbatar da hakan, abin da ke nufin ƙarin kashi 300 daga tsohon adadi.

Wannan mataki ya zo ne bayan ƙorafe-ƙorafen da Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Nijeriya NANNM ta yi a watan Yuli 2025, inda ta bayyana cewa ₦20,000 na shekara bai wadatar ba ga ma’aikatan jinya.

Shugaban kungiyar, Morakinyo-Olajide Rilwan, ya shaida wa manema labarai cewa an fitar da sanarwar ƙarin alawus ɗin ba tare da tuntubar ƙungiyar ba.

Jami’an tsaro sun lalata abin fashewa da ’yan ta’adda suka dasa a Zamfara

Jami’an tsaro sun yi nasarar lalata wani abin fashewa da ake zargin ’yan ta’adda ne suka dasa a hanyar Danjibga–Kuncin Kalgo a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

An gudanar da aikin ne ta haɗin gwiwar sashen ’yan sanda masu lalata bama-bamai (EOD–CBRN), sashen yaƙi da garkuwa da mutane, da kuma sojoji, tare da tsauraran matakan tsaro daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Yazid Abubakar, ya ce an gudanar da aikin ne a ranar Juma’a, ƙarƙashin jagorancin SP Abdulrazak Musa Hassan.

Noman watanni biyar ya lalace cikin sa’o’i 48 — Koken manoman  Tumatur a Borno

Manoman tumatir a jihar Borno sun koka bayan noman da suka shafe kusan watanni biyar suna yi ya lalace cikin sa’o’i 48, sakamakon matsalolin ajiya bayan girbi da faduwar farashi.

Rahotanni sun nuna cewa wasu manoma na rasa kashi 50 cikin 100 ko fiye na amfanin gonarsu, musamman waɗanda suka karɓi rance domin noman rani.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, manyan matsalolin sun haɗa da rashin rumbunan ajiya, rashin ingantattun hanyoyin sufuri, saurin lalacewar tumatir cikin makonni 2 zuwa 3 kacal, da kuma kwari irin su Tuta.

Manoman sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta shiga lamarin ta hanyar kafa masana’antun sarrafa tumatir, domin rage asarar bayan girbi da ceton manoma daga halin ƙuncin da suke ciki.

Ma’aikatan lafiya sun dakatar da yajin aiki bayan kwanaki 84

Ƙungiyar ma’aikatan lafiya ta JOHESU ta gargaɗi gwamnati da kada a gallaza ko hukunta mambobinta, bayan ta dakatar da yajin aikin ƙasa baki ɗaya na kwanaki 84.

JOHESU ta sanar da dakatar da yajin aikin ne a ƙarshen taron gaggawa na kwamitin zartarwa na Ƙasa (NEC) da ta gudanar a Abuja.

An kira taron ne domin nazarin sakamakon zaman sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da JOHESU, wanda aka gudanar a hedikwatar ma’aikatar ƙwadago da ayyukan yi ta tarayya a ranar Alhamis.

A cikin sanarwar haɗin gwiwa da ta fitar bayan taron, ƙungiyar ta ce an dakatar da yajin aikin ne domin ba da damar aiwatar da sharuɗɗan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin tarayya da JOHESU.

Shugabanni Nijeriya huɗu sun kashe Naira tiriliyan 7 don inganta lantarki amma har yanzu ƙasar na cikin duhu – Binciken jaridar Daily Trust

An kiyasta cewa gwamnatin tarayya ta kashe sama da naira tiriliyan 7 a fannin wutar lantarki tun daga 2013, lokacin da aka hannunta bangaren ga kamfanoni masu zaman kansu domin inganta samar da lantarki a Nijeriya.

Sai dai duk da wannan makudan kudade, ƙasar ba ta kai ga samun lantarki mai ɗorewa da tabbas ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A cikin watan farko na 2026 kaɗai, manyan biranen ƙasar sun fuskanci katsewar wuta sau biyu, sakamakon faduwar layin wutar lantarki na ƙasa (national grid), abin da ya sake jefa jama’a cikin duhu.

APC ta maye gurbin Uzodimma da Masari a shugabancin kwamitin taron ƙasa

0

Jam’iyyar APC ta sauya Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, daga shugabancin kwamitin shirya babban taronta na kasa, inda ta naɗa tsohon Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari, a matsayin sabon shugaban kwamitin.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Jam’iyyar APC na kasa, Surajudeen Basiru, ya fitar a ranar Jumma’a, gabanin taron ƙasa da APC za ta gudanar a ranakun 27 da 28 ga Maris, 2026.

Jaridar Punch ta rawaito cewa bayan shawarwari da jagorancin jam’iyya da manyan masu ruwa da tsaki, an sake fasalta kwamitin, inda aka sauya Hope Uzodimma ke takawa zuwa ma’aji treasurer.

Haka kuma jam’iyyar ta ƙara yawan mambobin kwamitin daga 73 zuwa 90, tare da shigar da sababbin jiga-jigan jam’iyyar.

Magoya bayan Senegal 18, da aka tsare a Morocco sun fara yajin cin abinci gabanin shari’arsu

0

Magoya bayan kasar Senegal guda 18, da aka tsare a Morocco bisa zargin tayar da tarzoma yayin wasan karshe na AFCON da aka yi a watan da ya gabata, sun fara yajin cin abinci gabanin shari’arsu, a cewar lauyansu.

Lauya Patrick Kabou ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Juma’a cewa mutanen sun shafe lokaci tun 18 ga Janairu ba tare da an bayyana musu tuhume-tuhumen da ake yi musu ba, ranar da aka kama su bayan rikicin da ya biyo bayan wasan karshe da Senegal ta doke Morocco.

Kabo ya ce wadanda ake tsare da su sun koka da cewa ‘yan sanda sun yi musu tambayoyi da harshen Faransanci da Larabci, alhali harshen da suka iya shi ne Wolof, wanda shi ne yaren gargajiyarsu.