Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 30

Kotu ta yankewa tsohon shugaban bankin NEXIM hukuncin daurin shekaru 490

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC, a yau Alhamis 5 ga Fabrairu, 2026, ta samu nasara a kotu, inda aka yanke wa Robert Orya, tsohon Darakta Janar na Bankin Shigo da Fitar da Kaya na Nijeriya (NEXIM) daga shekarar 2011 zuwa 2016, hukuncin daurin kurkuku kan laifin zamba ta kusan Naira biliyan 2.4.

EFCC, wadda lauya Samuel Ugwuegbulam ya wakilta wajen shari’ar, ta gurfanar da Orya a gaban Mai shari’a F.E. Messiri na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.

Kotun ta same shi da laifi a kan tuhume-tuhume guda 49, tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a kowane tuhuma, wanda jimillarsu ta kai shekaru 490 a gidan yari.

Shugaba Tinubu ya girke sojoji a Kwara bayan harin da aka kai jihar

0

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin girke dakarun soji a Kwara bayan harin da ya hallaka mutane da dama a jihar.

 

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga ya fitar, ya ce an girke dakarun ne domin zakulo wadanda suka kai harin, tare da hana afkuwar irin sa a nan gaba.

 

Kazalika ya nuna damuwa tare da yin Ala wadai da abin da ya kira ‘mummunan hari’ kan al’umma, baya ga bayyana maharan a matsayin marasa imani.

 

Harin da aka kai garin Woro a jihar ta Kwara, ya zo ne bayan wani sumame da sojoji suka kai a yankin cikin makon da ya gabata.

 

Tuni dai Gwamnan jihar Abdulrahman Abdulrazaq ya sha alwashin daukar matakin da zai kawo karshen ayyukan ta’addanci musamman a kan iyakokin Kwara da Neja.

‘Yansandan Nijeriya sama da 5000 za su yi ritaya cikin 2026

0

Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta bayyana cewa cewa jami’ai sama da 5,000 ne za su yi ritaya a cikin shekarar 2026.

 

Mataimakin kwamishinan ‘yansanda Sani Doki Yusuf ne ya bayyana haka yayin wani taro da aka shirya wa jami’an da za su yi ritaya cikin 2026 a jihar Kano.

 

A cewar sa, akwai bukatar dukkanin jami’ai su gaggauta dora bayanan su a shafin yanar gizo na rundunar, domin kaucewa fuskantar kalubale wajen karbar kudaden fansho.

Kiristocin da aka yi garkuwa dasu a jihar Kaduna sun shaki iskar ‘yanci

0

Kiristocin da aka sace suna tsaka da ibada a garin Kurmin Wali da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna sun shaki iskar ‘yanci.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa guda daga cikin jagororin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an saki Kiristocin ne a ranar Alhamis.

A ranar 18 ga watan Janairun 2026 ne aka yi awon gaba da kusan mutane 177 yayin da suke tsaka da ibada a coci, sai dai rahotanni sun bayyana cewa 80 daga cikin su sun tsere daga baya.

Har zuwa wannan lokaci dai babu tabbaci kan ko an biya kudin fansa kafin a sake su, da kuma adadin wadanda suka dawo gida, kana kuma babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar ko hukumomin tsaro.

Gwamnatin Nijeriya ta dora laifin talaucin ‘yan kasar kan gwamnoni da kananan hukumomi

0

Fadar shugaban Nijeriya ta bayyana cewa gwamnatocin jihohi da kuma kananan hukumomi ne silar fadawar ‘Yan Nijeriya miliyan 133 cikin kangin talaucin da suke fama da shi a yanzu.

Wata sanarwa da hadimin shugaba Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar a shafinsa na X ce ta bayyana hakan, inda ya ce kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa jihohi da kananan hukumomi ikon samar da duk wasu bukatu na cire al’umma daga talauci.

Kazalika ya ce babu wani sashe a kundin tsarin mulki da ya dora wa gwamnatin tarayya nauyin fitar da al’ummar Nijeriya daga talauci, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ya kuma soki yadda ya ce gwamnatocin jihohi na watsi da muhimman ayyuka tun daga tushe irin su kiwon lafiya da kuma ilimi, tare da cewa hakan na ruruta wutar kangin talauci.

Hatsari ya yi ajalin mutum 5,289 a Nijeriya cikin 2025 – Hukumar FRSC

0

Hukumar kiyaye hadurra ta Nijeriya, FRSC, ta bayyana cewa an samu hatsarin mota 10,446 a fadin kasar a shekarar 2025, inda mutane 5,289 suka rasa rayukansu sakamakon hadurran.

Kwamandan Janar na hukumar FRSC, Shehu Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gudana a Abuja ranar Laraba, 4 ga Fabrairu, 2026, inda ya ce alkaluman sun nuna cewa an samu raguwar mace-mace idan aka kwatanta da shekarar 2024.

Shehu Mohammed ya ce duk da cewa adadin mutuwar ya ragu daga 5,421 a 2024 zuwa 5,289 a 2025 an samu ragin kashi 2.4 cikin 100.

Majalisa Dattawa ta nemi Tinubu ya kafa sansanin soji a Katsina bisa dawowar hare haren ‘yan bindiga a jihar

0

Majalisar Dattawan Nijeriya ta nuna matuƙar damuwa kan tabarbarewar tsaro a jihar Katsina, musamman a yankin Funtua, bayan hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadin mutuwar mutane akalla 35 cikin sa’o’i 24 a ƙananan hukumomi uku.

Majalisar ta yi wannan kira ne a zaman ta na ranar Laraba, 4 ga Fabrairu, 2026, inda ta bukaci Shugaba Tinubu da ya gaggauta cika alkawarin kafa sabon sansanin soja a yankin, tare da gargadin kada a yi wata tattaunawa da ’yan bindigar da ke addabar al’umma.

Majalisar Dattawa ta fara nazarin kudirin gyaran dokar zabe

0

Majalisar Dattawan Nijeriya ta fara duba rahoton kudirin gyaran dokar zabe ta 2022 da ke gabanta.

A zaman wanda Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ke jagorantar zaman, ya zuwa yanzu, Majalisar ta amince da sashe na 1 zuwa na 22 na kudirin dokar.

Jinkirin gyaran Dokar Zabe na iya shafar jadawalin zaben 2027 — INEC

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta ce jinkirin yin gyara ga Dokar Zabe na iya shafar jadawalin gudanar da zaben 2027.

Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da Kungiyoyin Fararen Hula (CSOs) a ranar Laraba a Abuja.

Ya ce duk da jinkirin amincewa da kudirin gyaran Dokar Zaben da ke gaban Majalisar Tarayya a halin yanzu, hukumar INEC na ci gaba da shirye-shirye domin gudanar da babban zaben 2027.

Ba sai kundin tsarin mulki ya ban dama ba, zan iya bai wa duk wani mai mulki shawara – Sarki Sunusi II

Sarkin Kano, Alhaji na 15 Muhammadu Sanusi II, ya ce ba sai kundin tsarin mulki ya ba shi dama kafin ya ba Shugaban kasa ko Gwamna shawara kan muhimman al’amuran da suka shafi ƙasa ba, yana mai jaddada muhimmancin sarakuna wajen gina ƙasa da kyakkyawan shugabanci.

Sarkin ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels Television a ranar Laraba, 4 ga Fabrairu, 2026.

Ya ce ikon ba da shawara yana fitowa ne daga matsayin da yake da shi a matsayin jagoran al’umma, ba wai dole sai doka ta bashi damar ba.

Sarkin ya nanata buƙatar shigar mata a siyasa da harkokin mulki, yana cewa hakan zai ƙara inganta shugabanci da haɗin kai.