Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 34

Ba mu damu da batun tsige gwamnan Rivers ba saboda lamarin yana gaban kotu – Gwamna Abdullahi Sule

0

Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce gwamnonin jam’iyyar APC ba su cikin fargaba kan yunkurin tsige Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, inda ya jaddada cewa batun yana gaban kotu kuma doka ce ke tafiyar da shi.

Gwamna Sule ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin hirarsa a shirin Politics Today na tashar Channels Television, inda ya ce ba za a iya tsige gwamna kawai ba tare da bin tanadin doka da ka’ida ba, yana mai cewa gwamnonin APC na sa ido kan lamarin amma ba su ga dalilin firgici ba.

A halin yanzu dai, yunkurin tsige Gwamna Fubara ya tsaya cik bayan Babbar Kotun Jihar Rivers da ke Oyigbo ta dage sauraron shari’ar har sai Kotun Daukaka Kara ta yanke hukunci, yayin da Alkalin Alkalan jihar, Mai shari’a Simeon Amadi, ya ƙi kafa kwamitin bincike bisa umarnin kotu.

Nade-naden daraktoci a hukumar tattara haraji ya Nijeriya ya saba wa dokar kafa hukumar – Daily Trust

0

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa nadin daraktoci biyar daga cikin shida na Hukumar Tara Haraji ta Nijeriya (NRS) ya saɓa wa tanadin Sashe na 17 (1) na Dokar Kafa NRS ta 2025 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya wa hannu.

Dokar ta tanadi cewa Shugaban Ƙasa zai naɗa daraktoci shida, kowanne daga yanki ɗaya na ƙasar nan bisa tsarin juyawa da jerin jihohi a haruffa, tare da sharadin cewa shugaban hukumar da darakta ba za su fito daga jiha ɗaya ba. Sai dai bincike ya nuna cewa sai daraktar Kudu maso Kudu kaɗai, Iniabasi Akpan daga Akwa Ibom, ita kadai Ce ta dace da tanadin dokar.

A cewar rahoton, ya kamata nadin ya kasance daga Benue (Arewa ta Tsakiya), Jigawa (Arewa maso Yamma), Adamawa (Arewa maso Gabas), Abia (Kudu maso Gabas) da Ekiti (Kudu maso Yamma), amma an naɗa daraktoci daga wasu jihohi daban.

Ƙoƙarin jin ta bakin fadar shugaban ƙasa bai yi nasara ba, yayin da daraktan yada labarai na jam’iyyar APC ya ce ɓangaren zartaswa ne kaɗai ke da alhakin fadin wani abu gane da al’amarin.

Majalisar dattawan Nijeriya ta kafa kwamitin mutane 7 kan gyaran dokar zabe gabanin zaben 2027

Majalisar Dattawan Nijeriya ta kafa kwamitin wucin-gadi na mutum bakwai domin tattara da daidaita ra’ayoyin sanatoci kan kudirin gyaran Dokar Zaɓe, a yayin da ‘yan majalisa ke ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa tsarin zaɓe gabanin babban zaɓen 2027.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya sanar da hakan bayan zaman sirri na tsawon awanni uku da aka yi a ranar Alhamis, inda ya ce kwamitin zai tattara ra’ayoyi tare da magance batutuwan da har yanzu ke buƙatar gyara a kudirin dokar.

Ya bayyana cewa Sanata Niyi Adegbonmire ne zai jagoranci kwamitin, tare da sanatoci irin su Adamu Aliero, Aminu Tambuwal, Adams Oshiomhole, Danjuma Goje, Tony Nwoye da Titus Zam.

Akpabio ya ce an bai wa kwamitin wa’adin kwanaki uku kacal domin kammala aikinsa tare da gabatar da rahoto ga majalisar nan da ranar Talata mai zuwa, yana mai jaddada cewa dole ne Majalisar Dattawa ta yi taka-tsantsan duk da cewa Majalisar Wakilai ta riga ta amince da kudirin.

A cewar kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin zaɓe, gyare-gyaren da ake shirin yi za su ƙarfafa sahihancin zaɓe, su ƙara gaskiya da kuma gina amincewar jama’a. Daga cikin muhimman sauye-sauyen akwai tsaurara hukunci kan sayen ƙuri’a, tura sakamakon zaɓe ta na’ura, tantance masu zaɓe ta hanyar lantarki, da kuma tabbatar da sahihancin zaɓe tun daga 2027.

Rancen kudi daga kasuwannin cikin gida da Gwamnatin Nijeriya ta yi ya zarce na masu zaman kansu da Tiriliyan 9 a 2025 – Rahoton Punch

0

Bayanan Babban Bankin Nijeriya (CBN) sun nuna cewa a shekarar 2025, gwamnatin tarayya ta ƙara karɓar rance daga kasuwannin kuɗi sosai duk da karuwar riba, inda rancen gwamnati ya zarce na kamfanoni da N9.19 tiriliyan. Wannan ya nuna ƙarin matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati da dogaro da rancen cikin gida.

A gefe guda, rancen da aka bai wa ɓangaren masu zaman kansu ya ragu da N1.54 tiriliyan a shekarar, alamar cewa ’yan kasuwa na fuskantar wahala sakamakon tsauraran manufofin kuɗi da karuwar riba. Hakan ya nuna rashin daidaito, inda gwamnati ke shan kaso mafi tsoka na kuɗaɗen bankuna, yayin da kamfanoni ke ja da baya.

Masana sun ce wannan yanayi na iya hana bunƙasar tattalin arziki, domin yawaitar rancen gwamnati na rage damar da bankuna ke da ita wajen bai wa masana’antu da ’yan kasuwa rance, lamarin da ke rage saka hannun jari da samar da ayyukan yi kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Nijeriya ce kasa ta 3 mafi karfin soja a Afrika a 2026 – Global Firepower Index

0

Rahoton Global Firepower Index na 2026 ya nuna cewa Masar ce ke kan gaba a jerin ƙasashen Afirka masu ƙarfin soji, inda ta zo ta 19 a duniya, sakamakon ingantaccen horo, sabbin kayan aiki da ƙarfafa rundunar ruwa da sama.

Rahoton, wanda aka samu a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an tantance ƙasashe sama da 140 ne bisa ƙarfin soji, adadin ma’aikata, kayan aiki da dabarun tsaro, tare da duba yadda ƙasashe ke shirin kare tsaro da zaman lafiyarsu.

Bayan Masar, Aljeriya ta zo ta biyu a Afirka da matsayi na 27 a duniya, yayin da Nijeriya ta zo ta uku a nahiyar da matsayi na 33, sakamakon sabunta kayan tsaro da kuma dogaro da ƙarfin ma’aikata wajen tinkarar ta’addanci da matsalolin cikin gida.

Rahoton ya kuma nuna Afirka ta Kudu a matsayi na huɗu (40 a duniya), sai Ethiopia (47), Angola (59), Morocco (56), Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo (64), Sudan (66) da Tunisia (76), inda aka ce yawancin ƙasashen na ƙara zuba jari a fasaha, horo da dabarun zamani domin tabbatar da tsaro da daidaito a nahiyar Afirka.

Tsare-tsaren Tinubu na farfaɗo da martabar Nijeriya a duniya -Kashim Shatima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na sake gina martabar Nijeriya a idon duniya tare da dawo da amincewa ga ƙasar.

Shettima ya bayyana hakan ne a taron yaye wadanda aka horas kan sana’o’i da aka gudanar a State House Conference Hall, Abuja.

Mataimakin shugaban ƙasar, wanda Sanata Ibrahim Hadejia ya wakilta, ya ce halartar ƙwararru daga ƙasashen waje a shirye-shiryen mika takardun kammala samun horon na nuna ƙara amincewa da Nijeriya a duniya.

Ya ce yaye ƙwararru 2,100 karon farko a fannin sayen kayayyaki (procurement) daga Nijeriya da wasu ƙasashe alama ce ta jajircewar gwamnatin Tinubu wajen aiwatar da Renewed Hope Agenda.

Gwamnatin Nijeriya na shirin dakatar da shigo da kayan tsaro daga waje

Gwamnatin Nijeriya ta yi niyyar kera dukkan makami da ake buƙata a cikin gida nan da shekara biyu zuwa biyar masu zuwa.

Minista a ma’aikatar Tsaron kasar Bello Matawalle a yayin ƙaddamar da motar sulke ta soja DICON X-Shield da kuma wasu motocin sulke da aka kera a Nijeriya, ya ce gwamnatin Tinubu ta fara shimfiɗa tubalin dakatar da shigo abinda jami’an tsaro ke buƙata daga ƙasashen waje.

Jaridar Punch ta ruwaito Matawalle wanda Darakta Janar na DICON, Manjo Janar Babatunde Alaya ya wakilta, ya ce abin da ake gani a yanzu shi ne mataki na farko na babbar dabara da za ta kai ga cikakken shirin kera makamai a gida.

Ya ce nan da shekaru kaɗan Nijeriya za ta daina dogaro da ƙasashen waje domin samar da kayan tsaro, lamarin da zai samar da ayyukan yi, ya rage fitar da kuɗaɗen ƙasa waje, tare da bai wa Nijeriya damar fitar da makamai zuwa wasu ƙasashe.

Fayemi ya musanta rahoton da ke cewa ya yi ganawar sirri da Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi wata ganawa da tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Abuja.

A wata sanarwa da shugaban ofishin yaɗa labaransa, Ahmad Sajoh, ya fitar a ranar Alhamis, Fayemi ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya, yana mai buƙatar jama’a su yi watsi da shi.

Rahoton ya bazu ne a kafafen sada zumunta, musamman X (Twitter), tare da wani tsohon bidiyo da ke nuna Fayemi yana gaisawa da Kwankwaso.

Sai dai a sanarwar da jaridar Punch ta ambato ya ce ya haɗu da Kwankwaso sau ɗaya ne kacal cikin shekara guda, kuma hakan ya faru ne a taron ƙaddamar da littafi na tsohon Babban Lauyan Ƙasa, Mohammed Bello Adoke, SAN.

Sanarwar ta ƙara da cewa Fayemi bai taɓa yin wata ganawar siyasa ta sirri da Kwankwaso ba, kuma ba ya shirin yin hakan.

Gwamnatin Tinubu ta ba ’yan Nijeriya sama da miliyan 34 tallafin kudi – Minista

Gwamnatin Tarayya ta ce ta riga ta bai wa ’yan Nijeriya sama da miliyan 34 masu rauni tallafin kuɗi a ƙarƙashin shirin conditional cash transfer, domin rage matsin tattalin arziki da talauci.

Ministan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Dr Bernard Mohammed Doro, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Calabar, Jihar Cross River, yayin taron farko na National Council on Humanitarian Affairs and Poverty Reduction.

Doro ya ce shirin na nuna ƙudurin gwamnatin Tarayya na fitar da miliyoyin ’yan Nijeriya daga talauci ta hanyoyin tallafi masu tsari, haɗin kai da dogaro da bayanai.

Ya ƙara da cewa gwamnati na da burin kai miliyan 50 kafin ƙarshen shekarar nan, inda ya jaddada cewa kariyar jin-ƙai na daga cikin ginshiƙan manufofin rage talauci na gwamnatin Tinubu.

Gwamnonin jihohi ba su da ikon yafewa ’yan ta’adda a dokar Nijeriya – lauya

Wani lauya kuma ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin bil’adama, Deji Adeyanju, ya ce gwamnonin jihohi ba su da ikon doka na bayar da afuwa ko amnesty ga ’yan ta’adda, yana mai jaddada cewa hakan ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya.

Adeyanju, wanda ke shugabantar kamfanin Deji Adeyanju and Partners a Abuja, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa, yana sukar yadda wasu gwamnonin jihohi ke amfani da tattaunawa da amnesty a matsayin dabarun rage matsalar tsaro.

Ya ce a ƙarƙashin Sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulki, ikon gwamna na yafewa laifi ya ta’allaka ne kawai kan laifukan da dokokin jiha suka ƙirƙira, yayin da ta’addanci laifi ne na tarayya da ke ƙarƙashin Dokar Hana Ta’addanci, wadda ke cikin jerin ikon tarayya kaɗai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Adeyanju ya ce Shugaban Ƙasa ne kaɗai, bisa Sashe na 175, ke da ikon doka na bayar da amnesty kan laifukan ta’addanci, yana mai cewa duk wata afuwa da gwamna ya bayar a irin wannan hali ba ta da inganci a doka.

Adeyanju ya ƙara da cewa shirin amnesty na yankin Niger Delta da gwamnatin tarayya ta aiwatar shi ne misalin da ya dace da kundin tsarin mulki, ba shirye-shiryen jihohi ba.