Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya buƙaci Mataimakin Gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo da ya yi murabus idan ba zai iya ci gaba da tafiya da gwamna Abba Kabir Yusuf a sabon tsarin siyasa ba.
Waiya ya bayyana hakan ne yayin shirin kai tsaye a Muhasa Radio, inda ya ce sabanin siyasa a matakin koli na gwamnati na iya lalata amincewa da tafiyar da mulki, musamman ganin cewa mataimakin gwamnan na rike da muƙamin Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi.
Ya ce kamar yadda wasu kwamishinoni suka yi murabus saboda rashin jin daɗi, hakan ya dace mataimakin gwamnan ma ya ɗauki mataki cikin mutunci idan ba ya kan tafarkin siyasar gwamnan.
Waiya ya jaddada cewa shugabanci na bukatar haɗin kai da amincewa, yana mai gargadin cewa shakku na iya tasowa idan babban jami’in yana gwamnati amma yana bin wata hanyar siyasa ta dabam.
