Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 36

An ja da-ga tsakanin Wike da ma’aikatan Abuja kan umarnin kotu na dakatar da yajin aiki

0

Ma’aikatan Abuja sun jaddada cewa za su ci gaba da yajin aiki, duk da umarnin kotu da kuma barazanar takunkumi daga Ministan Abuja Nyesom Wike.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa yajin aikin, wanda kungiyoyin ma’aikata na hadin gwiwa ke jagoranta, ya fara ne a ranar Litinin bisa gazawa wajen magance korafe-korafe, da kuma tauye hakkin ma’aikata.

Daga cikin bukatu 14, ma’aikatan na neman biyan alawus na watanni biyar,sakamakon yajin aikin ya dakatar da ayyuka a Sakatariyar Abuja da wasu hukumomi da dama, ciki har da makarantun firamare da sakandare a kananan hukumomi shida.

An kai wa ‘yar Majalisar wakilan Amurka musulma Ilhan Omar hari da allura

0

An kai hari ga ‘yar Majalisar Wakilan Amurka, Ilhan Omar, inda wani mutum ya nemi caka mata allura yayin taron jin tattaunawa da jama’a da ta gudanar a birnin Minneapolis, jihar Minnesota.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Ilhan Omar, wadda ke wakiltar jihar Minnesota a Majalisar Wakilan Amurka, ke tattaunawa da jama’a.

Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an kama wanda ake zargi nan take a wajen taron.

An kai wa ‘yar Majalisar wakilan Amurka musulma Ilhan Omar hari

An kai hari ga ‘yar Majalisar Wakilan Amurka, Ilhan Omar, inda wani mutum ya nemi caka mata allura yayin taron jin tattaunawa da jama’a da ta gudanar a birnin Minneapolis, jihar Minnesota.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Ilhan Omar, wadda ke wakiltar jihar Minnesota a Majalisar Wakilan Amurka, ke tattaunawa da jama’a.

Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an kama wanda ake zargi nan take a wajen taron.

Barnar da jam’iyyar APC ta yi wa Nijeriya ta zarta ta mulkin soja – Atiku Abubakar

0

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin APC mai mulki da lalata tsari da yanayin kasar, yana mai bayyana ta a matsayin jam’iyya mai mulki mafi muni da ya taba gani.

Atiku ya bayyana hakan ne a Abuja yayin kaddamar da littafin sakataren jam’iyyar hadaka ta ADC Bolaji Abdullahi mai taken ‘The Loyalist’, inda ya ce ko a zamanin mulkin soji ba a samu barna irin ta APC ba.

A cewar sa, ya ji dadin haduwar ‘yan siyasa da dama wuri guda a cikin jam’iyyarsu ta ADC, a yunkurin sabunta fatan Nijeriya kan turbar dimukradiyya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Al’umma ne ke taka rawa wajen nasara a zabe ba gwamnoni ba – Aregbesola ga APC

0

Sakataren jam’iyyar ADC a Nijeriya ya gargadi APC mai mulki cewa al’umma ne ke taka rawa wajen nasara a zabe ba gwamnoni ba.

Ra’uf Aregbesola ya bayyana haka ne a Abuja, inda ya ce zabukan 2023 na yankin Kudu maso yamma da Kudu maso Gabashin Nijeriya sun tabbatar da hakan.

Aregbesola wanda tsohon gwamnan jihar Osun ne, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ADC a shekarar da ta gabata.

Ya kuma ja hankalin gwamnatin APC da ta tabbatar da ganin an gudanar da sahihin zabe a shekarar 2027, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Mahaifin dan wasan Nijeriya Wilfred Ndidi ya mutu a hatsarin mota

0

Kyaftin din tawagar kwallon kafar Super Eagles ta Nijeriya Wilfred Ndidi ya rasa mahaifinsa Sunday Ndidi a wani hatsarin mota da ya auku a yau Talata.

 

Rahotanni sun bayyana cewa mahaifin Ndidi wanda tsohon soja ne, ya gamu da hatsarin ne a jihar Delta, inda bayan garzayawa da shi asibiti, likitoci suka tabbatar da rasuwar sa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

Tuni kungiyar kwallon kafa ta Besiktas da Wilfred Ndidi ke taka wa leda a kasar Turkiyya ta aike masa da sakon jaje a shafinta na X.

Ma’aikata za su yi zanga-zanga kan haramta amfani da barasar leda a Nijeriya

0

Ma’aikata kamfanonin da ke yin giya za su yi zanga-zanga muddin ba a janye umarnin haramta amfani da barasar leda a Nijeriya ba.

 

Ma’aikatan sun bayyana haka ne yayin da suka yi fitar dango zuwa ofishin hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC da ke Legas.

 

A cewar su, matakin na shafar ayyukansu na yau da kullum musamman ta bangaren samun kudaden shiga, tare da cewa zai shafi akalla ‘yan Nijeriya miliyan 5.

 

Tuni dai shugabar hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ta tattauna da wadanda suka jagoranci zanga-zangar, amma ta ce ba za a dage haramcin ba har sai an samu sauye-sauye daga bangaren majalisar dokokin Nijeriya.

China ta yi alkawarin tallafa wa Cuba bayan barazanar Amurka

0

Gwamnatin China ta sha alwashin tallafa wa kasar Cuba bayan da Amurka ta yi mata barazana.

Gwamnatin Trump dai ta umarci Cuba da ta dauki matakin kulla yarjejeniya da ita, ko kuma ta fuskanci irin halin da Venezuela ta tsinci kanta a ciki.

A kwanakin baya sojojin Amurka sun kutsa cikin birnin Caracas tare da yin awon gaba da shugaban Venezuela Nicolas Maduro.

Sai dai mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China Guo Jiakun ya yi tir da lamarin, tare da bayyana cikakken goyon baya ga Cuba, kamar yadda ta saba yi a baya.

‘National Grid’ ya sake faduwa karo na biyu a 2026

0

Rumbun wutar lantarki na Nijeriya ya sake faduwa a karo na biyu cikin wannan shekarar ta 2026 a ranar Talata.

 

Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, bayanai sun nuna cewa a lokacin haɗa rahoton, babu ko megawatt ɗaya da ake samarwa ga kamfanonin rarraba wuta 11 na ƙasar.

 

Wannan na zuwa ne bayan da grid ɗin ya fuskanci faduwa karo na farko a bana a ranar Juma’a da ta gabata, wanda kuma ya zo makonni kaɗan bayan irin wannan matsala a ranar 29 ga Disamba, 2025.

 

Har zuwa lokacin da aka kammala rahoton, Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Nijeriya (TCN) ba ta fitar da cikakken bayani kan abin da ya jawo wannan matsala ba.

Kotu ta umurci ma’aikatan Abuja su dakatar da yajin aikin da suke yi

0

Mai shari’a Emmanuel Subilim na kotun ma’aikata ta Nijeriya ya bai wa daukacin ma’aikatan Abuja da ke yajin aiki umarnin su dakatar har zuwa lokacin da za a sake zaman sauraron shari’ar.

 

Wannan umarni ya biyo bayan karar da ministan Abuja Nyesom Wike ya shigar gaban kotun, yana neman ta tilasta wa ma’aikatan komawa bakin aiki.

 

A cewar mai shari’ar, wajibi ne a dakatar da duk wani sabani aka mika shi gaban kotu, har sai ta kammala aikinta, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya wallafa.

 

Kazalika ya ce duk wanda aka samu da kin bin umarni ko sabawa doka tabbas zai fuskanci hukunci.