Tuesday, April 7, 2026
Home Blog Page 37

Abba Kabir ka yi namijin ƙokari – Ministan jiragen sama

0

Ministan sufurin jiragen sama na Nijeriya Festus Keyamo ya jinjina wa Gwamna Abba Kabir kan komawa jam’iyyar APC.

 

A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 ne aka gudanar da bikin karbar gwamnan cikin jam’iyyar ta APC a dakin taro na Coronation da ke fadar gwamnatin Kano.

 

Manyan jiga jigai a jam’iyyar APC ne suka tarbe shi, wadanda suka hadar da tsohon shugabanta na Nijeriya Abdullahi Umar Ganduje, mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau I Jibrin, karamin ministan gidaje Yusuf Ata da dai sauran su.

 

Wata sanarwa da Keyamo ya wallafa a shafinsa na X, ya yabawa matakin da Gwamnan ya dauka, na bayyana sanya al’ummar jihar Kano a gaba da komai.

APC ta karyata rade-radin sauya Shettima a takarar Tinubu 2027

0

Jam’iyyar APC ta musanta rahotannin da ke cewa ana shirin sauya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a matsayin abokin takarar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a zaɓen 2027.

 

Sakataren Yaɗa Labarai na APC na Ƙasa, Felix Morka, ne ya yi wannan bayani a shirin Politics Today na Channels a ranar Litinin, inda ya ce rade-radin ba su da tushe.

 

“Yin hasashe kan sunayen mutanen da za su maye gurbin Mataimakin Shugaban Ƙasa kuskure ne. Bisa Dokar Zaɓe da dokokin ƙasa, an hana duk wasu harkokin kamfe yanzu. Bai kamata mu riƙa tattauna wannan batu sosai ba, yadda kafafen watsa labarai da jama’a ke yi.” In ji shi.

Mutanen kauyen da suka sayar da buhunan masara don hada N40m suka biya kudin fansa, aka karbi kudin aka kuma ki sako mutanen a jihar Kaduna

Dattawan al’ummar Gidan Waya da ke ƙaramar hukumar Lere a jihar Kaduna sun bayyana cewa sun sayar da buhunan masara sama da 3,000 domin tara Naira miliyan 40 da masu garkuwa da mutane suka nema a matsayin kudin fansa, amma duk da biyan kudin, mutane 13 da aka sace har yanzu na ci gaba da zama a hannun masu garkuwa bayan shafe makonni.

Da yake magana a wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Litinin, Shugaban Kwamitin Dattawa, Malam Rabo Sambo, ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai hari al’ummar Gidan Waya ne da tsakar dare a ranar 11 ga Nuwamba, 2025, inda suka kashe mutane hudu, sannan suka yi garkuwa da mutane 13 da suka hada da maza biyar da mata takwas.

Sojoji sun amince an kitsa yunkurin juyin mulki kan Tinubu

Rundunar sojin Najeriya ta amince cewa wasu jami’anta sun kitsa yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne rahotanni suka bayyana cewa an kama tare da tsare wasu jami’an soja, daga mukamin Kyaftin har zuwa Birgediya Janar, bisa zargin shirya juyin mulki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Hukumar Leken Asiri (DIA) ce ta gudanar da kamen.

A wancan lokaci, Hedikwatar Tsaro da kuma Fadar Shugaban Ƙasa sun musanta cewa akwai yunkurin juyin mulki, duk da rahotannin da suka danganta lamarin da soke bikin faretin Ranar ‘Yancin Kai ta 1 ga Oktoba da Shugaba Tinubu ya yi.

Sai dai a wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labaran Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya fitar, ya tabbatar da cewa kwamitin binciken da aka kafa ya kammala aikinsa tare da miƙa rahoton ga “hukumomin da suka dace”.

Uba ya ce duk jami’an da ake tuhuma, za a gurfanar da su a gaban kotun soja da ta dace, domin fuskantar shari’a bisa tanadin Dokar Rundunar Sojoji da sauran ƙa’idojin aiki da suka dace.

Hukumar ‘yansandan Nijeriya ta tsawaita wa’adin daukar jami’ai aiki

0

Hukumar Kula da ayyukan ‘yansandan Nijeriya (PSC) tare da rundunar ‘yansandan sun tsawaita wa’adin ɗaukar sabbin ‘constable’ guda 50,000 da makonni biyu, bayan da aka samu ƙarancin masu nema daga wasu jihohi ciki har da Legas.

 

A ranar 26 ga Nuwamban 2025, Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro a faɗin ƙasar, inda ya umarci rundunar ‘yansanda da sojojin ƙasa su ɗauki ƙarin jami’ai domin tunkarar ta’azzarar matsalar tsaro.

 

An buɗe shafin yin rijistar neman aikin a ranar 15 ga Disambar 2025, kuma an tsara rufewa a ranar 25 ga Janairun 2026.

 

Sai dai a cewar wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na PSC, Mista Torty Kalu ya fitar a ranar Litinin yanzu an tsawaita wa’adin zuwa ranar 8 ga Fabrairun 2026.

Shugaba Tinubu ya bar Abuja domin tafiya kasar Turkiyya

0

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bar filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe domin Kai ziyarar aiki kasar Turkiyya da kuma karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.

 

Sanarwar da fadar gwamnati ta fitar, ta ce manufar ziyarar ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa a muhimman bangarori da suka hada da tsaro, ilimi, ci-gaban al’umma, kirkire-kirkire, harkokin sufurin jiragen sama, sadarwa, kasuwanci, da kuma zuba jari.

 

Kazalika wannan ziyara ta biyo bayan ziyarar da Shugaba Recep Tayyip Erdoğan na Turkiyya ya kai Nijeriya a tsakanin 19 da 20 ga Oktoban 2021, wadda ta ƙara dankon alaƙa tsakanin Abuja da Ankara.

Maciji ya yi ajalin Malami a wata lalatacciyar makaranta da ke Abuja

1

Jagoran al’ummar kauyen Jamigbe a mazabar Gawu da ke yankin Abaji a Abuja, Mai Martaba Alhaji Danladi Aliyu, ya tabbatar da rasa ran wani malami mai suna Usman Mohammed sakamakon saran maciji.

 

Lamarin da ya faru a makarantar firamare ta yankin, ya jefa fargaba a cikin zukatan iyaye, dalibai da malamai baki daya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

 

Da ya ke jawabi, Alhaji Danladi ya ce mamacin ya gamu da ajalinsa ne, bayan da macijin ya shiga ofishinsa ta cikin wani rami ya kuma buya a karkashin kujera.

 

Bayan saran malamin, rahotanni sun nuna cewa macijin ya yi masa tsartuwa a idanunsa, inda jim kadan da mika shi asibiti likitoci suka tabbatar da rasuwar sa.

 

Alhaji Danladi ya dora alhakin faruwar lamarin da lalacewar makarantar da yayi sanadiyar bai wa halittu kamar maciji damar shiga ciki.

Za a haifi sabbin jarirai 700,000 a jihar Kano cikin 2026

0

Gwamnatin Jihar Kano ta ce tana sa ran samun haihuwar sabbin jarirai tsakanin 600,000 zuwa 700,000 a shekarar 2026.

Wannan kiyasin ya samo asali ne daga hasashen ƙaruwar yawan jama’a na shekara-shekara da aka yi tun a 2006, wanda ke nuna cewa jihar na da ƙimar ƙaruwa da kashi 3.5 cikin ɗari.

Sakataren hukumar kula da asibitoci na Kano Dr Mansur Mudi Nagoda be ya bayyana hakan a karshen mako, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai ya yi gargaɗin cewa jihar na fuskantar babban ƙalubale a bangaren lafiya, bayan da yawan mutane ke ƙaruwa fiye da adadin ma’aikatan lafiya da ake da su, inda hakan ke ƙara matsin lamba ga ƙarancin ma’aikata da cibiyoyin lafiya da ake fama da su.

Ya bayyana cewa a halin yanzu jihar na da gibin kwararrun ma’aikatan lafiya akalla 4,000.

Wasu tsoffin ‘yan majalisa da masu ci sun bukaci tsarin karba-karba a mulkin Nijeriya

0

Wasu ‘yan majalisar tarayyar Nijeriya masu ci da kuma tsoffi da suka hada da mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau I. Jibrin, tsohon kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, da tsohon shugaban majalisar dattawa Anyim Pius Anyim, sun bukaci a saka tsarin karba-karbar mulki tsakanin yankin Arewa da Kudu cikin kundin tsarin mulki domin tabbatar da adalci da daidaito a rabon mulki.

Wannan kira ya zo ne yayin da majalisar tarayya ke shirin kada kuri’a kan kudirin gyaran kundin tsarin mulki bayan dawowar ta daga hutun da ta dauka.

Sun bayyana matsayinsu ne a ranar Asabar yayin taron koli na tsofaffin ‘yan majalisa na shekarar 2026 da aka gudanar a birnin Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A jawabinsa, Gbajabiamila ya goyi bayan tsarin karba-karbar, yana mai cewa wannan tsari ne cike da hikima da adalci da aka tsara domin tafiyar da bambancin Najeriya, rage tashin hankali a siyasa, da kuma kare zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasa.

Tsadar bukukuwa da shirye-shirye na hana matasa yin aure – Gwamnatin Sokoto

0

Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bayyana cewa tsadar shirye-shirye na hana matasa da dama yin aure, lamarin da ya sa gwamnati ke shirin tabbatar da bin dokar da ke hana yin almubazzaranci wajen shirye-shiryen sa.

 

Gwamna Ahmed Aliyu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na fadar gwamnati Abubakar Bawa ya fitar.

 

A cewar sanarwar, gwamnan ya nuna damuwa kan yadda nauyin kuɗaɗen da ake ɗora wa ma’aurata kafin aure ke ƙara wahalar da samun aure.

 

Gwamnan ya ce wannan dabi’a ta sa yawan mutanen da ba su yi aure ba ya ƙaru a jihar, wanda hakan ke haifar da yawaitar rashin tarbiyya a tsakanin matasa da ba su da hali su biya kuɗaɗen da ake buƙata kafin auren.