Kungiyar Manchester City ta buga wasannin firimiya guda 30 a jere ba tare da an doke ta ba
Nasarar na zuwa ne bayan kungiyar ta doke Fulham da ci 3-2 a filin wasanta na Etih
ad
![]() |
| Babagana Umara Zulum |
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bukaci majalisar dokokin jihar da ta sahale masa karin biliyan 61 akan kasafin farko kudin na N358.7b na shekarar 2024,domin cike gibi da gudanar da wasu ayyuka.
Kakakin majalisar dokokin jihar, Abdulkarim Lawan ne ya karanta wasikar gwamnan a zauren majalisar a yau
Ƙarin kasafin kudin dai zai shafi muhimman ayyuka da suka lalace sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi a ranar 10 ga watan Satumba, wadda ta shafi kusan mutane miliyan 2 tare da lalata wasu sassan Maiduguri da ƙananan hukumomin da ke kewaye da ita.
Kasafin zai kuma kunshi kudaden da gwamnati ke kashewa wajen bayar da agajin gaggawa, tallafawa manoma, farfado da tattalin arziki da kuma kula da muhalli.
A ranar Alhamis ne Gwamna Zulum ya zagaya domin tantance wurare, hanyoyi,da asibitocin da suka lalace sakamakon ambaliyar ruwan domin tantance su.
![]() |
| Gwamnan jihar Borno/Baba Gama Umarar Zulum |
Kwamishinan Lafiya da ayyukan al’umma,na jihar Farfesa Baba Gana ya bayyana hakan a cibiyar kula da ido da ke Maiduguri, ya ce daga cikin samfura dari biyu da aka aika domin yin gwaji, goma sha bakwai sun kamu.
A cewarsa bullar cutar ta samo asali ne sakamakon ambaliyar ruwa da aka yi kwanakin baya a sassan jihar.
Farfesan ya ce wuraren da aka samu bullar cutar sun hada da Jere, Mafa, Konduga da kuma Dikwa.
A cewar sa haryanzu ba a samu rahoton mace-mace ba, kwamishinan ya ce ana samun karuwar masu kamuwa da cutar kwalarar a kananan hukumomin da dama, musamman ma a lokacin da jihohin Adamawa da Yobe da ke makwabtaka da ita cutar ta bulla.
Ya ce an samu rahoton mutum 451 da ake zargin sun fito ne daga kananan hukumomi daban-daban amma 17 ne aka tabbatar sun kamu da cutar.
Don haka gwamnatin jihar ta ba da sanarwar daukar matakin gaggawa don shawo kan barkewar cutar, yayin da hukumomin jin kai kamar hukumar lafiya ta Duniya WHO da Médecins Sans Frontières MSF suka samar da kayayyakin shawo kan matsalar, kuma an samar da alluran rigakafi kusan 400,000.
![]() |
| Hoto/Bankin Duniya |
Bankin Duniya ya amince da rancen dala miliyan 500 don tallafa wa aikin da ake yi na samar da wutar lantarki mai dorewa ga Nijeriya, SPIN, da nufin rage kalubalen da ke addabar aikin.
Daraktan Bankin Duniya dake kula da samar da ababen more rayuwa na Yammaci da Tsakiyar Afirka,Chakib Jenane,ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai wa ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli a Abuja ranar Alhamis.
Mista Jenane ya ce an amince da aikin ne a yayin taron da bankin duniya ya yi a ranar 26 ga watan Satumba, inda ya kara da cewa an shirya fara aikin ne a watan Janairun 2025.
A cewarsa, an tsara yin aikin ne domin magance matsalolin da suka shafi yanayi, da suka hada da ambaliyar ruwa ta hanyar amfani da shi wajen aiwatar da aikin , ya ce aikin zai amfanar da kusan mutane 950,000 da suka hada da manoma da makiya ya.
Jenane ya jaddada bukatar Nijeriya ta ci gaba da shirye-shiryen cika sharudan da suka rage domin fara aikin a watan janairu na shekarar 2025.
![]() |
| Sanata Rabiu Musa Kwankwaso |
Tsohon dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce da halin matsi da ake ciki a Nijeriya, ‘yan kasar za su yunkuro don kawo sauyi a 2027.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi ‘ya’yan jam’iyyar APC da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP a jihar Kano.
Kwankwaso ya tarbi ‘yan jam’iyyar APC da suka sauya sheka daga kananan hukumomin Dala, Kiru da Gwale a gidansa da ke Miller Road a Kano.
Ya ce ‘yan Nijeriya musamman ’yan Arewa sun sha wahala sosai a wannan lokacin kuma babu wani da zai tsorata su da zai sa su canja ra’ayinsu.
A cewar sa ya kamata ‘yan Nijeriya su sake tunani, yanzu ta bayyana a fili cewa al’umma na shan wahala a gwamnatin APC kuma ba za su gyara ba.
Ya kara da cewa ko da shirin su na amfani da jami’an tsaro da INEC a zabe mai zuwa, hakan ba zai yiwu ba saboda ‘yan Nijeriya sun gaji kuma tabbas za su yi fafutukar kawo sauyi.
![]() |
| Yahaya Bellon/Tsohon gwamnan jihar Kogi. |
Wata babbar kotun tarayya da ke Maitama ta yi sammaci ga tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, inda ta umarce shi da ya gurfana a gaban ta a ranar 24 ga Oktoba, 2024.
Ana tuhumar Yahaya Bello ne tare da wasu mutane biyu Umar Oricha da Abdulsalami Hudu a bisa wasu sabbin tuhume tuhume guda 16 da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin Kasa zagon kasa ta EFCC ta kai gaban ta.
A baya dai wata kotun karkashin mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da sammacin kama shi a ranar 17 ga watan Afrilu.
Yahaya Bello na fuskantar tuhume tuhume 19 da suka shafi karkatar da kudade da kuma karkatar da naira biliyan 80.2 a gaban kotun mai shari’a Nwite amma ya kasa gurfana a gaban ta.
Mai shari’a Maryanne Anenih, wacce aka shigar da sabbin tuhume tuhumen a gabanta, ta yanke hukunci a ranar Alhamis dinnan cewa, dole ne tsohon gwaman ya gurfana a gaban kotu domin ya kare kansa kan tuhume tuhumen da ake masa.
Sammacin ya biyo bayan bukatar da hukumar EFCC ta shigar gaban ta,hukumar dai ta yi ikirarin cewa Yahaya da wadan da ake tuhuma sun karkatar da kudaden da aka damka musu.
A hukuncin da ta yanke, Mai shari’a Anenih ta umurci hukumar EFCC da ta buga sammacin a cikin wata jarida da ke yaduwa da kuma manna kwafin sammacin a wuraren da ake gani iya gani.