DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
Home Blog Page 389

‘Yan Nijeriya 400 da Dubai ta dawo dasu sun sauka a Abuja

‘Yan Nijeriya 400 da Dubai ta dawo dasu sun sauka a Abuja

An dawo da ‘yan Nijeriya dari hudu daga hadaddiyar daular Larabawa Dubai, inda suka iso Nijeriya, kamar yadda wani rahoto da gidan talabijin na Nijeriya ya fitar.

Jami’an ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tare da hadin gwiwar hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure da kuma hukumar hana safar mutane ta kasa ne suka tarbi mutanen a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.

Wa’yanda aka maido dasu dari hudu da suka hada da mata 90 da maza 310 daga Dubai din sun shiga kasar ne da zummar karatu daga bisani suka bige da kwadago ba tare da takar da ba.

Idan za a iya tunawa,ko a kwanakin baya gwamnatin tarayya ta dawo da ‘yan Nijeriya 190 daga Hadaddiyar Daular Larabawa a watan Yulin 2024.

A watan Yuni, bayan tattaunawa da dama da hukumomin UAE, gwamnatin Nijeriya ta tabbatar wa ‘yan kasar cewa nan ba da dadewa ba za a dage haramcin biza. A daidai wannan lokaci ne aka bayyana cewa Najeriya ta biya kashi 98 cikin 100 na dala miliyan 850 da ake bin kasar, lamarin da ke nuna an samu ci gaba wajen warware takaddamar dake tsakanin kasashen.

Osimhen dan wasa ne maikyau amma banason salon wasan sa– Mourinho

Osimhen dan wasa ne maikyau amma banason salon wasan sa– Mourinho

Kocin kungiyar Fenerbahce, Jose Mourinho, ya caccaki Victor Osimhen kan halinsa a filin wasa.

Shahararren kocin ya yarda cewa Osimhen, tare da dan wasan gaba na Liverpool Mohammed Salah, a matsayin manyan ‘yan wasan kwallon kafa na Afirka a duniya.

Sai dai tsohon kocin na Chelsea da Manchester United ya yi ikirarin cewa dan wasan na Najeriya ya na da sharri a cikin filin wasa.

Dan wasan ya koma Galatasaray ne a matsayin aro a makon da ya gabata bisa rashin jituwa da ya samu da Napoli.

Kocin Fenerbahçe ya shawarci Osimhen da ya canza halayensa idan yana son ya ci gaba da samun nasara a fagen kwallon kafa.

A cewar sa Osimhen babban dan wasa ne,kuma zai iya bugamin wasa saboda kyakkyawar alaka ta dashi

Jami’an tsaro sun kama alburusai 610 a Katsina

Jami’an tsaro sun kama alburusai 610 a Katsina

Jami’an tsaron da gwamnatin jihar Katsina ta kafa,na Community Watch Corps, sun cafke wata mota makare da alburusai 610 a karamar hukumar Batsari da ke jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Nasir Muazu ya fitar ranar Laraba a Katsina.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Batsari na daga cikin kananan hukumomin da ke kan gaba wajen fuskantar matsalar rashin tsaro.

Yace jami’an mu sun gudanar da wani gagarumin aiki a ranar 10 ga Satumba, 2024, da misalin karfe 7:30 na dare, a garin Batsari.

A bisa ga sahihan bayanan sirri, jami’an sun kama wata motar haya, dauke da fasinjoji 17 – mata 13 da maza hudu, ciki har da direban motar.

A lokacin da jami’an suke gudanar da bincike a wani shingen binciken ababen hawa, sun gano tarin alburusai da aka boye a karkashin kujerar mota, inda daga baya aka gano akwai harsashin harsasai 610 na AK-47 da kuma Mashin.

Za a fuskanci ɓarkewar kwalara, rashin abinci da tsaro a Maiduguri in ji MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi game da yiyuwar barkewar cutar kwalara a sansanonin ‘yan gudun hijira na wucin gadi da aka kafa a Maiduguri, babban birnin Borno sakamakon ambaliyar ruwa da ya mamaye jihar.
Rahoton da ofishin kula da ayyukan bada agaji na Majalisar Dinkin Duniyar ya fitar, yace abubawan da za’a bukata cikin gaggawa sun hada da abinci da tsaro da wurin kwana da kuma tsaftataccen ruwa, inda ya kara da cewar wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurbace, kuma na iya janyo barkewar cututtuka irinsu kwalara.
An ruwaito rahoton na cewa, “bukatun gaggawa da ake dasu sun hada da abinci da matsuguni da tsaftataccen ruwan sha, saboda wasu daga cikin hanyoyin samun ruwan sun gurbace.
Tsaro na daga cikin muhimman abubuwan damuwa, musamman ga yaran da basa tare da kowa ko suka rabu da danginsu da tsofaffi da masu bukata ta musamman.
Wuraren da ambaliyar tafi shafa a birnin Maiduguri sun hada da Gwange da Hanyar Bama da Gidan Namun Daji da Gidan Waya da Sakatariyar Jihar da Titin Legas da Fadar Shehun Borno da babbar kasuwar Maiduguri da yankunan Custom da Gamboru da Budum da Asibitin Kwararru da kuma gaba dayan yankin gidan waya.
Mutane da dama sun rasa matsugunansu, sai dai mahukunta, sun shaida cewa wasu sun soma komawa gidajensu.

Manufofin Tinubu sun kara wahalhalu ga ‘yan Nijeriya– APC

 Manufofin Tinubu sun kara wahalhalu ga ‘yan Nijeriya– APC

Jam’iyyar APC mai mulki ta amince cewa manufofin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bullo da shi sun kara wahalhalun tattalin arziki a Nijeriya.

Sakataren yada labaran jam’iyyar APC na kasa Barista Felix Morka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yayin da yake mayar da martani ga tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa maso Yamma Salihu Mohammed Lukman.

Lukman dai ya zargi jam’iyyar APC da gazawa ga ‘yan Nijeriya, inda ya kara da cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma shugaban kasa mai ci Bola Ahmed Tinubu sun kasa cika alkawuran da suka dauka a yakin neman zabe.

Lukman ya kuma bukaci shugabannin ‘yan adawa da su hada kai su yi aiki tukuru don ganin bayan gwamnatin APC a zaben 2027.

Da yake mayar da martani, Morka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata ya bayar da hujjar cewa Shugaba Tinubu na daukar matakai masu tsauri don sake farfado da tattalin arzikin kasar da ya dade yana karyewa, yana mai bayanin cewa sauye-sauyen da ya yi sun kara wahalhalun tattalin arziki a kasar.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaba Tinubu tana daukar kwararan matakai don sake farfado da tattalin arzikin kasar, da inganta tsaron kasa da kuma maido da kasar nan zuwa ga ci gaba mai dorewa.

Ya ce wadannan sauye-sauyen da babu makawa sun kara wa al’ummarmu wahalhalun tattalin arziki. Hasali ma rashin son gwamnatocin da suka gabata na yin wadannan gyare-gyare da magance matsalolin da suka samo asali ne ya sa tattalin arzikin kasar ya dade yana cikin tabarbarewa.

Amma bisa sabon tsarin fatan gwamnatinsa, ya zabi ya magance matsalolin tattalin arzikin kasar nan domin amfanin ‘yan Nijeriya baki daya.

ASUU ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a Jami’ar Gombe

ASUU ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a Jami’ar Gombe

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ta sanar da yajin aikin sai baba-ta-gani a Jami’ar Jihar Gombe (GSU) bisa la’akari da wasu matsalolin walwalar ma’aikata.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Larabar nan, shugaban kungiyar ASUU reshen jihar, Dakta Suleiman Salihu Jauro, ya ce yajin aikin ya zama dole sakamakon rashin kayan koyo da koyarwa a jami’ar.

Ya ce a cikin shekarun da suka gabata, kungiyar ta yi kokarin wasu dabaru tare da warware matsalolin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.

Wasu daga cikin batutuwan sun hada da rashin aiwatar da yarjejeniyar aiki (MoA) na shekarar 2021 tsakanin kungiyar ASUU da gwamnatin jihar, kan karin kudade ga jami’ar da kuma rashin biyan kudaden da aka tara na Academic Allowances (EAA).

Sauran manyan abubuwan da ke cikin shirin MoA na 2021 da gwamnati ta soke shi ne samar da Naira miliyan 50 ga jami’a a duk shekara.

Ya ce kusan shekaru hudu da rattaba hannu kan yarjejeniyar, har yanzu gwamnatin jihar ba ta biya kobo.

Shugaban na ASUU ya koka da cewa rashin biyan kudin EAA sama da shekaru biyar ya sa ma’aikatan ke ci gaba da fuskantar matsaloli wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu duk da rashin yanayin aiki mekyau.

Ya bayyana cewa akwai kuma batun rashin biyan bashin karin girma na shekaru hudu da rashin aiwatar da kashi 35 cikin 100 na albashin ma’aikata da kuma kashi 25 na albashin ma’aikatan ilimi.

Kungiyar ta ce gazawar da gwamnati ta yi wajen mutun ta yarjejeniyar ya sa kungiyar ba ta da wani zabi illa ta shiga yajin aikin da ba a taba gani ba.

Gwamnatin Jigawa za ta kashe N300bn a fannin lafiya,Ilimi da samar da hanyoyi

Gwamnatin Jigawa za ta kashe N300bn a fannin lafiya,Ilimi da samar da hanyoyi 

Gwamnatin jihar Jigawa za ta kashe sama da Naira biliyan 300, da nufin inganta hanyoyin da jihar ke da su, da ilimi da kuma fannin kiwon lafiya.

A zaman da majalisar zartaswar jihar ta yi a jiya, Gwamna Malam Umar Namadi ya jaddada aniyar gwamnati na samar da ababen more rayuwa ga al’ummar Jihar.

Gwamna Umar Namadi ya ce wadannan ayyuka za a yi su ne domin bunkasa tattalin arziki, da inganta rayuwa, da kuma sanya jihar Jigawa a matsayin cibiyar zuba jari da ci gaba.

Gwamnan ya bayyana cewa an bayar da kwangilar ginawa da gyaran hanyoyi guda 45, wanda ya kai kilomita 835.36, duk cin Naira biliyan 300.46.

Sauran ayyukan sun hada da biliyan 16.03 na kiwon lafiya, sai miliyan 473.62 na samar da ruwa, da kuma miliyan 871.69 na ilimi.

Don tabbatar da kammala aikin a kan lokaci, ya ce gwamnati ta amince da biyan kashi 10% na jimillar kudaden kwangilar da aka baiwa ayyukan.

Sama da mutum miliyan daya ambaliyar ruwa ya shafa a Maiduguri – Zulum

Sama da mutum miliyan daya ambaliyar ruwa ya shafa a Maiduguri – Zulum

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce adadin mutane miliyan 1 ne ambaliyar ruwa ta shafa a jihar,da ta faru a ranar Talata.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai, yayin da yake raba kudade da dafaffen abinci ga ‘yan gudun hijirar da suka fake a sansanin Bukassi,a Maiduguri.

Ya ce an kafa kwamitin bayar da agajin gaggawa na lafiya domin dakile annobar ambaliyar ruwa a Maiduguri da birnin Jere.

Ya ce ya zuwa yanzu, ba mu iya tantance yawan asarar da aka yi ba, amma kusan kashi daya bisa hudu na daukacin garin Maiduguri ya cika da ruwa.

Gwamnan ya ce mutanen da abin ya shafa sun kai miliyan 1, abin da muke yi a safiyar yau shi ne samar da agajin gaggawa, wanda ke da kyau da kuma bayar da abinci

Zulum ya bayyana cewa, tawagar bincike da ceto ta fara gudanar da ayyuka a fadin yankin al’ummomin da abin ya shafa domin tantance adadin asarar rayuka da dukiyoyi,za a tattara bayanan mutanen da abin ya shafa.

Gwamnan ya ce ya samu Naira biliyan 3 da aka ware don shawo kan ambaliyar ruwa daga Gwamnatin Tarayya kuma za a yi amfani da ita wajen magance kalubalen da ambaliyar ta shafa.

Jami’an ‘yan sanda 32 ne kawai ke tsare kauyuka 200 a Katsina – Gwamna Radda

Jami’an ‘yan sanda 32 ne kawai ke tsare kauyuka 200 a Katsina – Gwamna Radda

Gwamnan jihar Katsina Dikko Ummar Radda ya sake yin tsokaci kan kalubalen tsaro da ke ci gaba da addabar jihar.

Yayin da yake hira da DW Hausa, gwamnan ya ce jami’an ‘yan sanda 32 ne kawai ke sintiri a karamar hukuma daya a jihar.

Gwamnan, wanda bai bayyana ko wane daga cikin kananan hukumomin ba, ya ce ya kunshi unguwanni 10 da kauyuka sama da 200.

A cewarsa, a cikin jami’an 32, bindigu guda tara ne kawai ke da su, inda guda biyar kacal suke aiki.

Ya ce a yanzu haka a Katsina akwai karamar hukuma mai ‘yan sanda 39 da bindigu guda tara, kuma bindigogin da zasu iya aiki su biyar ne.

Mun bullo da wani shiri wanda duk wata al’umma da ke shirye ta kare kanta, za mu ba su goyon baya da horon da ya dace don kare kai kafin zuwan jami’an tsaro.

Katsina ta sha fama da munanan hare-hare daga ‘yan bindiga.

Ko a kwanakin baya Gwamna Radda ya yi kira ga al’ummar jihar da su dauki matakan kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.

Ya yi wannan jawabi ne a wani taro da aka yi a Daura.

A cikin wani faifan bidiyo da ya yadu, Radda ya fusata sosai, ya kuma bukaci malaman addinin Musulunci da su fadakar da ‘yan kasar muhimmancin kare kai kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kudin shiga da gwamnatin tarayya ke samu ya karu zuwa N9.1trn a 2024- Minista

Kudin shiga da gwamnatin tarayya ke samu ya karu zuwa N9.1trn a 2024- Minista

Ministan Kudi, Wale Edun ya ce kudaden shiga na gwamnatin tarayya na wata uku na farko na shekarar 2024 ya karu zuwa Naira tiriliyan 9.1.

Ministan ya bayyana hakane lokacin da yake jawabi a ranar Talata a wajen taron (CIBN) karo na 17 na bankin da hada-hadar kudi a Abuja, Edun ya ce wannan ya ninka sau biyu akan na 2023.

Edun, wanda ya samu wakilcin Armstrong Takang, manajan darakta a ma’aikatar kudi, ya ce karin kudaden shiga na nuna nasarar manufofin tattara kudaden shiga na gwamnati da kuma yadda ake amfani da fasaha wajen cigaban aikin.

Yace duk da wannan ci gaban, babban kalubalen da muke fuskanta shi ne magance hauhawar farashin kayan abinci. Amma Shirye-shirye sun yi nisa don inganta tare da wadatar abinci, dakile hauhawar farashin kayayyakin abinci.

Ministan ya kuma ce sauye-sauyen haraji na da tasiri, yana mai cewa gwamnati ba ta kara haraji ba.