Kasashe 15 na duniya ne za su shiga gasar karatun Al-Qur’ani da ke tafe, ciki hada Nijeriya
Za mu kamo Bello Turji – Janar Christopher Musa
Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya Janar Christopher Musa ya sha alwashin cafke kasurgumin dan bindigan nan Bello Turji cikin kankanen lokaci.
Christopher Musa ya bayyana hakan ne a Abuja, ya yin da yake zantawa da manema labarai.
Bello Turji na daya daga cikin jagororin ‘yan bindiga da ya addabi yankin Arewa maso Yamma, yana zaune a dajin jihar Zamfara.
Kwanan nan Bello Turji ya sanya harajin Naira miliyan 30 ga mazauna wani yankin domin kare kansu da kada ya kaimasu hari.
Ambaliyar ruwa ta sa fursunoni da dama sun tsere a Borno
Rahotanni sun bayyana cewa fursunoni da ba a bayyana adadinsu ba a tsohun gidan yari na Maiduguri sun tsere bayan faduwar katangar gidan sanadiyyar ambaliyar ruwan sama.
Hukumomin gidan yarin sun tabbatar da faruwar lamarin, kuma sun sanar cewa wadanda suka tsere suna da matukar hadari.
Sai dai an bayyana cewa jami’an tsaro na ci gaba da farautar fursunonin da suka arce
APC ta caccaki Kwankwaso kan shinkafar Tinubu a Kano
Jam’iyyar APC a jihar Kano ta caccaki jagoran Kwankwasiyya, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso, kan sukar tsarin da gwamnatin tarayya na rabon kayan abinci a jihar.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaban Jam’iyyar, Abdullahi Abbas, ya ce Gwamnatin Tarayya ta dukufa wajen ganin an kawar da yunwa a kasar, amma gwamnatin NNPP a Jihar na kawo cikas ga kokarin.
Abbas ya kuma musanta zargin Kwankwaso na cewa rabon kayan ga yan Jam’iyyar APC ne kawai.
Shugaban jam’iyyar APC ya ci gaba da cewa, duk da gargadin da gwamnatin jihar ta yi na cewa za ta tunkari duk wanda aka samu da hannu wajen karkatar da kayan abinci, amma an gano manajan Darakta na KASCO, Dakta Tukur Dayyabu Minjibir da hannu a sayar da hatsin gwamnatin jihar.
Ambaliyar ruwa ta cinye wata makabarta a Borno
Ambaliyar ruwa ta cinye wata makabarta yayin da wasu namun daji suka arce daga gidan zoo na Maiduguri jihar Borno.
Jaridar Daily Trust ta ba da labarin yadda aka wayi garin Talatar nan da ambaliyar a cikin birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.
Rahotanni sun ce har namun dajin da ke gidan adana namun daji na Shehu Sanda Kyarimi sun arce, da bayanai suka ce akwai hatsari sosai tattare da kubcewar wadannan namun daji, musamman ga al’ummar da ke yankin.
Ruwan dai ya cike Maiduguri Bypass da hanyar gidan namun daji ta zoo road, har zuwa kwalejin koyon aikin kiwon lafiya ta College of Health Technology Maiduguri.
Baya ga wadannan wurare, bayanai sun kuma ce ambaliyar ruwan ta malaya har zuwa wata makabarta da kiristoci ke binne ‘yan’uwansu idan sun mutu ta wajen gidan Amb Baba Ahmad Jidda a tsohuwar GRA.
Kazalika, jami’ar Maiduguri ta UNIMAID ma ta sanar da dakatar da harkokin karatu har sai an ga abin da hali ya ba da.
A cikin wata sanarwa daga magatakardan jami’ar Ahmad A Lawan, ta ce jami’ar ta yanke shawarar hakan, inda take jajanta wa malamai, ma’aikata da daliban jami’ar bisa wannan ibtilai da ya faru.
Shugaba Tinubu zai karrama muhimman mutane da Lambobin yabo
Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da fara shirye shiryen bada lambar yabo ta kasa na shekarar 2024 ga ‘yan Najeriya wadanda suka ba da gudunmawa wajen ci gaban kasar.
Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati Zaphaniah Jisalo ne ya bayyana haka a wajen wani taro na ma’aikatar a Abuja.
Jisalo ya kara da cewa gwamnatin tarayya za ta karrama ‘yan kasar da suka yi fice a fannoni daban-daban.
Ministan ya ce fom din tsare-tsare da za su kai ga bayar da lambar yabon kyauta ne
Majalisar wakilai ta umarci JAMB da ta tura N3bn ga asusun gwamnatin tarayya
Majalisar wakilai ta umurci hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB da ta tura naira biliyan 3.602 ga asusun hadakar kudaden shiga na gwamnatin tarayya.
Shugaban kwamitin kula da harkokin jama’a, Bamidele Salam ne ya bayar da wannan umarni a yayin wani zaman bincike ga hukumar a Abuja, wanda hukumar kula da kasafin kudi ta (FRC) ta bukata.
Salam ya ce wannan lamari ne na doka, kuma ba shi da alaka da banbancin kashi 25 da kashi 50 bisa 100 kamar yadda hukumar JAMB ta ce.
Rashin Tinubu a gari ya sa muka dage taron mu na masu ruwa da tsaki – APC
Jam’iyyar APC ta dage taron ta na kwamitin zartarwa da ta shirya yi a ranar 11 da 12 ga wannan Satumbar 2024.
Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Felix Morka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Morka ya bayyana cewa nan gaba za’a sanar da ranakun taron lokacin da ya dace.
Jam’iyyar ta bayyana cewa an dauki matakin ne biyo bayan rashin shugaba Tinubu na halartar taron.
Barayin daji sun kutsa kai asibiti, sun sace malaman jinya a Kaduna
Barayin daji sun kutsa kai asibiti, sun sace malaman jinya a Kaduna
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ma’aikatan jinya a cibiyar kiwon lafiya matakin farko da ke kauyen Layin Dan Auta da ke gundumar Kuyello a yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
A cewar wata majiya, ‘yan bindigar sun far wa wata makarantar firamare da ke Kuyello, a wajen garin.
Sai dai kuma da suka kasa samun daliban da za su yi garkuwa da su, an ce sun koma asibitin da ke kusa inda suka yi awon gaba da ma’aikatan jinya da ke bakin aiki.
Wani shugaban al’ummar yankin da ya bukaci a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana lamarin a matsayin abin damuwa.
Yace suna isa unguwar suka wuce kai tsaye wata makaranta da ke kusa da su, a zatonsu za su sami dalibai. Sai dai makarantar babu kowa, don haka suka wuce PHC da ke Kuyello suka yi awon gaba da ma’aikatan jinya da ke bakin aiki,
Shi ma wani shugaban matasan Kuyello, Baba Isah ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya bayyana cewa ma’aikatan jinya biyu suna bakin aiki lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari. Har yanzu dai ba a san ko an sace wasu majiyyata ba, saboda yawancin sun bar asibitin.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnatin jihar ko kuma ta ‘yan sanda.
Kuma an kasa samun wayar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan.
Mun san wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar da aka yi a watan Augusta, PDP ta fadawa Tinubu
Mun san wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar da aka yi a watan Augusta, PDP ta fadawa Tinubu
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa ta san wadanda suka dauki nauyin zanga-zangar #EndBadGovernance da ta da akayi a watan Agusta.
Wasu ‘yan Nijeriya da kungiyoyi sun fito kan tituna a garuruwa da dama tsakanin ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agusta domin nuna adawa da wahalhalun da ake fama da su a kasar.
Da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja a ranar Litinin, Debo Ologunagba, Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na kasa, ya bayyana cewa yunwa ce ta dauki nauyin zanga-zangar, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta kama yunwa ba ‘yan Najeriya ba.
Ologunagba ya yi magana ne a kan yadda aka kama shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajearo.
Kakakin PDP ya ce akwai bukatar a yi taka-tsan-tsan An yi zanga-zanga a kasar nan, gwamnati ba ta yi komai ba.

.jpeg)

.jpeg)

.jpeg)
.jpeg)
.jpeg)

