DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
Home Blog Page 391

Kungiyar kwadago ta kasa NLC shiga wata ganawar sirri kan tsare shugaban ta Ajaero

Kungiyar kwadago ta kasa NLC shiga wata ganawar sirri kan tsare shugaban ta Ajaero

Bayan tsare shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya Joe Ajaero da DSS ta yi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa kasar Burtaniya domin halartar taron ma’aikatan duniya, kungiyar NLC ta shiga wani taron sirri.

Shugaban hulda da jama’a na NLC, Benson Upah ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya fitar.

A cewar Upah, jami’an gwamnatin Nijeriya sun kama Ajaero ba tare da wani sammaci na doka ba, kuma ba a san inda yake ba da kuma halin lafiyarsa a halin yanzu.

Kungiyar ta NLC ta yi Allah wadai da tsarewar ashugaban nata ta ce wannan “aiki ne na rashin bin doka da kuma tsoratarwa” tare da neman a gaggauta sakin Ajaero ba tare da wani sharadi ba.

Majalisar ta kuma yi kira ga kasashen duniya, kungiyoyin kare hakkin dan Adam, da masu rajin tabbatar da dimokuradiyya da su lura da yadda ake samun karuwar mulkin kama-karya a Nijeriya.

An shirya Ajaero zai yi jawabi a taron da zai je a Burtaniya a madadin ma’aikatan Nijeriya, inda zai tattauna muhimman batutuwa kamar ‘yancin ma’aikata, adalcin zamantakewa, da daidaiton tattalin arziki.

A halin yanzu dai Majalisar na yin wani zama na sirri domin tattauna lamarin, kuma nan ba da jimawa ba za a bayyana sakamakon da aka samu a bainar jama’a.”

DSS ta kama shugaban NLC Ajaero

 DSS ta kama shugaban NLC Ajaero

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) Joe Ajaero.

LEADERSHIP rawaito cewa an kama Ajaero da safiyar ranar Litinin a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ajaero na shirin shiga jirgi zuwa kasar Ingila domin gudanar da wani aiki a hukumance sai DSS ta dauke shi.

Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, an bukaci Ajaero da ya halarci taron kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) da za a yi a kasar Ingila ranar Litinin.

Sai dai ba a bayyana cikakken bayani da dalilin kama shi ba, majiya mai tushe ta ce an mika Ajaero ga hukumar leken asiri ta kasa NIA.

Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) Joe Ajaero.

LEADERSHIP rawaito cewa an kama Ajaero da safiyar ranar Litinin a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Ajaero na shirin shiga jirgi zuwa kasar Ingila domin gudanar da wani aiki a hukumance sai DSS ta dauke shi.

Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, an bukaci Ajaero da ya halarci taron kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) da za a yi a kasar Ingila ranar Litinin.

Sai dai ba a bayyana cikakken bayani da dalilin kama shi ba, majiya mai tushe ta ce an mika Ajaero ga hukumar leken asiri ta kasa NIA.

Karin kudin man fetur: Gwamnatin Edo ta dage komawa makaranta

Karin kudin man fetur: Gwamnatin Edo ta dage komawa makaranta 

Gwamnatin jihar Edo ta dage komawa makaranta saboda tashin farashin man fetur da kalubalen da iyaye ke fuskanta.

A ranar litinin 9 ga watan Satumba ne za a koma makarantu a galibin sassan Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta sanya wa hannu, tace an dage ci gaba da aiki a duk makarantun gwamnati da masu zaman kansu,har sai an sanar da su zuwa.

Sanarwar ta kara da cewa wata sanarwa a hukumance daga gwamnati ta bayar da umarnin cewa makarantu za su cigaba da kasancewa a rufe saboda tashin farashin man fetur da kuma kalubalen da iyaye da masu kula da yara ke fuskanta.

A baya-bayan nan ne kamfanin mai na (NNPCL) ya kara farashin man fetur zuwa ₦ 855 karin kudin da kamfanin man fetur na kasar ya yi ya sanya wasu ‘yan kasuwa sayar da man sama da ₦900 kan kowace lita, inda wasu ke sayar da shi sama da ₦1000 kan kowace lita.

Karin harajin VAT da gwamnati ke shirin yi zai kara nakasa al’umma – Atiku

 Karin harajin VAT da gwamnati ke shirin yi zai kara nakasa al’umma – Atiku 

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya kalubalanci shirin da gwamnatin Nijeriya ke yi na kara kudin harajin harajin harajin VAT.

Atiku ya bayyana hakan ne a shafinsa na sada zumunta na Facebook a ranar Lahadi.

Atiku ya ce aiwatar da wannan mataki na iya zama “abin da zai kara jefa talakawa a cikin mawuyacin hali “

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2027 – Kwankwaso

 Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2027 – Kwankwaso

Babban jigo a jam’iyyar NNPP a Nijeriya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce shi ne zai yi nasarar lashe zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Kwankwaso, wanda shi ne ya yi wa jam’iyyar ta NNPP takarar shugaban kasa a zaben 2023, kuma shi ne ya zo na hudu a zaben, ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar a lokacin da ya kaddamar da sakatariyar jam’iyyar NNPP, a kan titin IBB, a jihar Katsina.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ce Kwankwaso ya isa jihar Katsina ne domin yin ta’aziyyar rasuwar Hajiya Dada mahaifiyar tsohon shugaban Nijeriya Marigayi Umaru Musa ‘Yar’Adua. 

Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar rasuwar mutane 20 a jihar Yobe

 Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar rasuwar mutane 20 a jihar Yobe

Mutane 20 ne suka mutu sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta addabi karamar hukumar Bade ta Yobe tun farkon watan Agusta, in ji shugaban karamar hukumar, Babagana Ibrahim.

Ibrahim ya shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Juma’a a Gashua 

Gidajen da yawancin suka rufta a yankin mafi yawa irin wadanda aka yi su ne da samfurin ginin laka.

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 20, tare da raba mutane 3,000 da muhallansu a yobe

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 20, tare da raba mutane 3,000 da muhallansu a yobe

Akalla mutane 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu a cikin makonni biyun da suka gabata a Gashua, karamar hukumar Bade a jihar Yobe sakamakon rugujewar gidaje bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Shugaban na karamar hukumar, Babagana Ibrahim ya shaidawa wakilin gidan talabijin na Channels cewa, yanzu haka mazauna yankin da dama na samun mafaka a wasu sansanoni uku da aka kebe.

A cewarsa, gwamnati na samar da agaji na gaggawa ga mutanen da suka rasa matsugunansu kamar kayan abinci, kula da lafiya,ruwan sha mai tsafta, da abinci don kare su daga barkewar wata cuta.

Yace mutanen da suka rasa matsugunansu ya haura kusan 3,000 muna bukatar gwamnatin tarayya da hukumomin bayar da agaji don tallafawa jahohi da kananan hukumomin da ambaliyar ruwa ta shafa wajen samar musu da kayan agaji.

A kwanakin nan ana ruwan sama kuma gidaje da dama suna rugujewa musamman gidajen laka.

Tuni dai aka rufe hanyoyin biyu na gwamnatin tarayya zuwa Gashua a cikin kwanaki goman da suka gabata, lamarin da ya sa ma’aikatan agaji ke shan wuya kafin isar su wajen ‘yan gudun hijirar.

Shugaban ya umurci wadanda ke zaune a gidajen laka da su fice domin dakile afkuwar ambaliyar ruwa.

Ku rage farashin man fetur, ‘yan Nijeriya na fama da yunwa, Kukah ya fadawa jam;iyyar APC

Ku rage farashin man fetur, ‘yan Nijeriya na fama da yunwa, Kukah ya fadawa jam;iyyar  APC

Babban limamin cocin Katolika na Sokoto, Mathew Hassan Kukah, ya bukaci shugabannin jam’iyyar APC mai mulki da su rage farashin man fetur a halin yanzu, yana mai cewa ‘yan Nijeriya na fama da yunwa.

Ya yi wannan jawabi ne a Juma’ar nan a Abuja, yayin da ake kaddamar da cibiyar ci gaba (TPI).

A ranar Talatar da ta gabata ne farashin man fetur a Nigeriya ya karu daga N855, zuwa N918,a gidajen man ‘yan kasuwa kuwa ana sayar da man N1000,zuwa 1200 a cikin kasar.

Kukah ya ce,‘yan Nijeriya jin yunwa, ya kamata a  nemo hanyar rage farashin man fetur a wannan lokaci.

Ya ce mu tuna da cewa idan har ba a kafa dimokuradiyya a kan ingantaccen tushe ba, to za mu yi gini a kan yashi, don haka ya kamata mu gyara matsalar dimokradiyya a Nijeriya.

‘Yan Nijeriya masu shaidar dan kasa ta NIN ne kadai za su iya sayen shinkafar da gwamnatin tarayya za ta sayar a ₦40,000 – Ministan Noma

‘Yan Nijeriya masu shaidar dan kasa ta NIN ne kadai za su iya sayen shinkafar da gwamnatin tarayya za ta sayar a ₦40,000 – Ministan Noma

Gwamnatin tarayya ta ce wadanda ke da rajistar shaidar dan kasa ta  (NIN) ne kadai za su samu damar sayen shinkafar da gwamnatin za ta sayar a naira 40,000 kan ko wane buhu.

Shugaba Bola Tinubu wanda ya samu wakilcin ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, ya ce sun dauki wannan mataki ne domin dakile tsadar kayan abinci a kasuwannin Nijeriya.

Kyari ya kara da cewa za a sayar da su a hannu ne kawai kuma namiji ko mace kowa zai iya mallakar buhu daya.

Ya ce shinkafar wacce za a sayar da ita kan kudi Naira 40,000 a kan kowane 50kg,gwamnatin tarayya ce ta sa baki wajen sayar da shinkafar don magance matsalar abinci da ake fama da ita a Nijeriya.

A cewarsa tallafin abincin ya dace a wannan lokacin idan aka yi la’akari da lokuta da kalubalen da ake ciki a wannan kasa mai girma.

‘Yan sanda sun kama wasu mutane 11 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Kaduna, tare da kwato bindigogi da harsasai

 ‘Yan sanda sun kama wasu mutane 11 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a Kaduna, tare da kwato bindigogi da harsasai

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutane 11 da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da kwato tarin makamai da makudan kudade.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan, Mataimakin Sufeto Mansir Hassan, ya ce kamen na da nasaba da sace wani hakimi a ranar 14 ga watan Agustan 2024, wanda aka sake shi bayan kwanaki biyu.

Hassan ya kara da cewa, jami’an ‘yan sanda tare da hadin gwiwar ‘yan sakai sun kai sumame kauyuka uku da ke karamar hukumar Lere, inda suka kama wasu mutane biyar tare da kwato wata bindiga kirar ganga guda, mota, babur, da kuma wayoyin hannu da dama.

A wani samame na daban kuma an kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu a wani wurin ajiye motoci, lamarin da ya kai ga kwato bindigogi kirar AK-47 guda hudu, da wasu manyan bindigogin guda biyu, da wasu makudan kudade.

Sanarwar ta ci gaba da cewa,dangane da yin garkuwa da wani hakimi a ranar 14 ga watan Agusta, 2024, wanda aka sako a ranar 16 ga watan Agustan 2024, jami’an ‘yan sanda a Saminaka tare da hadin gwiwar ‘yan sakai sun kai farmaki kauyuka uku a karamar hukumar Lere, wato Maraban Wasa Gurzan Hakimi Mariri.

An kama wadanda ake zargi guda biyar Abdulhamid Abubakar (mai suna Bala, mai shekaru 30), Danjuma Luka (wanda aka fi sani da Uba, 25), Ayuba Simon (50), da Idi Saleh (57). Kayayyakin da aka gano sun hada da bindiga guda daya, koriyar mota kirar Golf, babur Bajaj, da wayoyin hannu guda takwas.