DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Monday, April 13, 2026
Home Blog Page 392

Farashin tsohuwar masara ya tashi a wasu kasuwannin Nijeriya

A yayinda sabbin kayan amfanin gona ke fara shigowa kasuwannin jihohin Nijeriya, wasu tsoffin kayan abincin kuwa na kara tsada a wasu kasuwannin kasar.

A wannan mako ana sayar da buhun tsohuwar masara N90,000 a jihohin Adamawa da Legas, to a makon jiya ma haka aka sai da a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas.

A kasuwar Mai’adua jihar Katsina N93000 aka sai da a makon daya gabata, yayinda a wannan mako aka sayar da ita N92000

A kasuwar Dandume jihar Katsina N85,000-88000 ake sayar da buhun masarar a wannan satin, amma a makon daya gabata N88000-90,000 aka sayar da buhun.

Sai kasuwar Giwa jihar Kaduna ana sayar da buhun N83000 a wannan sati.

Masarar tafi sauki a kasuwar Dawanau a jihar Kano da ake sayar da ita akan N80,000 daidai a makon nan da ke shirin karewa, bayan da a makon jiya aka sayar da ita N90,000.

Ita kuwa Shinkafar Hausa tashi ta yi a kasuwannin jihar Adamawa wanda ake sayar da buhunta N180,000 a wannaan satin, amma a makon daya shude N156-160,000 aka sayar da buhun a kasuwar.

A kasuwar Dawanau jihar Kano an sayi buhun Shinkafar N160,000 a satin da wuce, amma a makon nan N155,000 ne kuɗinta.

A ‘yan kwanakin nan dai shinkafar Hausa tafi sauki a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas a kudancin Nijeriya, inda ake sayar da ita akan N135,000 a wannan satin, yayinda a makon daya gabata aka sayar da ita a N140,000 daidai.

N145,000 ake sayar da buhun shinkafa ‘Yar gida a kasuwar Mai’adua jihar Katsina da kasuwar Giwa jihar Kaduna a wannan mako.

An sayi buhunta N165-170,000 a kasuwar Dandume jihar Katsina a makon daya gabata, yayin da a wannnan mako ake sayar da buhun sabuwar Shinkafar kan kuɗi N120,00-1220000.

To a bangaren Shinkafar waje ma tafi sauki a kasuwar Mile 12 International Market Legos da ake sayar da ita a N70,000 cif a makon nan da ke mana bankwana, bayan da a makon jiya aka sayar da ita N73000.

Farashin Shinkafar Bature bata sauya zani ba dana makon jiya da ake sayar da ita N80,000 daidai a kasuwannin jihar Adamawa, haka nan ake sayar da ita a makon nan.

Ana sayar da Shinkafar waje a kasuwar Dawanau jihar Kano N97000 a wannan farko na watan na Satumban 2024, amma a makon daya shude N95000 ne kuɗinta.

To a kasuwar Giwa jihar Kaduna N85000 ne ake sayar da buhun shinkafar a wannan satin.

N83000 ake sayar da Buhunta a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a makon nan mai karewa, haka kuma aka sayar da ita a makon jiya.

A Kasuwar Dandume jihar Katsinan N72000 kuɗin buhun Shinkafa ‘yar Gwamnati a wannan mako, amma a makon daya gabata N75000 aka sai da buhun.

Farashin tsohon wake ma dai bai sauya zani ba dana makon jiya wanda aka saida N190000-200,000 a kasuwannin jihar Adamawa, to sai dai N170,000 ne ake sayar da buhun sabon wake a kasuwar a wannan satin nan.

A kasuwar Giwa jihar Kaduna ana sayar da buhun farin wake N180,000 daidai a wannan mako.

Tsohon wake yafi tsada a kasuwar Mile 12 International Market da ke jihar Legas da ake saidawa N240,000 a makon nan, bayan da a makon jiya aka sayar N180,000.

A kasuwar Dandume jihar Katsina ana sayar da buhun N140,000-150,000 a wannan mako, yayinda a makon daya gabata aka sai da N185,000

Farashin wake bai canza zani ba dana makon jiya, wanda aka sayar N135,000 a kasuwar Dawanau jihar Kano, haka nan ake sayar wa a wannan satin nan.

N120,000 ake sayar da buhun kananan wake a kasuwar Mai’adua jihar Katsina a wannan mako.

To bari mu kammala farashin kayan abinci na makon nan da Spaghetti.

Inda Har yanzu farashin taliyar yaki sauka a kasuwar Mile 12 International Market Legos da ke jihar Legas wanda ake saidawa N19000. 

A jihar Adamawa ma dai farashin bai sauya ba dana makon daya gabata da aka sayar da ita N17600.

N19,500 ake sai da kwalin taliyar a kasuwar Dawanau jihar Kano a makon nan, bayan da a makon jiya aka sayar N19,000 cif.

An samu karin N500 kan farashin taliya da aka sayar N19,500 a kasuwar Dandume jihar Katsina a makon jiya, amma a makon nan N20,000 ake sayar da ita.

A Mai’adua jihar Katsina N17,400 aka sayar da kwalin taliya a makon daya gabata, amma a makon nan N17000 ake sayar da Kwalinta.

DCL Hausa A’isha Usman Gebi

Hukumar ICPC na tuhumar Chris Ngige minista lokacin mulkin Shugaba Buhari kan batun wasu kwangiloli

Hukumar ICPC na tuhumar Chris Ngige minista lokacin mulkin Shugaba Buhari kan batun wasu kwangiloli

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta gayyaci Chris Ngige, daya daga cikin ministocin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari domin amsa tambayoyi.

Ngige, wanda ke kula da ma’aikatar kwadago da samar da ayyukan yi, an yi masa tambayoyi kan rawar da ya taka a wasu kwangiloli da ayyukan yi da suka faru a daya daga cikin hukumomin a lokacin da ya rike madafun iko.

An bayyana cewa tsohon Ministan ya kasance tare da jami’an hukumar ICPC na tsawon sa’o’i biyar a ranar Laraba domin amsa wasu tambayoyi kan yadda aka bayar da wasu kwangiloli a asusun inshorar jama’a na Nijeriya NSITF.

A baya dai Daily Trust ta bayyana yadda ICPC ta gayyaci wasu manyan jami’an NSITF domin amsa tambayoyi kan biyan N47m gratuity ga tsohon shugaban hukumar, Mrs Maureen Allagoa, a lokacin da take aiki.

Hakazalika, tsohon Ministan Kwadago, Simon Lalong, wanda yanzu haka yake a Majalisar Dattawa, ya kafa kwamitin bincike na musamman don binciki badakalar bada kwangilar da aka bayar na N1.8bn a hukumar.

Tuni dai hukumomin yaki da cin hanci da rashawa — ICPC da EFCC suka shiga cikin lamarin tare da gayyata ta baya-bayan nan ga tsohuwar ministar. An gayyaci Ngige ne a lokacin da yake kasar Amurka domin duba lafiyarsa.

Kashim Shettima ya gayyaci Lokpobiri, Kyari zuwa villa kan karin farashin man fetur

Kashim Shettima ya gayyaci Lokpobiri, Kyari zuwa villa kan karin farashin man fetur

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya gayyaci karamin ministan albarkatun Man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, da Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, zuwa Aso Rock.

Shi ma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu ya halarci taron wanda hakan bai rasa nasaba da karin farashin mai.

Haka kuma a taron akwai wasu jami’an gwamnati daga ofishin mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.

Karin farashin man fetur na baya-bayan nan ya sa farashin sufuri ya tashi sama da kashi 50 a manyan biranen Nijeriya.

Sabon karin farashin, wanda Kamfanin (NNPCL) ya aiwatar, ya tashi daga N855 zuwa N897 kowace lita, ya danganta da wurin da ake ciki, daga N568-N617 a baya.

‘Yan kasuwa masu zaman kansu sun maida farashin su zuwa tsakanin N930 zuwa N1,200 kowace litar man fetur.

Majalisar dokokin Kano ta amince da kasafin kudin cike gibi N99.2bn da gwamnatin jihar ta aike mata

Majalisar dokokin Kano ta amince da kasafin kudin cike gibi N99.2bn da gwamnatin jihar ta aike mata

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da  kasafin kudin cike gibi na naira biliyan 99.2 ta da gwamnatin jihar ta aike mata akwanakin baya.

An amince da kasafin kudin cike gibin ne bayan majalisar ta yi zama na Uku a yau alhamis

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudin cike gibin a ranar 26 ga Agusta, 2024 inda ya nemi a kara kasafin kudin zuwa N536, 559, 816, 357.84 daga farkon N437, 338, 312, 787 da aka sanya wa hannu a watan Disamba 2023.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Hon Aminu Sa’ad, ya bayyana cewa kashi 58% na kasafin kudin an ware su ne domin a cigaba da yiwa al’umma aikin raya kasa.

Hon Sa’ad ya kara da cewa karin kasafin kudin zai kunshi zabukan kananan hukumomi da ke tafe, da biyan sabon mafi karancin albashi, da kudin gudanar da aiki a sabbin ma’aikatun da aka kafa da sake bude cibiyoyin koyar da sana’o’i da sauran ayyukan da gwamnati ta sa gaba.

Hakazalika, Majalisar ta kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gina dakunan kwanan dalibai domin samar da ingantattun masauki ga daliban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil.

Haryanzu kamfanin NNPCL Ltd bai fara daukar man fetur din mu ba – Dangote

Haryanzu kamfanin NNPCL Ltd bai fara daukar man fetur din mu ba – Dangote

Kamfanin Dangote ya yi watsi da rahotannin da ke cewa kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya fara daukan man fetur daga matatarsa.

Wata jarida ta ruwaito cewa NNPCL ya dauko man fetur daga matatar Dangote ya sayar wa ‘yan Nijeriya kan Naira 897 kan kowace lita.

Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote ya bayyana cewa matatar ta shirya don fara hakowa da sayar da man fetur.

Sai dai kuma, Anthony Chiejina, Babban Daraktan Sadarwa na Rukunin Dangote, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce har yanzu kamfanin na NNPC bai fara dauke mai daga matatar man ba.

A cewar Rukunin Dangote, kasuwar man fetur tana da ka’ida sosai, don haka kamfanin ba zai iya tantancewa,ko tasiri kan farashin man da ke karkashin kulawar hukumomin gwamnati da abin ya shafa ba.

Muna so mu bayyana cewa NNPC bai fara daukar tataccen mai ba.

Don haka batun kayyade farashin man fetur da aka ce anyi daga matatar man bai taso ba, domin har yanzu ba mu kammala kwantiragin mu da NNPC ba.

Kasuwar PMS tana da kayyadadden tsari, wanda duk ‘yan kasuwar mai da masu ruwa da tsaki a fannin suka sani, don haka ba za mu iya tantancewa ba.

Muna kira ga jama’a da su yi watsi da labaran da ake yadawa domin yaudara ce kuma ba gaskiya a wannan lamari. Muna ba wa ‘yan Nijeriya tabbacin samun ingantataccen man fetur da za a samu cikin sauki a duk fadin kasar.

Burkina Faso ta fitar da sabon fasfo ba tare da tambarin ECOWAS ba

Burkina Faso ta fitar da sabon fasfo ba tare da tambarin ECOWAS ba

Burkina Faso ta fitar da wani sabon fasfo na biometric ba tare da tambarin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ba.

Ministan tsaron Burkina Fasfo Mahamadou Sana ne ya kaddamar da sabon fasfo din

Idan za a iya tunawa, Burkina Faso, Nijar da Mali, sun yanke hulda da ECOWAS, sakamakon takunkumin da aka kakaba musu saboda juyin mulkin da sojoji suka yi.

Da take mayar da martani, ECOWAS ta zargi kasashen uku da nufin tauye ‘yancin walwalar yankin.

Sana ya shaida wa manema labarai a wajen kaddamar da fasfo din cewa, wannan sauyin ya zo ne ga matakin da Burkina Faso ta dauka na ficewa daga kungiyar ECOWAS, wadda aka yi a watan Janairu.

Ya ce, A kan wannan fasfo, babu tambarin ECOWAS. Tun daga watan Janairu, Burkina Faso ta yanke shawarar janyewa daga wannan ECOWAS, kuma wannan shi ne kawai fahimtar matakin da Burkina Faso ta riga ta dauka.

Karin kudin man fetur zai munana irin talaucin da ma’aikatan Nijeriya ke ciki-kungiyar TUC

Karin kudin man fetur zai munana irin talaucin da ma’aikatan Nijeriya ke ciki-kungiyar TUC

Hadaddiyar kungiyar kwadago ta Nijeriya (TUC) ta yi fatali da karin farashin man fetur na baya-bayan nan, inda ta yi gargadin cewa hakan zai kara ta’azzara talauci a tsakanin ma’aikata.

Kungiyar ta bayyana matsayin ta ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba.

Shugaban kungiyar ta TUC, Kwamared Festus Osifo, wanda ya sanya hannu kan sanarwar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar soke wadannan shawarwari, ta inganta manufofin da za su karfafa Naira, da kuma daukar kwararan matakai don rage radadin da ’yan Nijeriya ke ciki.

Ta yi nuni da cewa ba zato ba tsammani an kara farashin ba tare da tuntubar al’umma ba, yana nuna rashin kula da jin dadin al’ummar Nijeriya, musamman ma’aikatan da ke da alhakin irin wadannan shawarwari.

Ya kara da cewa yunkurin  kara farashin mai da wutar lantarki ba zato ba tsammani zai kara ta’azzara wahalhalun da ake ciki ga al’umma.

Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta soke wadannan abubuwa, ta inganta manufofin da za su karfafa Naira da kuma daukar kwararan matakai don rage radadin ’yan Nijeriya. Dole ne gwamnati ta yi gaggawar maido da kwarin gwiwa tare da hana ci gaba da tabarbarewar yanayin rayuwar ‘yan kasarta.

Domin TUC ta damu matuka da karin farashin wutar lantarki da kashi 250 cikin 100, inda ta ce wutar lantarki na da matukar muhimmanci ga rayuwar marasa galihu a cikin al’umma.

Nijeriya ba ta da wata wahalar jagoranta, shugabanni na gari ta rasa in ji Obasanjo

Nijeriya ba ta da wata wahalar jagoranta, shugabanni na gari ta rasa in ji Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi mamakin yadda kasar nan ke kara a tabarbarewa ga rashin ingantaccen shugabanci, yana mai cewa kasar ba ta da wahalar jaroganta.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron tunawa da marigayi Akintola Williams, mai taken: ‘Leadership Dynamics: Current Realities And Way Forward,’ wanda Cibiyar Chartered Accountants of Nigeria (ICAN) ta shirya a Legas.

Sai dai ya amince da irin sarkakiyar da kasar ke ciki, sai dai ya jaddada cewa ginshikin ci gaban al’umma shi ne umarni da shugabanci na gari.

Yace a koyaushe ina cewa Nijeriya kasa ce mai sarkakiya, dole ne ku fahimci hakan amma Nijeriya ba kasa ce mai wahalar jagoranta ba. Dole ne sai kun kasance masu gaskiya da rikon amana.

Ya bayyana yadda ya zama shugaban kasa, inda ya tabbatar da cewa ya yi wa kasa hidima da albarkatun da take dashi, yana mai cewa kasar na da tattalin arziki mai kyau.

Yakara da cewa lokacin da nake shugabanci, na yi duk abin da ya kamata na yi wa Nijeriya kuma zan iya bugun kirjina in fadi haka.

Na karbi ragamar tafiyar da harkokin Nijeriya a matsayin zababben shugaban kasa da N3.7b a ajiya kuma muna kashe N3.5b wajen biyan basussukan aiki a lokacin.

An samu ‘yan majalisar dokokin Nijeriya 164 da ba su taba gabatar da kudiri ba

Wani rahoto da OrderPaper, kungiyar sa ido a majalisar dokokin Nijeriya ya fitar, ya nuna cewa Sanatoci 15 da ‘yan majalisar wakilai 149 ba su kai wani kudiri ba a shekarar farko ta majalisar dokokin kasar ta 10.

Rahoton, wanda Oke Epia, Babban Darakta na OrderPaper, ya fitar a Abuja, ya yi karin haske kan yadda majalisar ta fitar da kudirori 77 kacal daga cikin 1,442 da aka gabatar tsakanin watan Yuni 2023 da Mayu 2024.

Sanatocin da rahoton ya bayyana cewa basu gabatar da kudurin ba sun hada da Amos Yohanna (PDP, Adamawa North), Victor Umeh (LP, Anambra Central), Samaila Kaila (PDP, Bauchi North), Abdul Ningi (PDP, Bauchi Central), Ani Okorie (APC, Ebonyi South), Adams Oshiomhole (APC, Edo North), Neda Imasuen (LP, Edo South), da Kelvin Chizoba (LP, Enugu Gabas).

Sauran sun hada da Muntari Dandutse (APC, Katsina ta Kudu), Jiya Ndalikali (PDP, Neja ta Kudu), Onyesoh Allwell (PDP, Rivers Gabas), Haruna Manu (PDP, Taraba ta tsakiya), Ahmad Lawan (APC, Yobe North), Napoleon Bali ( PDP, Plateau South), Abubakar Yari (APC, Zamfara Central).

Binciken da Daily Trust ta samu a wani rahoto ya gano cewa hudu daga cikin tsofaffin gwamnoni 13 a Majalisar Dattawa da wasu Sanatoci 21 ba su kai wani kuduri ba daga watan Yuni 2023 zuwa Maris 2024.

Epia ya kuma bayyana cewa, rahoton ya kuma yi nuni da yadda ake sake yin amfani da dokar, inda aka dawo da sama da rabin kudurorin majalisar dattawa da kusan kashi daya bisa uku na dokokin majalisar daga majalisu da suka gabata.

Majalisar dattijai ta ce an gabatar da kudirori 475, inda 19 kawai suka amince da shi, yayin da majalisar ta gabatar da kudirori 1,175, inda ta zartar da 58 kawai. Rahoton ya jaddada rarrabuwar kawuna tsakanin tallafin kudirin da kuma ci gaban da suke samu, wanda ke nuni da samun gibi wajen aiwatar da ayyukan majalisar.

Dole ne a kawo karshen rashin tsaro a yankinmu a yanzu – Kungiyar tuntuba ta Arewa ACF

Dole ne a kawo karshen rashin tsaro a yankinmu a yanzu – Kungiyar tuntuba ta Arewa ACF

Bayan wani babban taro da masu ruwa da tsaki a Arewa da suka hada da tsaffin gwamnonin jihohi, ministoci, shugabannin hukumomi, ‘yan majalisar dokoki ta kasa, manyan jami’an gwamnati da suka yi ritaya, malamai, kwararru da sauran ‘yan kasa masu kishin kasa, kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) ta yi kira da a dauki matakin gaggawa dan kawo karshen matsalar tsaro a Arewcin Nijeriya.

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, shine sakataren yada labarai na ACF na kasa, ya karanta sanarwar bayan taron kwamitin amintattu (BoT). Ya soki dabarun da ake bi a yanzu na yaki da masu tada kayar baya da ‘yan bindiga, yana mai cewa,ya ce akwai bukatar a sake salon yadda ake fada da ‘yan bindiga .

Tun da farko, shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Bashir Muhammad Dalhatu, ya bayar da uzuri ga al’ummar Arewacin Nijeriya dangane da gazawar da shugabannin suka yi wajen kare yankin daga daya daga cikin munanan rikice-rikice a cikin tarihin yankin.

Dalhatu ya jaddada cewa, ACF na yin nazari sosai kan dabarun magance matsalolin da ake fuskanta a Arewa da Nijeriya baki daya. Ya kuma bayyana cewa Arewa a shirye ta ke ta goyi bayan sake duba kundin tsarin mulki da kuma sauye-sauyen da aka zo dashi.

An kira taron ne domin magance tabarbarewar tsaro, tsadar rayuwa, fatara, rashin aikin yi, da sauran rikice-rikicen da suka addabi Arewacin Nijeriya.

Ta kuduri aniyar cewa dole ne ‘yan Arewa su himmatu wajen rikon  amana da hadin kai a tsakanin su, ba tare da la’akari da kabilanci ko addini ba. An yi kira ga membobin da su guji kalaman batanci ga ‘yan uwansu.