Matsalolin Nijeriya na bukatar a yi musu taron-dangi – Kasshim Shettima
Kungiyar Dalibai ta kasa sun yi barazanar rufe manyan biranen Nijeriya
Kungiyar Dalibai ta kasa sun yi barazanar rufe manyan biranen Nijeriya
Kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ta sanar da shirin ta na rufe dukkan manyan biranen Nijeriya daga ranar 15 ga Satumba, 2024.wannan na a wani mataki na martani ga karin farashin man fetur da aka yi a kwanakin nan.
A ranar Talata ne dai aka samu karin farashin man fetur kimanin ₦887 kan kowace lita, kuma an aiwatar da hakan a duk gidajen mai na NNPC.
Hakan ya haifar da cece kuce a duk faɗin ƙasar tare da ƙungiyoyin ma’aikata suna neman a sauya sabon farashin nan take.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Larabar nan Okunomo Henry Adewumi, shugaban dattawa ta NANS, ya bukaci a gaggauta sauya farashin man fetur.
Sanarwar ta ce za a gudanar da zanga-zangar ne cikin lumana da bin doka.
Yace sun rubuta ne domin sanar wa game da rufe dukkan manyan biranen Nijeriya, daga ranar 15 ga Satumba, 2024, domin nuna adawa da karin farashin man fetur da aka yi.
Karin farashin man fetur da aka yi a baya ya kawo wa talaka wahalhalu, kuma ba za mu iya tsayawa muna kallo ba alhalin muna ganin makomarmu.
Muna kira ga daukacin daliban Nijeriya a fadin kasar nan da su amsa wannan kira, domin za mu mamaye dukkan manyan biranen kasar a ranar 15 ga Satumba, 2024. Ba za mu yi shiru ba, kuma ba za a tsorata mu ba. Za mu tashi tare domin neman ingantacciyar Nijeriya.
Dole ne shugabannin duniya su sake farfaɗo da haɗin gwiwar duniya don yau da gobe
Harajin da ake karba a Nijeriya ya yi kadan-Bill Gates
Harajin da ake karba a Nijeriya ya yi kadan-Bill Gates
Gates ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa tsakanin matasan kasashen Afrika kan abinci mai gina jiki a Abuja, ranar Talata.
Daily Trust ta ruwaito cewa a halin yanzu hamshakin dan kasuwan nan na Amurka yana Nijeriya domin gudanar da wasu ayyuka.
Da yake jawabi a wurin taron, Gates ya ce karancin kudaden haraji na haifar da kalubale wajen samar da isassun kudade masu muhimmanci a fannonin kiwon lafiya da ilimi.
Ya ce domin ‘yan kasa su samu kwarin guiwa kan ayyukan gwamnati na samar da ingantacciyar kiwon lafiya, dole ne a daura damarar tabbatar da cewa an sarrafa kudaden da ake kashewa a shirye-shiryen kiwon lafiya.
Bill Gates ya ce, “Bayan lokaci, akwai tsare-tsare na Nijeriya na samar da kudade fiye da yadda take yi a yau. Harajin da Nijeriya take karba ya yi kadan.
Yace Idan ‘yan kasa suna son ilimi da kiwon lafiya, yayin da suke samun kwarin gwiwa cewa wadannan shirye-shiryen za a iya gudanar da su sosai, kuma gidauniyar sa ta hada da dimbin misalan da ke nuna hanya wajen tabbatar da an kashe kudaden
Kungiyar Kwadago ta kasa NLC da wasu sauran kungiyoyi sun bukaci a sauya farashin man fetur daga yadda yake yanzu
Kungiyar Kwadago ta kasa NLC da wasu sauran kungiyoyi sun bukaci a sauya farashin man fetur daga yadda yake yanzu
Kungiyar kwadago ta Nijeriya NLC ta bukaci da a gaggauta cire karin farashin man fetur na da akayi a kwanakin nan a fadin kasar.
Shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Joe Ajaero, ya ce kungiyar kwadagon na ganin gwamnatin tarayya ta ci amanar su kan sabon karin farashin man fetur.
Duk da cewa kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) bai sanar da karin farashin a hukumance ba, amma gidajen man da sauran manyan gidajen mai a fadin kasar sun daidaita farashin man fetur a ranar litinin.
A Legas, tashoshin NNPC sun maida farashin su zuwa N855 daga N568; Kano, N902; Abuja, N887 akan kowace lita daga N617.
Hakan ya faru ne kwanaki biyu bayan da hukumar NNPCPL ta sanar da jama’a bashin dala biliyan 6 da ta ke bin masu shigo da kaya da kuma matsalolin kudi da take fuskanta.
Ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa kungiyar kwadagon, a lokacin da ake tattaunawa kan mafi karancin albashin su zabi wani kaso a kara farashin man fetur ko kuma su karbi Naira 70,000 a mafi karancin albashi sannan a bar farashin man fetur ya ci gaba da zama kamar yadda yake.
Amma, bayan wata daya da gwamnati har yanzu ba ta fara biyan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa ba, sun fuskanci abubuwan da ba za su iya bayyanawa ba.
IGP Egbetokun zai cigaba da shugabantar ‘yan sandan Nijeriya har 2027
Shugaba Bola Tinubu ya amince da Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Kayode Egbetokun, ya ci gaba da rike mukaminsa har zuwa shekarar 2027.
Dangane da rahotannin da ke cewa an tsawaita wa’adin aikinsa, wata majiya mai tushe daga ‘yan sanda, da ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana cewa wasikar ba ta tsawaita wa’adin nasa ba, ta dai tabbatar da ya kammala wa’adin sa na shekaru hudu kamar yadda ya bayyana a wasikar nadin nasa.
Majiyar ta ce, ba a tsawaita wa’adin IGP din ba, sai dai an yi karin haske kan wasikar nadin nasa wadda ta kunshi shekaru hudu a matsayin shi na babban sufeton ‘yan sandan Nijeriya.
A watan Yuli ne dai majalisar dokokin kasar ta zartar da dokar gyaran dokar ‘yan sanda domin baiwa mutumin da aka nada a ofishin babban sufeton ‘yan sandan kasar damar ci gaba da rike mukaminsa har zuwa karshen wa’adin da aka tanadar a cikin takardar nadi.
Shugaba Tinubu ya mika kudirin dokar ga majalisar wakilai da ta dattawa domin yin kwaskwarima ga dokar.
‘Yan majalisar sun yi gaggawar zartar da kudurin dokar a zauren majasun duka.
Shugaban ya nada Egbetokun a matsayin IGP a watan Yunin 2023 na tsawon shekaru hudu. An nada shi tare da sabbin shugabannin hukumomin tsaro guda hudu.
Dangane da sashe na 18 (8) na dokar ‘yan sanda ta 2020, Egbetokun, wanda aka haifa a ranar 4 ga Satumba, 1964, ana sa ran zai yi ritaya a watan Satumba na 2024, lokacin da ya cika shekaru 60.
A halin yanzu dai Egbetokun ya shafe shekara daya da wata uku a kan karagar mulki, saura shekaru biyu da wata tara a ya cike shekaru hudu a nadin nasa.
Za a kammala aikin titin jirgin kasa daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano ba da jimawa in ji Shugaba Tinubu
Za a kammala aikin titin jirgin kasa daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano ba da jimawa in ji Shugaba Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da tabbacin za a kammala aikin titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano don inganta harkar sufuri a Nijeriya da yammacin Afirka baki daya.
Tinubu ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kai hedkwatar kamfanin gina layin dogo na kasar Sin (CRCC) a birnin Beijing, mai magana da yawun sa Ajuri Ngelale, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Shugaban ya amince da rawar da kamfanin ke takawa a matsayin amintaccen abokin huldar gwamnatin tarayya a cikin shirin samar da ababen more rayuwa ga ‘yan Nijeriya, ya kuma yaba da ayyukan da yake yi na layin dogo a Nijeriya.
Yace yana da matukar muhimmanci ya baiwa al’ummar Nijeriya tabbacin cewa a duk fadin kasar, za a kammala aikin layin dogo daga Ibadan-Abuja-Kaduna-Kano, da kuma yin yadda zai inganta sufuri a Nijeriya da yammacin Afrika baki daya.





