Akwai shawarar da muke shirin bayarwa na kara harajin VAT zuwa 10% a Nijeriya – Kwamiti
Shugaba Tinubu na aiki ba gajiyawa don tsaro ya inganta a Nijeriya – Kasshim Shettima
Babu wani tsamin danganta tsakanin Shugaba Tinubu da Mataimakinsa Kasshim – Fadar Shugaban kasa
Wike zai gurfana gaban kwamitin ladabtarwa bisa zargin yi wa PDP zagon-kasa na “Anti Party”
Jam’iyyar PDP ta gayyaci ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, bisa zargin yi ma jam’iyyar zagon-kasa.
Mataimakin sakataren yada labarai na Jam’iyyar na kasa, Ibrahim Abdullahi, ne ya bayyana haka a ranar Litinin a wani shiri na gidan Talabijin na Channels mai suna Sunrise Daily.
Abdullahi ya bayyana cewa an gayyaci Wike a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Tom Ikimi wanda kwamitin ayyuka na jam’iyyar ya kafa.
Nijar na shirin gina wata sabuwar matatar mai a jihar Dosso
Wata tawagar hadin gwiwar wasu ma’aikatun Nijar karkashin jagorancin sabon ministan mai, ta kai ziyarar aiki domin gani da ido na wurin da za’a gina sabon kamfanin matatar mai a cikin jihar Dosso.
Ana sa ran sabuwar matatar man za ta rika tace ganga dubu 30 a ko wace rana a tashin farko kafin daga bisani a fadada zuwa dubu 100 a kowace ranar.
Ko baya ga matatar man ma akwai kuma babban cibiyar samar da wutar lantarki a jihohin Tillaberi Dosso da babban birnin Yamai domin rage dogaro da na ketare inji hukumomin.
An kama hedimasta da ake zargin ya cefanar da kadarar makarantarsa a Kano
Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta kama shugaban makarantar firamare ta Gaidar Makada da ke karamar hukumar Kumbotso bisa zargin sayar da kadarorin makarantar.
Hakan na a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Kabir Abba Kabir, ya fitar ranar Asabar. Yana mai ce wa kamen ya biyo bayan bayanan sirri da hukumar ta samu na sayar da muhimman kadarorin makaranta ba bisa ka’ida ba.
Ya kara da cewa hukumar na binciken lamarin, kuma ana kokarin kwato kadarorin da aka salwantar.
Mun sa a binciki dalilin tashin gobara a gidan gwamnati – Gwamnan Katsina Dikko
Gobara ta tashi a gidan gwamnatin jihar Katsina
Gobara ta tashi da sanyin safiyar Litinin, ta kone wani sashe na babban dakin taro na gidan gwamnan jihar Katsina.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa babban dikin taron (red chamber)na kusa da ofishin gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda inda ya ke ganawa da muhimman mutane.
Ya zuwa hada wannan rahoto babu wani takamaiman musabbabin tashin gobarar da barnar da ta yi.
Atiku, Obi da Kwankwaso na tattaunawar dunƙulewa waje daya in ji PDP
Manya-manyan ‘yan adawa uku a Nijeriya na tattaunawa kan yiwuwar hadaka gabanin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Mataimakin kakakin jam’iyyar PDP na kasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
Abdullahi ya ce, za su ajiye muradun kashin kansu a gefe su kulla kawance mai karfi don ceto Nijeriya a cikin kangin da jam’iyyar APC ta cefa kasar a shekarar 2027.

.jpeg)

.jpeg)

.jpeg)
.jpeg)