DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 395

Za’a fara shari’ar mutanen da aka kama lokacin zanga-zanga a Abuja

A yau ne za a fara shari’ar masu zanga-zangar tsadar rayuwa a Abuja, Kano, Kaduna da Borno, kamar yadda mataimakin babban sufeton ‘yan sanda Dasuki Galadanchi ya bayyana.

Galadanchi ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara na kungiyar lauyoyin Najeriya da aka kammala a Abuja.

Ya ce wadanda za a gurfanar gaban kotun su 126 ne da aka zargin su da laifin daga tutar kasar Rasha tare da neman a sauya tsarin mulki a lokacin zanga-zangar, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane tare da sace dukiyoyin jama’a da na gwamnati a wasu jihohin kasar.

Lauyan mai kare hakkin bil’adama Femi Falana ne zai jagoranci sauran lauyoyin da za su kare masu zanga-zangar a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja.

SERAP ta kai karar Akpabio, Abbas kotu kan zargin yanka wa kansu alawus mai gwabi

Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci a Nijeriya ta maka shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas gaban kotu kan kawo karshen kayyade alawus-alawus dinsu.

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi zargin cewa ‘yan majalisar su ke yanke na kansu albashi da alawus-alawus.

Sai dai Majalisar ta musanta wannan zargi.

A cikin karar da aka shigar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1289/2024 a ranar Juma’ar da ta gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja, SERAP na neman da a tilasta wa Akpabio da Abbas su kawo karshen wannan lamari na kayyade albashi da alawus-alawus.

Gwamnatin tarayya za ta saka dala $800m a fannin wutar lantarki

Gwamnatin tarayya za ta saka dala $800m a fannin wutar lantarki

Gwamnatin tarayya ta ce ta na shirin zuba jarin dala miliyan 800 domin gina cibiyoyin rarraba wutar lantarki a wani bangare na shirin samar da wutar lantarki na shugaban kasa (PPI).

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Bolaji Tunji, mai baiwa ministan wutar lantarki shawara na musamman kan harkokin yada labarai da ya fitar ranar Lahadinan a Abuja.

Tunji ya ce, ministan wutar lantarki, Mista Adebayo Adelabu, ya bayyana haka a lokacin da yayi zuwan gani da ido masana’antar wutar lantarki da rarraba wutar lantarki ta kudancin TBEA a birnin Beijing na kasar Sin.

Ya ce, ministan ya je birnin Beijing domin halartar taron koli na hadin gwiwar Sin da Afirka.

Adelabu ya ce za a raba jarin gida biyu: dala miliyan 400, wanda ya shafi yankunan Benin, Fatakwal, da Enugu Distribution Companies (DISCOs), da dala miliyan 400, wanda ya shafi Abuja, Kaduna, Jos da Kano.

Ya ce duk da koma bayan da aka samu, gwamnati na da burin kara samar da wutar lantarki zuwa megawatt 6,000 a karshen shekara.

Adelabu ya jaddada kudirin gwamnati na hada kai da kungiyoyi masu daraja ta duniya irin su TBEA domin cimma burin Shugaba Bola Tinubu kan harkar wutar lantarki.

An hana wasu matasan NYSC shiga sansanin da ake horar da su na jihar Kano

Wasu matasa da za su yi wa kasa hidima na NYSC na can bakin kofar shiga sansanin da ake horar da su na Kusalla da ke karamar hukumar Karaye ta jihar Kano sun gaza shiga ciki.
Wani matashi da ya nemi jaridar Daily Trust ta sakaya sunansa, ya sanar cewa an hana su shiga ne saboda dalilan da ake kyautata zaton cewa sun je sansanin a makare.
Majiyar ta ce mafi yawan wadanda aka hana shiga din sun zo ne daga wurare masu nisa daga kudanci da gabashin Nijeriya da suka samu tangardar ababen hawa a yayin zuwansu Kano din.
Majiyar ta ce sun sha wahalar tafiya a hanya, wasunsu sun kwashe kwanaki 2-3 gashi sai a kurarren lokaci aka tura musu takardar iznin shiga sansanin matasan na NYSC wato “Call Up Letter”.
Ya ce sun kusa kai su 100 da aka hana shiga wannan sansani.

Gwamnatin jihar jigawa ta bayar da jari ga mata sama da dubu 12,a jihar

Gwamnatin jihar jigawa ta bayar da jari ga mata sama da dubu 12,a jihar

Gwamnan jihar jigawa Mallam Umar Namadi ya kaddamar da shirin bunkasa tattalin arzikin mata na JCARES a fadin jihar a yankin Gwari da ke karamar hukumar Dutse.

A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Namadi ya bayyana mahimmancin sabon shirin na karfafa tattalin arzikin mata, wanda ya shafi mata sama da 12,600 a fadin jihar inda kowanen su za ta samu tallafin kudi naira 50,000, jimilla ₦630 miliyan na tallafin tattalin arziki.

Gwamna Namadi ya jaddada kudirin gwamnatin sa na tabbatar da cigaban al’umma,wanda ya ba da fifiko wajen karfafawa matasa da mata da hanyoyi da rayuwarsu za ta inganta.

Ya kuma jaddada muhimmancin mayar da hankali ga mata wadanda ke da kashi 51% na al’ummar Jihar Jigawa, don tabbatar da bunkasar tattalin arzikinsu da inganta rayuwar iyalansu da al’ummarsu.

Gwamnan ya kuma sanar da kaddamar da wani sabon shiri na tallafawa mata tare da hadin gwiwar bankin duniya mai suna Nigeria for Women Project. Wannan shiri dai zai shafi dubban mata ne, tare da samar musu da abubuwa masu amfani da kuma shawo kan matsalolin cibiyoyi da kasuwanni domin bunkasar tattalin arzikin su.

Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin kudi na N50,000 da su yi amfani da kudaden domin bunkasa tattalin arzikin su domin samun ingantacciyar rayuwa.

Gwamna Bala ya sanar da nada sabon Sarkin Ningi a jihar Bauchi

Wanda aka ba sarautar shi ne Chiroman Ningi Alhaji Haruna Yunusa Danyaya.
Alhaji Haruna Danyaya shi ne babban da ga marigayi Sarkin Ningi.
Haruna Danyaya shi ne Sarkin Ningi na 17 kuma mai daraja ta daya.

Za mu zuba jarin Dala bilyan 4.8 a fannin kiwon lafiya – Gwamnatin Nijeriya

Gwamnatin Nijeriya ta sanar da shirinta na zuba jarin kudin da suka kai Dalar Amurka bilyan 4.8 a fannin kiwon lafiya.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a yayin da yake karin haske kan sauye-sauyen da gwamnatin ta yi a fannin kiwon lafiya wanda a cewarsa, zai lashe kudi sama da dala biliyan 4.8 wajen zuba jari duk a yunkurin gwamnati na ganin an farfado da ingancin kiwon lafiya a kasar tare da magance kalubalen da ya jima  yana addabar bangaren kiwon lafiyar
Shettima, ya bayyana hakan ne a wajen bikin kaddamar da rukunin asibitocin Sahad a birnin Abuja, 
“Gwamnatin mu ta kuma Kaddamar da gyare-gyare a kan bangarori huɗu masu mahimmanci wanda suka haɗa: sauya tsarin kula da kiwon lafiya, samar da ingatattun bangarorin binciken lafiya, buɗe Sabbin Cibiyoyin , da ƙarfafa sashin riga-kafi ga kamuwa da cututtuka.
Shettima ya yi kira ga  kamfanoni masu zaman kansu da su shigo wannan tsarin saboda muhimmancinsu ga  cimma burin samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya a Najeriya.
Kashim, ya kuma yaba wa mammallakin Kamfanin Sahad Group of Companies, Alhaji Ibrahim Mijinyawa, bisa namijin kokarin da yake yi na samar da ingantaccen kiwon lafiya.
Asibitocin Sahad din dai sun kunshi dakuna masu gadaje 200 da kuma kayan aikin kula da lafiya na zamani.

Napoli ta yanke shawarar kin mayar da Victor Osimhen cikin tawagar ta

Napoli ta yanke shawarar kin mayar da Victor Osimhen cikin tawagar ta

Hukumomin kulab din na Seria A sun tabbatar da hukuncin a daren ranar Asabar, kamar yadda masanin harkokin kwallon kafa Fabrizio Romano ya bayyana.

Napoli ta tabbatar da cewa ba ta da wani shiri na sake cigaba da amfani  da Victor Osimhen a cikin tawagar.

Fabrizio Romano ne ya tabbatar da hakan a shafin sa na X,kamar yadda kungiyar ta bayyana a daren lahadi.

Manajan kungiyar Antonio Conte ya bayyana takaicin sa kan gazawar kungiyar ta siyar da Osimhen a kakar wasan da ta gabata.

Kungiyar ta Napoli ta maye gurbin Osimhen da Romelu Lukaku da ke benci a kungiyar wanda ya basu nassara a wasan da suka yi a makonnan.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Beijing na kasar Sin domin aiwatar da wasu ayyuka a kasar

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya isa birnin Beijing na kasar Sin domin aiwatar da wasu ayyuka a kasar

Shugaban ya isa kasar Sin ne da sanyin safiyar Lahadinnan

A ranar Alhamis ne shugaban ya tashi daga Abuja zuwa babban birnin kasar Sin domin gudanar da wasu ayyuka a hukumance.

Mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale, ya ce shugaba Tinubu “zai yi dan takaitaccen aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa.”

Yayin da yake jawabi ga taron manema labarai, a fadar shugaban kasa, Ngelale ya ce, ana sa ran shugaban kasar zai shiga jerin tarurruka da “ayyukan da ke da amfani ga tattalin arzikin Najeriya da al’umma.”

Ya ce, shugaba Tinubu zai gana da takwaransa na kasar Sin, shugaba Xi Jinping, inda za a rattaba hannu kan yarjejeniyoyin fahimtar juna kan hadin gwiwar, “tattalin arzikin, aikin gona, bunkasa fasahar tauraron dan adam, bunkasa sana’o’i, da inganta sana’o’i, gami da bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.

Wannan dai zai kasance wani bangare na tattaunawa mai zurfi inda shugabannin kasashen biyu za su tattauna batutuwan da suka shafi hadin gwiwa, ba wai kawai tattalin arziki ba, har ma da batun tsaron kasa,da kasa,.

Ngelale ya bayyana cewa, shugaba Tinubu zai kuma halarci taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka (FOCAC), inda shugabannin kasashen Afirka da dama za su halarci domin tattaunawa da shugabannin kasar Sin kan wasu muhimman batutuwa.

Gwamnan Sokoto ya gargadi ‘yan siyasa da su daina siyasantar da matsalar tsaro

Gwamnan Sokoto ya gargadi ‘yan siyasa da su daina siyasantar da matsalar tsaro

Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya gargadi mutane ko kungiyoyi da su daina siyasantar da matsalar tsaro a jihar.

Ya yi wannan gargadin ne a wata ziyarar godiya da ya kai karamar hukumar Goronyo a ranar Asabar.

Yace tsaro wani lamari ne mai mahimmanci wanda ya shafi kowa da kowa, kuma ba za su lamunci da duk wani yunƙuri na amfani da shi don cin riba ta siyasa ba.

“Saboda haka, ina kira ga kowa da kowa da ya guji yin kalamai masu tayar da hankali ko kuma daukar matakan da za su kawo cikas ga lafiyar ‘yan kasar,”

Gwamnan, ya jaddada cewa tsaro wani nauyi ne da ya rataya a wuyansa, don haka ya bukaci hadin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki.

Gwamnan ya kara da cewa, “Ba za mu amince da duk wani mai kokarin sanya siyasa a harkokin tsaro ba, kuma za mu dauki matakan da suka dace don hana irin wadannan ayyuka kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharmu.