DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 396

Nijar ta yi bikin yaye sabbin sojoji hada na kasashen ketare

Nijar ta yi bikin yaye sabbin sojoji hada na kasashen ketare

Ministan tsaron jamhuriyar Nijar janar Salifou Modi ya jagoranci bikin yaye sabbin kananan sojoji a kwalejin su da ke jihar Agadez a arewacin kasar.

A jimilce dai sabbin dakarun 375 ne da suka hada da na kasar ta Nijar da wasu kasashen Afirka suka kwashe watanni suna samun hora da dubaru na aikin soja.

Daga cikin sojojin kasashen ketaren kuwa da aka yaye a Nijar din akwai biyu na Burkina Faso, biyu na Mali sai na kasashen Sénégal, Cameroun da Guinée.

Wannan yaye sabbin manyan sojoji na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke kara fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda da bullar sabbin kungiyoyin tawaye duk kuwa da ikirarin da hukumomin mulkin sojan na Nijar suke na kawo karshen matsalar tsaro.

To amma wannan na daga cikin matakin da suka sanar na daukan sojoji dubu 10 a ko wace shekara domin tunkarar matsalar.

Rundunar ‘yan sanda ta sake gayyatar shugaban kungiyoyar kwadago ta kasa (NLC)-Joe Ajaero

Rundunar ‘yan sanda ta sake gayyatar shugaban kungiyoyar kwadago ta kasa (NLC)-Joe Ajaero

Kwanaki biyu bayan ya amsa gayyatar da aka yi masa , rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sake gayyatar shugaban kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), Joe Ajaero domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake masa.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma bukaci Emmanuel Ugboaja, babban sakataren kungiyar ta NLC ya bayyana a gabanta tare da Ajaero.

A wata takarda mai kwanan watan Agusta 28, 2024, mai dauke da sa hannun mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Ibitoye Rufus Alajide, an umurci shugabannin NLC da su gana da mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda a sashin leken asiri na rundunar (FID) da ke Abuja a ranar Alhamis 5 ga Satumba, 2024. .

Wasikar ta bayyana cewa, a ci gaba da gudanar da bincike kan zargin da ake, an bukaci su zo tare da Comrade Emmanuel Ugboaja domin sake samun bayanai. 

Benson Upah, jami’in yada labarai na NLC, ya tabbatar da cewa an karbi wasikar ne a ranar Juma’a, 30 ga watan Agusta.

Mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Maradi dake janhuriyar Nijar ya yi sanadin rayukan mutane da dama

Mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihar Maradi dake janhuriyar Nijar ya yi sanadin rayukan mutane da dama

Saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a ranar juma’ar nan da ta gabata ya yi sanadin rayukan mutane da dama tare da jikkata wasu masu yawan gaske.

Rahotanni da wadansu fefen bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta na zamani na nuni da yadda ruwan ya yi awan gaba da dukiyoyin al’ummar garin Maradin da kewaye.

Kazalika ambaliyar da mazauna garin ke cewa ba a taba ganin irin ta ba a tarihi ta yi sanadiyyar lalacewar hanyoyi da rubtawar gidaje masu tarin yawa.

Ko da yake a hukumance ba a sanar da adadin asarar da ake fuskanta da rayukan ba amma wasu rahotanni na nuni da cewa mutum 14 ne suka hallaka a cikin wannan ambaliya yayin da kadarori da dukiyoyin al’umma na a kalla bilyoyin Cfa ne suka tafi a cikin ruwan.

Wani gini ya rufta da wata mata, tare da wasu yara Kano

Wani gini ya rufta da wata mata, tare da wasu yara Kano

Rushewar ginin ya faru ne a unguwar Makwarari da ke jihar Kano, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar rugujewar wani gida wanda ya yi sanadin mutuwar wata mata mai suna Balaraba Tijjani mai shekaru 35 da raunata ‘ya’yanta biyu a ranar Juma’a.

SolaceBase ta ruwaito cewa yaran Abdulnasir ne da Abdallah, masu shekaru 11 da 13.

A cewar mijin matar, Tijjani Magaji, ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya fara a daren ranar Alhamis kuma aka ci gaba da yi har safiyar Juma’a ne ya sa ginin ya ruguje.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin hukumar kashe Gobara ta Kano,Saminu Abdullahi, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa a ranar Juma’a, da misalin karfe 9:30 na safe, daga daga wani ma’aikacin su Ibrahim Isah, cewa wani gini ya ruguje.

Bayan samun labarin, suka aika da ‘yan kwana-kwana cikin gaggawa zuwa wurin da abin ya faru.

Abdullahi ya bayyana cewa an ceto wadanda lamarin ya rutsa da su a raye kuma an kai su Asibitin kwararru na Murtala Muhammed da ke Kano domin yi musu magani.

‘Yan sanda a katsina sun kama masu safarar makamai Uku tare da masu fashi da makami

‘Yan sanda a katsina sun kama masu safarar makamai Uku tare da masu fashi da makami

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan harsasai masu yawa a cikin garin Dutsinma da ke jihar.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, ASP Abubakar Sadiq, wannan na daga cikin gagarumin nasarar rundunar ta samu a yaki da ‘yan bindiga.

Wadanda ake zargin su ne Ahmed Mohammed Kabir, mai shekaru 25, mazaunin Hayin Danmani, jihar Kaduna, Mannir Musa, mai shekaru 25, daga garin Dutsinma, karamar hukumar Dutsinma da Aliyu Iliya, mai shekaru 25, daga kauyen Dankauye ta, karamar hukumar Safana, jihar Katsina.

An kama su ne a ranar 29 ga watan Agustan 2024, da misalin karfe 12:45, yayin da suke kokarin kai harsasai dari bakwai da arba’in (740) ga wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne a dajin Yauni, kauyen Ummadau, cikin karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, a cewar hukumar. 

ASP Sadiq a yayin da yake zantawa da manema labarai, ya ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wadanda ake zargin sun karbi harsashin ne daga jihar Nasarawa domin kai wa wani Harisu, wanda ake zargi da hannu wajen shiga ayyukan ‘yan bindigar.

A wani labarin kuma, rundunar ta ce a ranar 27 ga watan Agusta, 2024, ta kama wasu mutum uku Abubakar Ibrahim, mai shekaru 35 a kauyen Dunawa, Jamhuriyar Nijar; Abdullahi Nafi’u, m, mai shekaru 35, Madalla quarters, Abuja, da Adam Musa, mai shekaru 36, dan jihar Kano, dangane da laifin fashi da makami a karamar hukumar Baure ta jihar Katsina.

Kotu ta tura ɗan jarida gidan yari saboda ɓata sunan gwamnan Kano

 

Kotu ta tura ɗan jarida gidan yari saboda ɓata sunan gwamnan Kano

An tasa keyar wani dan jarida Muktar Dahiru, a gidan yari saboda yada wani labari na zargin Gwamna Abba Yusuf

‘Yan sanda sun kama Muktar Dahiru, ma’aikaci a gidan rediyon Nijeriya Pyramid FM Kano, tare da gurfanar dashi gaban kuliya.

An tuhumi Dahiru da sakin wata hirar sauti da wani dan siyasa a bangaren adawa yana zargin gwamnan da cin hanci da rashawa.

An gurfanar da Dahiru a gaban Kotun Majistare ta 24 a dake Gyadi Gyadi, da laifin bata suna, da kuma cin mutunci.

Nan ba da dadewa ba za mu shawo kan matsalar tsaro – Janar Lagbaja

 

Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Taoreed Lagbaja, ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa nan ba da dadewa ba sojoji za su shawo kan kalubalen tsaro da kasar ke fama da ita.

Lagbaja ya bayyana hakan ne a Uyo, ranar Alhamis, ya na mai tabbatar wa ‘yan Nijeriya kudurin su na ci gaba da hada kai da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin kasar.

Ya kamata Arewa ta marawa Shugaba Tinubu baya a zaben 2027 – Shehu Sani

Kamata ya yi ‘yan Arewa su marawa Shugaba Tinubu baya a zaben 2027 – Shehu Sani

Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya magantu kan sake tsayawar takarar shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.

Shehu Sani ya bayyana hakanne yayinda yake zantawa da manema labarai a Kaduna,yace a ra’ayin shi, ya kamata arewa su bar wa ‘yan kudu takara a zaben 2027,domin Arewa ta samu shugaban kasa a 2031.

A cewar sa,duk da kundin tsarin mulkin kasa ya bai wa kowane dan kasa damar tsayawa takara amma kamata ya yi ‘yan arewa su marawa ‘yan kudu baya a zabe mai zuwa.

Kamfanin NNPC zai mika Matatun Mai na Warri da Kaduna ga kamfanoni masu zaman kansu

Kamfanin NNPC zai mika Matatun Mai na Warri da Kaduna ga kamfanoni masu zaman kansu

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya NNPCL, ya ce yana neman hada hannu da kamfanoni masu zaman kansu masu inganci don cigaba da aikin da kula da Matatar mai dake Warri da kuma ta Kaduna.

An bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a a shafin sa na X.

Matatar mai ta Warri da ke Warri a Jihar Delta ta fara aiki ne a shekarar 1978. Warri wata matatar mai ce mai sarkakiya mai karfin sarrafa faranti mai karfin 6,250,000 MTA (125,000 bpd). Rukunin matatun ya haɗa da masana’antar petrochemical da aka ba da izini a cikin 1988 tare da ƙarfin samar da 13,000 MTA.

A nata bangaren kuma, an kaddamar da matatar mai ta Kaduna a shekarar 1980 domin samar da albarkatun mai ga A rewacin Nijeriya mai karfin 50,000 B/D. A cikin 1983, an faɗaɗa ƙarfin ta zuwa 100,000 B/D.

Ya zama wajibi gwamnatinmu ta magance matsalar rashin abinci mai gina jiki – Kasshim Shettima

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya yi kira wajen kara karfafa hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Kungiyar Tarayyar Turai domin yaki da Matsalar karancin Abinci mai gina jiki da sauran kalubalen jin kai a kasar.
Kashim Shettima ya furta hakan ne a yayin da yake karbar bakuncin tawagar jakadan EU mai barin gado Samuela Isopi a wata ziyarar bankwana da ya kai fadar shugaban kasa. 
Mataimakin ya kuma yaba da irin gudunmawar da kungiyar ta EU ke bai wa Najeriya Musamman a fannin Ayyukan jin kai da kasuwanci.
Shettima ya yaba da ayyukan Isopi a Najeriya, ciki har da rawar da ta taka wajen karfafa huldar EU da Najeriya, wajen samar da zaman lafiya da tsaro.
A nata  bangaren ita ma Isopi ta yi tsokaci kan ayyukan ta na shekaru uku, inda ta bayyana ci gaba da hadin gwiwar da aka samu, sannan ta jaddada kudirin kungiyar EU na ci gaba da tallafa wa Najeriya a fannin zaman lafiya da tsaro, taimakon jin kai, ilimi, lafiya, da bunkasar tattalin arziki.   
A karshe ta kuma bayar da tabbacin ci gaba da baiwa Najeriya hadin kai da goyon baya.