DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 397

Shugaba Tinubu ya jajanta wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana matukar damuwarsa kan barnar da ambaliyar ruwa ta yi wa al’umma a fadin kasar.

Hakan dai na a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Laraba, yana mai cewa shugaban ya damu matuka da halin da wasu yan kasar suka tsinci kansu na ambaliyar ruwa, rasa rayuka, gonaki da matsugunansu.

Gwamnatin tarayya ta amince da tallafin lantarki kashi 50% ga asibitocin gwamnati

 

Gwamnatin tarayya ta amince da tallafin wutar lantarki da kashi 50% ga asibitocin gwamnati a fadin kasar.

Karamin ministan lafiya da walwalar jama’a Dr. Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a jihar Kaduna yayin wata ziyarar aiki.

Yace wannan dai na da nufin rage kudaden tafiyar da asibitocin gwamnati.

Kotu ta daure matashi wata 9 kan satar doya

Wata kotun majistare da ke garin Kafanchan a Jihar Kaduna, a ranar Alhamis ta yanke wa wani mutum mai suna Cletus Gandu dan shekara 40 hukuncin daurin watanni tara a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kwaryar doya biyu.

Gandu ya yarda cewa ya saci doyar, amma yunwa ce ta saka shi aikata hakan. Amma ya roki kotu da tayi masa sassauci.

An bindige “DPO” a shingen binciken sojoji a jihar Zamfara

Babban jami’in dan sanda mai kula da ofishinsu na Wasagu wato DPO a jihar Kebbi ya rasa ransa ta dalilin harbin bindiga da ake zargin wani jami’in soja ya yi masa.

Jaridar Daily Trust ta ba da labarin cewa Halliru Liman ya hadu da ajalinsa ne a wani shingen ababen hawa da sojoji suka kafa a yankin Dan Marke na karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Yazid Abubakar ya ce babban jami’in dan sandan na kan hanyarsa ta zuwa Kebbi don halartar wani taro. A kan hanyar ne sojojin da ke aiki a karkashin shirin Operation Hadarin Daji suka tsayar da shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ya ce sojojin sun bindige DPO din nan take duk kuwa da ya nuna musu shaidar cewa shi jami’in dan sanda ne.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan ya fitar a ranar Alhamis, ta ce rundunar ‘yan sandan ta bukaci da a gudanar da kwakkwaran bincike don hukunta wadanda ke da hannu.

An fara neman sarautar sarkin Ningi ta jihar Bauchi.

 

An fara gudanar da gasar neman sarautar Masarautar Ningi a hukumance bayan rasuwar marigayi Sarkin, Alhaji Yunusa Mohammed Danyaya, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata yana da shekaru 88 a duniya.

Sarkin wanda ya shafe shekaru 46 yana mulki tun bayan hawansa karagar mulki a shekarar 1978, ana samun gadon sarautar ne bisa al’ada.

Gwamnatin jihar Bauchi ta umarci majalisar masarautu da sarakuna da su fara tantancewar.

An saki yan kasar Poland da aka kama sun daga tutar Rasha yayin zanga-zanga a Kano

 

An saki yan kasar Poland da aka kama sun daga tutocin Rasha yayin zanga-zanga a Kano

An saki wasu daliban kasar Poland da aka kama a Naijeriya yayin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana a ranar Laraba.

A farkon wannan wata ne Najeriya ta ce ta kama wasu ‘yan kasar Poland bakwai da suka daga tutocin kasar Rasha a lokacin zanga-zanga a jihar Kano.

Nijeriya na daga cikin kasashen da aka fi samun yawan sakin aure – Rahoto

Wani rahoto da shafin yanar gizo na kasar Amurka mai suna Divorce.com  ya lissafa Nijeriya daga cikin jerin kasashen da ke yawan samun mutuwar aure.

Rahotan ya bayyana cewa yawan kisan aure a Nijeriya ya zarta na kasashen Kanada, Indiya, Vietnam, Sri Lanka da kuma kasar Peru.

Alkaluman da aka buga a shafinsu na yanar gizo a watan Yuli, sun nuna cewa Nijeriya ta zo ta goma sha daya cikin kasashe ashirin da shida da aka fi yawan samun matsalar ta mutuwar aure.

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kudin cike gibi ga majalisar Dokokin jihar

Gwamnan Kano ya gabatar da kasafin kudin cike gibi ga majalisar Dokokin jihar

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rubutawa majalisar dokokin jihar takardar neman amincewar kwarya kwaryar kasafin kudin shekarar 2024, N99bn.

An karanta wasikar bukatar Gwamna Yusuf a zauren majalisar yayin zaman da kakakin majalisar, Ismail Falgore ya jagoranta a ranar Talatar nan.

Da yake karanta wasikar, Falgore ya bayyana cewa gwamnan yana neman amincewarsu a karkashin sashi na 122 (A da B) na kundin tsarin mulkin kasar na 1999 don aiwatar da ayyukan da suka sa a gaba da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar.

Har ila yau, ya bayyana cewa, daga cikin Karin kasafin kudin, an ware Naira biliyan 33 na kudin mafi karancin albashi, N34bn na kudin da ake kashewa na manyan ayyuka.

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan gabatar da wasikar ga majalisar, kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi na jihar, Musa Shanono, ya ce, kafin kasafin kudin jihar na shekarar 2024 ya kai N437, 338, 312, 787.

“Idan aka hada kasafin na da da karin kasafin kudin, aka amince da shi a matsayin doka, zai kara kasafin kudin 2024 zuwa N536, 559, 816, 357.84.”

Za kuma a yi amfani da karin kasafin kudin don biyan sabon mafi karancin albashin da aka cimma tsakanin kungiyar kwadago ta Nijeriya da gwamnatin tarayya.

Bayan dawowa daga Faransa Tinubu zai tafi kasar Sin

Bayan dawowa daga Faransa Tinubu zai tafi kasar Sin

Mako guda da dawowa daga ziyarar da ya kai kasar Faransa, shugaba Bola Ahmed Tinubu na shirin tafiya kasar Sin.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a fadar shugaban kasa a Villa a Talatar nan.

Da yake jawabi ga taron manema labarai, Ngelale ya ce, ziyarar kasar Sin da ake sa ran za a yi a cikin makon farko na watan Satumba, wani bangare ne na kokarin gwamnati mai ci na inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.

A kasar Sin, ana sa ran Tinubu zai gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping, inda za a rattaba hannu kan wata yarjejeniya (MoU).

Shugaba Tinubu zai kuma gana da manyan jami’an kamfanoni guda goma a kasar Sin a bangarorin

Man fetur da gas, samar da Aluminum, Noma da fasahar tauraron dan adam.

Yadda mai sana’ar sayar da shayi ya yi ajalin wani matashi bisa zargin satar masa biredi da taliya a Jigawa

 Yadda mai sana’ar sayar da shayi ya yi ajalin wani matashi bisa zargin satar masa biredi da taliya a Jigawa

Abdulrashibu Ya’u dan shekara 40 mai sana’ar shayi a kauyen Sararai da ke garin Jigawar Tsada a karamar hukumar Dutse ta Jihar Jigawa ya yi wa Hassan Garba dan shekara 20 dukan tsiya har lahira.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ya’u ya zargi Garba da satar masa biredi, da taliyar yara, da kuma fetur.

Da samun rahoton ‘yan sandan sun tura jami’ai wurin da lamarin ya faru, inda suka cafke wanda ake zargin, yayin da aka garzaya da wanda aka halaka zuwa asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni, inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa,DSP Lawan Shiisu Adam ya ce a lokacin da yake amsa tambayoyi a sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Dutse, Ya’u ya amince da aikata laifin, inda ya bayyana cewa satar da Garba ya yi masa itace ta kara fusata shi, kuma a baya ya sanar da iyayensa, amma ba a dauki mataki ba.

Ya ce a fusace, Ya’u ya daure Garba da igiya, ya yi masa duka da sanda har ya kai ga mutuwarsa.

Makwabta sun ba da rahoton jin kukan Garba na neman agaji amma sun kasa shiga tsakani har sai da jami’an ‘yan sanda suka iso.

Yace bayan kammala bincike, za a gurfanar da Ya’u a gaban kotu domin ya fuskanci shari’a.