DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Sunday, April 12, 2026
Home Blog Page 398

Farashin tafiye-tafiye a jirgi ya karu, yayin da na mota da masu haya da babura ya sauko a watan Yulin, 2024 a Nijeriya

Farashin tafiye-tafiye a jirgi ya karu, yayin da na mota da masu haya da babura ya sauko a watan Yulin, 2024 a Nijeriya

Wani sabon rahoto da Hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ta fitar ya ce matafiya masu hawa jirgi sun samu karin kashi 25 na kudin jiragen sama a watan Yulin 2024.

 A cikin rahoton sa na watan Yuli ya ce farashin jiragen sama ya tashi da kashi 25 cikin 100 duk shekara (YoY) zuwa ₦98,561.74 a watan Yuli 2024 daga ₦78.775.74 a watan Yulin 2023.

NBS ta ce a cikin tafiye-tafiyen jirgin sama, karanacin kudin da fasinjojin jirgin ke biya na yakai N98,561.74 a watan Yulin 2024, wanda ya nuna karuwar kashi 9.65 cikin 100 idan aka kwatanta da watan da ya gabata (Yuni 2024).

A bisa tsarin YoY, farashin kudin ya tashi da kashi 25.12 daga N78,775.74 a watan Yulin 2023.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin tarayya a watan da ya gabata, ta ce za ta kara haraji, sakamakon korafe-korafen da kamfanonin jiragen sama na Nijeriya ke yi kan yawan haraji.

Duk da karuwar kudin jirgi a watan Yuli, farashin da ake biya na mota bas da babur dana jirgin ruwa ya ragu a watan Yulin 2024.

NBS ta ce karancin kudin da matafiya ke biya na tafiye-tafiye a cikin gari kowace ya ragu zuwa 2.18% daga N963.58 a watan Yuni 2024 zuwa N942.61 a Yuli 2024. A duk shekara, ya ragu da 29.46 % daga N1,336.29 a watan Yuli 2023.

Nijeriya ta fara kai iskar gas ta LNG a kasashen China da Japan

Nijeriya ta fara kai iskar gas ta LNG a kasashen China da Japan

Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC Ltd.) ya fara jigilar jigilar iskar Gas (LNG) zuwa kasashen Japan da China bisa dogaron Ex-Ship (DES).

Babban Jami’in Sadarwa na Kamfanin NNPC, Mista Olufemi Soneye ya rawaito Mista Segun Dapo, Shugaban zartarwar na, NNPC Ltd., na bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Litinin.

An ambato Dapo yana cewa ci gaban ya yi daidai da dabarun da kamfanin ke da shi na zama amintaccen mai samar da makamashi a duniya.

“Baya ga samun karin kudi, tsarin na DES ya baiwa NNPC Ltd. damar kutsawa cikin sassan da ke karkashin LNG,

Kamfanin Dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa Delivered Ex-Ship (DES) wani tsarine na kasuwanci na kasa da kasa wanda ke buƙatar mai siyarwar ya kai kayan sa a wata tashar jiragen ruwa.

Soeye ya kuma ruwaito Dapo na cewa, kamfanin na NNPC ya samu nasarar hakan ne tare da hadin gwiwar wasu rassansa guda biyu.

Ya lissafta kamfanonin kamar NNPC LNG Ltd da NNPC Shipping Ltd.

Ya ce ta isar da kayanta na farko na DES LNG daga jirgin ruwan LNG mai tsawon mita 174,000,a Japan, a ranar 27 ga Yuni, 2024.

Jihohi 21 a Nijeriya na neman karbo bashin tiriliyan 1.65

 Jihohi 21 a Nijeriya na neman karbo bashin tiriliyan 1.65 

Jihohi ashirin da ɗaya na ƙasar nan suna neman bashin na naira tiriliyan 1.65 domin cike gibin kasafin kuɗinsu na shekarar 2024 duk da ƙarin kason kudi da suka karɓa daga Kwamitin rarraba kudade na kasa wato FAAC a cikin shekarar da ta gabata.

Daga watan Yuni na 2023 zuwa wannan shekarar, dukkanin jihohi 36 da ƙananan hukumomi 774 sun karɓi jimillar naira tiriliyan 7.6 daga FAAC. wannan ƙarin kudaden shiga ya faru ne galibi saboda cire tallafin fetur da gwamnatin tarayya ta yi a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Binciken da Daily Trust ta yi ya nuna cewa ana sa ran jihohi 36 za su karɓi naira tiriliyan 5.54 daga FAAC a wannan shekarar, idan aka kwatanta da naira tiriliyan 3.3 da aka rarraba musu a bara.

Bisa ga cikakkun bayanai na shirin cin bashin kuɗin da aka bayyana, Gwamnatin Jihar Adamawa na shirin karɓar bashin Naira biliyan 68.46, Anambra Naira biliyan 245, Bauchi Naira biliyan 59.08,Bayelsa Naira biliyan 64, Benuwai Naira biliyan 34.69,Borno Naira biliyan 41.71,Ebonyi Naira biliyan 20.5,Edo Naira biliyan 42.71, da Jihar Ekiti Naira biliyan 27.15.

Wasu daga cikin sauran jihohin sun haɗa da Jigawa Naira biliyan 1.78, Kaduna Naira biliyan 150.1,Kebbi Naira biliyan 36.7, Katsina Naira biliyan 163.87,Kogi Naira biliyan 37.08, Kwara Naira biliyan 30.76, Osun Naira biliyan 12.36, Oyo Naira biliyan 133.4, Nasarawa Naira biliyan 32.93,Gombe Naira biliyan 73.75, Enugu Naira biliyan 103, da kuma Imo Naira biliyan 271.34.

Ina samun Naira milyan 7 duk shekara a noman tumatur da barkono, in ji wani manomi daga jihar Gombe

Ina samun Naira milyan 7 duk shekara a noman tumatur da barkono, in ji wani manomi daga jihar Gombe

Wani manomi mai shekaru 35 da haihuwa daga yankin Bula a karamar hukumar Akko ta jihar Gombe, Saleh Maikudi, ya ce yana samun sama da Naira miliyan 7 a duk shekara daga noman tumatir da barkono.

Manomin ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN a garin Bula a ranar Litinin, 26 ga watan Agusta, 2024.

Maikudi, ya bayyana cewa ya kashe sama da Naira miliyan 1.5 a gonakin kadada 30 da ya noma a shekarar 2023, ya kuma samu sakamako mai kyau.

Yace yana noma tumatir, barkono,Tatashe, barkono barkono, a gonar tasa.

Maikudi, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar manoman kayan lambu a cikin yankin, ya ce yana noma kadada 30 na kayan lambu a duk shekara.

Ya ce sai da aka kwashe makonni 10 da noman kayan lambu kafin a fara girbin kayayyakin na tsawon mako 10.

Manomin ya bayyana cewa a daminar bana manoma sun fara girbi, inda ya kara da cewa masu noman rani na zuwa ga al’ummarsu domin sayen kayayyakin da za a kai wa jihohin Nijeriya.

Gwamnatin jihar Katsina za ta zuba Naira Biliyan N30bn a fannin noma

Gwamnatin jihar Katsina za ta zuba Naira Biliyan N30bn a fannin noma

A ci gaba da kokarin da take yi na bunkasa ayyukan noma don samar da abinci da tattalin arzikin karkara, gwamnatin jihar Katsina ta ce tana shirin zuba sama da Naira biliyan 30 kan harkar noma.

Gwamnan jihar, Mallam Dikko Umar Radda ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan dawowarsa daga hutun wata daya.

Radda wanda ya tafi kasar Sin a karshen hutun da ya yi don duba hanyoyin daidaita harkokin noma a jiharsa, ya ce za a yi amfani da wani bangare na kudaden ne wajen kafa cibiyoyin sarrafa kayan gona a kowace karamar hukuma.

Ya ce cibiyoyin za su horar da manoma dabarun noma na zamani tare da samar musu da kayan aikin noma, ta yadda manyan manoma da kananan manoma za su samu damar yin amfani da kayan aiki daidai gwargwado.

Shugaba Tinubu ya nada Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin Shugaban hukumar tsaron farin kaya ta DSS

 Shugaba Tinubu ya nada Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin Shugaban hukumar tsaron farin kaya ta DSS

Shugaba Bola Tinubu ya nada Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS).

Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan al’umma Ajuri Nglele ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Ajayi ya maye gurbin Yusuf Magaji Bichi wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a shekarar 2018.

Yan sanda sun dakile harin ‘yan bindiga a Katsina

 ‘Yan sanda sun dakile harin ‘yan bindiga a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce jami’anta sun dakile hare-haren ‘yan bindiga guda biyu tare da kubutar da wasu mutane biyar da aka yi garkuwa da su, yayin da aka halaka wasu masu garkuwa da mutane biyu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Litinin dinnan.

A cewar sa, rundunar ‘yan sandan ta samu kiran gaggawa a ranar Lahadi kan harin da ‘yan bindiga suka kai a kauyen Layin Minister, karamar hukumar Malumfashi ta jihar.

Ya ce an yi garkuwa da mutane biyar a yayin harin.

Yace bayan samun rahoton, an yi gaggawar tattara jami’an tare da tura su wurin. Da suka lura da kasancewar ‘yan sandan, ‘yan bindigar sun bude wuta kan jami’an, inda suka mayar da martani da gaggawa.

Ya ce an samu nasarar kubutar da dukkan wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji rauni ba, yayin da maharan suka mika wuya ga jami’an, inda suka tsere da raunukan harsasai daban-daban.

An dage taron wakilan gwamnatin tarayya da aka shirya tare da malaman jami’o’i

 An dage taron wakilan gwamnatin tarayya da aka shirya tare da malaman jami’o’i

An dage zaman da ake shirin yi tsakanin gwamnatin tarayya da mambobin kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da aka shirya gudanarwa a yau.

Ko da yake ba a bayyana dalilin dage taron ba, amma a yanzu ana sa ran gudanar da taron a ranar Laraba 28 ga watan Agusta.

Malaman jami’o’in gwamnati a karkashin kungiyar ASUU a makon jiya sun yi barazanar shiga yajin aiki a fadin kasar saboda abin da suka bayyana a matsayin rashin goyon bayan gwamnatin tarayya na mutunta yarjejeniyar da aka sake kullawa a shekarar 2009.

Sanarwar dai na daga cikin kudurorin da aka cimma a taron majalisar zartarwar kungiyar, wanda aka gudanar a jami’ar Ibadan a karshen makon da ya gabata.

Bukatun ASUU sun hada da harkokin jin dadin ma’aikatan, samar da kudade ga jami’o’i da kuma bukatar dakatar da yaduwar jami’o’i a fadin kasar nan.

Taron da aka shirya shi ne don hana sake yajin aikin ASUU.

Ban yi almubazzaranci da kudin da na samu daga wajen Gwamna Abba Kabir Yusuf ba– Zainab Ado Bayero

Ban yi almubazzaranci da kudin da na samu daga wajen Gwamna Abba Kabir Yusuf ba– Zainab Ado Bayero 

Daya daga cikin ‘ya’yan marigayi sarkin Kano, Zainab Jummai Ado Bayero, ta karyata ikirarin da ake na cewa ta yi almubazzaranci da kudaden da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya baiwa ita da mahaifiyar ta tare da dan uwanta.

A watan Yunin wannan shekarar ne dai, Jummau ta fito ta bayyanawa jama’a neman tallafin kudi, a lokacin da ita tare da mahaifiyarta da yayanta, ake yi musu barazanar kora daga wani gida a Legas sakamakon rashin biyan kudin haya.

A cewar Zainab, ‘yan uwanta sun shiga mawuyacin hali tun bayan rasuwar mahaifinsu da suka hada da rashin wurin kwana da kudin da za su ci gaba da karatunsu.

Sai dai a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature ya fitar, ya ce ya ziyarce su a Legas ne a ranar Talata 25 ga watan Yuni, 2024 bisa umarnin gwamnan domin ganawa da Manajan gidan da iyalan Ado Bayero suka zauna, Mista Sunel Kumar tare da biya musu kudin.

Zainab wadda ta godewa gwamnan bisa wannan karimcin, rahotanni sun bayyana cewa, daukar matakin ya zo ne a daidai lokacin da aka shirya wasu matasa domin su kore su daga gidan saboda sun kasa biyan kudin hayar.

Sai dai bayan wata biyu jummai Bayero ta sake fitowa neman taimako, inda ta roke su cewa suna bukatar karin kudi domin su samu biyan bukatunsu su mayar da dan uwanta makaranta.

Hakan dai ya haifar da cece-kuce inda wasu suka ce ta salwantar da kudaden da gwamnan ya aike mata da ‘yan uwan ta.

Gwamnatin tarayya za ta zauna da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU a yau kan batun shiga yajin aiki

Gwamnatin tarayya za ta zauna da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU a yau kan batun shiga yajin aiki

A yau ne wakilan gwamnatin tarayya karkashin jagorancin ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, za su gana da jami’an kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da sauran masu ruwa da tsaki domin warware batutuwan da suka shafi kowane bangare.

Hakan ya biyo bayan barazanar da ASUU ta yi na shiga yajin aikin a baya-bayan nan bayan fitar da sanarwar kwanaki 21 ga gwamnatin tarayya kan wasu batutuwa da ba a warware ba.

An bayar da sanarwar ne a karshen taron kungiyar ASUU ta kasa (NEC), wanda aka gudanar a jami’ar Ibadan, kuma an mika kwafin ga ma’aikatun kwadago da ilimi na tarayya.

Wasu daga cikin batutuwan sun hada da asusun farfado da jami’o’in gwamnati na gaggawa; biyan alawus-alawus na ilimi; da kuma sakin albashin da aka hana, basussukan karin girma, IPPIS da cire wasu mambobi da sauran su.

Yajin aikin karshe da kungiyar ASUU ta shiga a lokacin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya shafe sama da watanni takwas ana gudanar da harkokin ilimi a fadin kasar nan.

Ministan ilimi ya shaida wa manema labarai, a wani taron manema labarai na cika shekara guda na gwamnatin, a karshen mako a Abuja, cewa an aike da wasikun gayyata ga jami’an ASUU da wasu kungiyoyi da dama da za su zauna a taron.